Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da rabon sabbin baburan hawa ga shugabannin jam’iyyar APC na mazabun kananan hukumomi 12 na shiyyar Jigawa ta Arewa maso yamma wadda Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya bayar da kyauta.

A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya yaba da kokarin Sanatan tare da shawartar shugabannin da suka sami ababan hawan da su yi amfani da su yadda ya kamata.

A jawabin sa, Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya ce ya bada baburan ne domin saukakawa shugabannin jam’iyya gudanar da ayyukan su cikin sauki.

Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa nasarorin da ya samu a shekaru biyu da ya yi akan karagar mulki.

 

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Babura Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ummar Karamar Hukumar Dutse Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Yashe Madatsar Ruwa Ta Warwade

Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin.

Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata.

Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum.

Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran bukatun yau da kullum.

Yace ana samun ribar kimanin naira dubu goma zuwa ashirin a kowace rana daga siyar da kifin ga matafiya da kuma baki masu kai ziyara garin.

A don haka, Umar yayi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta yi yashen madatsar ruwan saboda a samu karin kifaye da kuma ruwa da za a iya amfani da shi domin noman rani.

Shi ma a yayin tattaunawa da Dagacin Warwade, Malam Musa Ado, ya ce madatsar ruwan tana samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da hana tafiya zuwa cirani a sauran yankunan kasar nan da sunan yin sana’o’i.

Ya ce matasan yankin suna gudanar da sana’ar kamun kifi da kuma nomar rani da ta damina.

Sai dai kuma, Malam Musa ya koka kan rashin samar da injinan noman rani da kuma Malaman gona kamar yadda ake yi a gwamnatocin baya.

Kazalika, yace a ‘yan kwanakin baya gwamnatin jihar Jigawa ta kai ziyara kauyen inda ta sanar da cewar Bankin duniya zai samar da wasu kudade ta hannun gwamnatin tarayya wanda za’a baiwa gwamnatocin jihohi domin yashewa tare da gina burtuloli da hanyoyin noman rani.

Bisa haka ne dagacin yayi kira ga gwamnatin jihar da ta fara yin garambawul a madatsar ruwan domin a baiwa mazauna yankunan damar amfani da shi.

A shekarun baya dai, gwamnatin jihar Jigawan ta samar da irin kifaye guda dubu Dari uku domin inganta samar da kifi a yankin.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rikicin kabilanci: Mutane 2 sun mutu, wasu 7 sun jikkata a Jigawa
  • Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
  • Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
  • Za A Yi Wa Masu Lalurar Ido Aiki Kyauta A Jihar Jigawa
  • Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna 
  • Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal
  • Al’ummar Karamar Hukumar Dutse Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Yashe Madatsar Ruwa Ta Warwade
  • Gwamna Uba Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna