Gobara Ta Ƙone Shaguna 12 A Kasuwar Siminti Ta Oyo
Published: 11th, April 2025 GMT
A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar.
Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka, ya bayyana cewa jami’ansu sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:02 na dare, inda nan take suka tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Cfs Jimoh.
Akinyinka ya bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wutar lantarki mai ƙarfi. Ya ƙara da cewa an kare dukiyoyi da darajarsu ta kai biliyoyin Naira a kasuwar, duk da cewa shaguna 12 sun ƙone baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gobara
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Borno ta yi kira ga mazauna da su fito cikin kwanciyar hankali domin kada kuri’arsu a zaɓen ƙananan hukumomin da ake gudanarwa a yau Asabar.
Tundunar ta tabbatar da cewa za a samar da isasshen tsaro a lokacin zaɓen da kuma bayan kammalawarsa.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya yi wannan kira ne a yayin wani taron tsaro mai muhimmanci da aka gudanar tare da ƙungiyoyi, kwamandojin tsaro, shugabannin sassa, da dukkan DPOs a faɗin jihar, kafin zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a yau Asabar, 13 ga Disamba, 2025.
“Rundunar tana kira ga jama’a da su fito ba tare da wani shakka ba domin aiwatar da nauyin da ke kansu cikin lumana,” in ji sanarwar, wadda kakakin Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a Maiduguri
Ya kuma gargadi mazauna jihar da su kasance cikin taka tsantsan, tare da kauce wa labaran ƙarya da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.
Rundunar ta bayyana cewa an riga an fara amfani da dabarun tura jami’an tsaro da sanya idanu a fadin jihar domin tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.