2025-06-15@13:02:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2358
«Isra ila»:
Ofishin shugaban kasar Turkiya, ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya a birnin Istanbul, za ta kai ga tsayar da tsagaita budewa juna wuta wanda kuma zai ga, kawo karshen yakin baki daya. Ofishin shugaban kasar Turkiya ya bayyana haka a yau Talata, ta kuma kara da cewa,; Tattaunawar...
Wasu kuma sun ce akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan da mahaifinsa, Oba Akinruntan. Bayan saukar Akinruntan, an zaɓi Ololade Gbegudu daga Okitipupa a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar. Gbegudu, mai shekara 42, ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin tsaro da ci gaban al’umma a majalisar kafin wannan sabon muƙamin. Oluwatoyin James daga Akoko ta Arewa Maso...
Iftila’in ambaliyar ruwa a garin Mokwa a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta Jihar Neja ta yi ajalin mutane sama da 200, yayin da wasu sama da 500 suka bata. Ambaliyar, wadda ita ce mafi muni a yankin cikin shekaru 60, ta shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa, bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Alakar Iran Da Lebanon Tarihi Ce Mai Tushe Da Ta Ginu Kan Mutunta Juna
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Dangantakar Iran da Lebanon tarihi ce, mai tushe, kuma ta ginu ne bisa mutunta juna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana alakar da ke tsakaninta da kasar Lebanon a matsayin mai tarihi, mai tushe, kuma ta ginu ce bisa mutunta juna. Ya ce: “Kasashen biyu...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Soki Rahoton Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Kan Kasarsa
Ministan harkokin wajen Iran ya soki rahoton hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya yayin ganawa da Grossi a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya soki sabon rahoton da hukumar ta IAEA ta fitar kan shirin makamashin nukiliyar kasar Iran yayin ganawarsa da babban darektan hukumar ta makamashin nukiliya ta duniya...

Iran Ta Yi Watsi Da Da’awar Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa Na Da’awar Mallakar Wasu Yankunan Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Tsibiran guda uku na Tunb Babba da Tunb Karami da Abu Musa yankuna ne Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da ikirari da kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGCC) ta yi dangane da tsibiran Iran guda uku, yana...
Sojojin mamayar Isra’ilan sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi a birnin Rafah, inda suka kashe mutane da dama a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji Fararen hula 23 ne suka yi shahada yayin da wasu kusan 200 suka jikkata a yau Talata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka bude wuta kan mai uwa...
Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni. Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau. Malam Gusau ya...
Dillalan rago a jihar Kano sun nuna damuwarsu kan rashin zuwan masaya da suke fuskanta duk da ‘yan kwanaki da suka rage ayi bukukuwan Sallah. Ziyarar da aka kai kasuwar dabbobi ta Gandun Albasa ta nuna cewa, da yawa daga cikin masu sayar da kayayyaki sun shafe tsawon yini ba tare da yin cinikin...
Wata hajiyar Najeriya daga Jihar Filato ta rasu a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya. Hajiya Jamila Muhammad ta rasu ne a yayin da alhazai ke shirin fara gudanar da aikin Hajji gadan-gadan. Sakataren Hukumar Kin Dadin Alhazai ta Jirage Filato, Daiyabu Dauda, ya sanar a ranar Litinin cewa Hajiya Jamila ta rasu ne a asibitin...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan...
’Yan bindiga sun sako wani magidanci da suka yi garkuwa da shi da amaryarsa na tsawon wata bakwai, bayan sun bindige matar tasa tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 30 daga iyalansa. A watan Oktobar 2024 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutumin suna Yakubu Dada tare da amaryarsa, a yayin da ma’auratan...
Ya ce an kai farmakin ne a kudancin yankin Mai-Galma a karamar hukumar Maru, domin dakile wani gagarumin farmaki da ‘yan bindiga suka shirya kai wa wasu al’ummomi. Bayan harin ta sama, sai aka tura sojojin kasa domin bin sahun ‘yan ta’addan da aka tarwatsa. “Sun tabbatar da lalata babura tare da kashe...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musuluinci ta Iran wanda ya kai Ziyarar aiki kasar Masar ya bayyana cewa, cinikayya a tsakanin kasashen biyu za ta karu. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Masar ya ce: “A bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka...
Sabon fira ministan kasar Sudan Kamil Idris ya yi kira ga kasashen waje masu taimaka wa dakarun daukin gaggawa “RSF” da su kawo karshen taimakon da suke bawa masu aikata laifi.” Idris wanda yake jawabin bayan kama aiki a jiya ya ce; Jami’an tsaro da kuma mahukuntan kasar ta Sudan suna da cikakken goyon baya...
Gwamnan Babban Bankin Iran ya wanda yake Ziyara a kasar China ya gabaatr da shawarar a kafa bankin hadin gwiwa a tsakanin kasashe mambobi a kungiyar Shangai. Muhammad Riza Farzin ya isa kasar ta China ne domin halartar taron gwamnonin manyan bankunan kasashen da suke mambobi a cikin wanann kungiya, domin yin nazarin hanyoyin aiki...
Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan ya jaddada goyon bayan da kasarsa take bai wa tattaunawar da ake yi a tsakanin Rasha da Ukiraniya, ya kuma kara da cewa; Ana yin nazarin yadda za a gana, a kuma tattauna tsakanin shugabannin kasashen biyu.” Fidan ya kuma bayyana fatansa na ganin cewa tattaunawar da aka bude...
A ranar Alhamis da ta gabata ce Fira ministan kasar Senegal Usman Sonko ya bude ziyarar aiki a kasashen yamamcin Afirka domin kara dankon zumunci da kasashen. Daga cikin kasashen da ziyarar ta shafa dai akwai Cote-De Voire, Serra Lione, da Guinea Conakry . A makon da ya gabata ne dai a yayin taron kira...
Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwanaki goma domin bikin Babbar Sallah da za a yi ranar Juma’ar wannan makon. Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa makarantun za su fara hutun ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki, zuwa ranar Lahadi, 15 ga...
Rundunar ‘yansanda a jihar Gombe ta umurci rufe duk wata tashar sauka ko daukar fasinjoji a cikin garin Gombe ciki har da fitacciyar tashar Dadin Kowa, inda ta ce, tashar Ibrahim Hassan Dan-Kwambo ce kadai halastacciya. Bugu da kari, motocin haya da ke dauke da amintaccen launin kala na gwamnati a cikin garin Gombe...
Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin Tinubu ta kaddamar ta ofishin mataimakin shugaban kasa a cikin shekaru biyu da suka gabata: Noma Ta bayyana karara tun farkon shekarar 2025, lokacin da Shugaba Tinubu ke neman mukamin shugaban kasar nan, cewa noma ne zai zama babban abin da gwamnatinsa za ta sa a gaba....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Rahoton IAEA na nuna son kai kuma an shirya shi ne a karkashin tasirin wasu kasashe Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta fitar ya kunshi maimaici da wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da shugaban kasar Masar a birnin Alkahira Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi a yau Litinin. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya isa birnin Alkahira da yammacin jiya Lahadi domin tattaunawa da manyan jami’an kasar Masar. A...
Sojojin Yemen sun kai jerin hare-hare har sau 4 kan filin jirgin saman Ben Gurion tare da wasu wurare masu muhimmanci a cikin Isra’ila Sojojin Yemen sun sanar da aiwatar da hare-haren soji masu tsanani guda hudu a kan filin jirgin sama na Lod, wanda aka fi sani da “Ben Gurion” a haramtacciyar kasar Isra’ila,...
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da suka yi tawaga zuwa wajen raba kayan agajin jin kai a garin Rafah Rahotonni sun bayyana cewa: A rana ta biyu a jere, sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar zirin Gaza da ke fama da yunwa. Shafin yanar...
Wani yaro ɗan shekara 15 ya rasa ransa bayan mahaifinsa ya harbe shi bisa kuskure, yana zaton biri ne. Wannan lamari mai ban tausayi ya faru ne a gonar magidancin inda shi da ɗan nasa suke aiki, a yankin Iye Ekiti da ke Ƙaramar Hukumar Ilejemeje ta Jihar Ekiti. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ekiti, ...
A wani lokaci yau Litini ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai fara ziyarar kwanaki biyu a kasashen Masar da Lebanon. Yayin ziyarar Araghchi zai gana da manyan jami’an Masar da na Lebanon domin tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu dama rikicin yankin. Ziyarar Araghchi a Masar za ta gudana ne bisa gayyatar...
Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban...
Iran ta gargadi kasashen yamma aka daukar duk wani irin mataki kan ta a daidai lokain da ake shirin gudanar da taron gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a mako mai zuwa. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya yi watsi da rahoton...
Jami’ai a Falasdinu sun ce akalla mutum 31 ne sukayi shahada sannan wasu sama da 150 sun jikkata, bayan wani hari da Isra’ila ta kai kusa da wurin rabon abinci a birnin Rafah. Dama shugaban hukumar MDD da ke kula da yan gudun hijirar Falasdinawa, Philippe Lazzarini, ya ce rabon kayan agajin ya zama tarkon...
Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da cewa a ranar hawan arfa na bana, za a fassara hudubar da za a yi da harsuna 34 daga cikinsu da akwai Hausa da filatanci. Wasu harsunan Afirka da za a fassara hudubar ta Arfa da su, sun hada yarabanci, Sawahili, Somali da kuma Amharic na kasar Habasha. A...
Sa’oi kadai da su ka gabata jiniyar gargadi ta kada a cikin garuruwa da sansanonin ‘yan share wuri zauna 300 a HKI saboda makami mai linzami da mutane Yemen su ka harba. Kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniya sun ambaci cewa; an rufe filin saukar jiragen saman a “Ben Gorion” da kuma dakatar da kai da...
Mataimakin shugaban kungiyar Iraniyawa masu bayar da kyautar gabban jikinsu ga mabukata, Umid Qabadi, ya bayyana cewa; A cikin shekaru 25 da su ka gabata, yadda ake kyautar gabban jiki domin yin dashe a duniya ya karu da kaso 70%, kuma Iran ce ta farko wajen yin dashen koda, har ma ana yi ma ta...
A gobe Litinin ne dai za a bude taron karawa juna sani anan Tehran mai taken; Imam Khumaini da batun Falasdinu” wanda zai sami halartar masana na cikin gida da kuma waje. Jawabin bude taro zai fito ne daga shugaban kungiyar kare hakkokin al’ummar Falasdinu, Hujjatul-Islam Muhammad Hassan Rahimiyan, haka nan kuma magajin garin Tehran...
Ya bayyana kamen na su biyo bayan kama wasu alhazai biyu – Ibrahim Umar Mustapha da Muhammad Siraj Shifado a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, da ke Kano a ranar Litinin 26 ga watan Mayu. An kama mutanen biyu ne a lokacin da ake tantance fasinjojin jirgin na Ethiopian Airline ET 940...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Tattauna Darakta-Janar Na Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna da Grossi kan sabbin abubuwan da suka shafi tattaunawar nukiliyar Iran Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya Rafael Grossi sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka shafi tattaunawar nukiliya da kuma dage takunkumin da aka kakabawa Iran a...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Gargadi Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Ta Duniya Da Wasu Kasashe
Iran ta gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya da wasu kasashe Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’ar kasa da kasa Kazem Gharibabadi, ya gargadi hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA da wasu kasashen duniya kan ci gaba da bin tafarki maras kyau da suka...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Taron Kungiyar BRICS Zai Kawo Bunkasar Tattalin Arziki
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Taron kungiyar BRICS wata dama ce ta bunkasa alaka mai karfi ta tattalin arzikin duniya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Halartar tawagar wakilan majalisar dokokin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a zauren majalisar dokokin BRICS wata dama ce mai kima...
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake yi kutse cikin garin Al-Qunaitra na kasar Siriya tare da kafa wurin bincike lamarin da ya fusata al’ummar yankin Sojojin mamayar Isra’ila da suka sake yin Kutse cikin yankunan kasar Siriya sun gudanar da sintiri a yankunan tare da kafa shingen binciken ababan hawa tsakanin Khan Arnabeh da kauyen Jaba...
Gwamna Yusuf wanda a halin yanzu yake kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin 2025, ya bayar da umarnin ware ranar Litinin 2 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu domin bai wa al’ummar damar yin jimami tare da yi wa wadanda suka rasu addu’a. Ya kuma yi kira ga limamai da...
Iran ta tabbatar da cewa ta samu shawarar da Amurka ta gabatar mata daga hannun kasar Oman game da shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya da ake tattaunawa a kai. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa Iran ta samu wani bangare na shawarwarin daga Amurka daga Oman mai shiga tsakani...
Bayanai na nuni da cewa gwamnatin Isra’ila ta hana tawagar ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da dama shiga gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye domin wani taro a birnin Ramallah. Isra’ila dai ta ce ba za ta amince da tawagar ministocin kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya su ziyarci yankin Isra’ila saboda ta lura hukumomin...
Iran ta soki sabon rahoton da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya fitar, tana mai cewa rahoto ne dake kunshe da tuhume-tuhume mara tushe kan shirin nukiliyar kasar. A wata tattaunawa ta wayar tarho da babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa JMI ta gina shirinta na makamashin nukliya ne kan fahinta da kuma kundin tsarin mulkin kasar wanda yayi tir da mamaya da kuma babakere. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a safiyar yau Asabar a hubbaren Imam Ruhullah...
Kamfanin Barakat, mai samar da magunguna a nan JMI ya kaddamarda sabbin magunguna har 23 wanda kamfanin ya samar a cikin gida daga ciki har da riga kafi mai suna HPV. Kamfanin dilancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan ci gaban da kamfanin Barakat ya samu mataki ne mai girma a fagen...
A karon farko, rundunar tsaron Indiya ta tabbatar da cewa ta rasa wasu jiragen yaƙi a yayin arangama mai tsanani da suka fafata da Pakistan a farkon watan Mayu. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Babban Hafsan Tsaro na Indiya, Anil Chauhan, a taron Shangri-La Dialogue, babban taron tsaro na Asiya, a Singapore. Tun...
Masu zanga zanga kimani makunni uku da suka gabata a kasar Libya sun bukaci firai ministan kasar Abdulhamid Dubba ya sauka saboda shi ne ya haddasa rikicin da ya faru a cikin yan makonnin da suka gabata a kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa masu zanga zanga kimani 200 sun...