2025-08-12@13:50:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5531
«Matsalar Ruwan Sha»:
Mai ba da Shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da tsohon fira ministan Iraki sun jadadda goyon bayansu ga kugiyoyin gwagwarmaya Mai ba da shawara kan harkokin kasa da kasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da tsohon fira...
“Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi. Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba. Ejah ya ƙara da cewa...
Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun. ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar...
Wani kurtun soja ya soka wani ɗan sanda mai mukamin Constable, Aaron John da wuƙa har lahira a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. Kakakin ’yan sanda na jihar, James Lashen, ya ce wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, da ke gefen birnin Jalingo....
A ranar Juma’a da yamma, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare motar haya a mararrabar Ogbabo, kan titin Itobe-Anyigba a jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da fasinjoji 9. Direban motar da wasu fasinjoji 6 kuwa sun tsere ba tare da an sace su ba. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe...
A gobe Lahadi ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman gaggawa kan halin da ake ciki a zirin Gaza, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya bayyana. Wannan shawarar ta zo ne bayan amincewar majalisar ministocin Isra’ila da shirin firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya hada...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai...
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar a yau jumma’a cewa Jamus za ta dakatar da duk wani izinin fitar da kayan aikin soji da za a iya amfani da su a zirin Gaza, biyo bayan matakin Isra’ila na mamaye Gaza. Da yake magana bayan zaman majalisar ministoci ta Isra’ila da kuma amincewarta da shirin...
Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa Lebanon da yankin gabas ta tsakiya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi hadari a tarihin baya-bayan nan, inda al’ummar yankin ke fuskantar barazanar wanzuwa da kuma ‘yancinsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na yau da kullun, kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince ta bada sama da naira miliyan 156 domin sayen tikitin jirgi na mayar da daliban jihar masu karatun likita har su 184 da suka kammala hutun su a gida zuwa makaranta a kasar Cyprus. Shugaban Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar, Alhaji Saidu Magaji, ya bayyana hakan ga manema labarai...
An shawarci sabbin mataimaka na musamman da su kasance masu adalci da gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa. Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Binyaminu Ahmad Adamu Kafur ne ya bayar da wannan shawara yayin bikin rantsar da sabbin mataimaka na musamman 69 da aka gudanar a Auyo. Alhaji...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar, da ofishin jakadancin kasar a Philippines, sun gabatar da korafi da babbar murya dangane da kalaman da aka jiyo jagoran Philippines na yi game da batun yankin Taiwan na Sin. Kakakin wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, ya ce, yayin ziyarar da...
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Bauchi tare da ba da tallafin Naira miliyan 15 don tallafa wa harkar ilimi. Obi, ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 9:40 na safe. Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno ’Yan...

Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da...
A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya. Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin...
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin. Ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kasar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan rikicin Ukraine da kuma...
Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick....
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda. Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama. ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon...
Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma...
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki...
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji “Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya,...
Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka...
Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da...
Nijeriya ta kasance ƙasa ce, mai girman gaske, wadda kuma ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi, Al-kamar irinsu; Al- Ƙaeda da ISIS da ke aikata ayyukan ta’addancinsu a yankin Sahel ke kutsowa cikin ƙasar, domin aikata ta’addanci. Bugu da ƙari, ba tun yau ne, wasu ƙwararru a ɓangaren tsaro na ƙasar nan, suke yin gargaɗin cewa,...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci da nufin ƙarfafa harkar yawon buɗe ido da hanzarta gudanar da shari’a a faɗin jihar. Shugaban majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ne ya sanar da amincewar majalisar yayin zaman, ta wanda aka gudanar a harabar majalisar da ke Kaduna. Dokar farko mai taken...

Hizbullah Da Amal Na Kasar Lebanon sun Yi Tir Da gwamnatin Kasar Saboda Bukatar Kwance Damarar Hizbullah
Kungiyar Hizbullah da Amal na kasar Lebanon sun bayyan amincewar gwamnatin kasar Lebanon wajen kwance damarar kungiyar hizbullah wani abu ne wanda kasashen waje suka fada masu su yi haka, wanda ya yi watsi da diyaucin kasar Lebanon da kuma cikekken iko a kan kasar. Labarin ya kara da cewa shuwagabannin kasar ta Lebanon sun...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah,...
Kudirin gyaran dokar fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji...

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12. Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce...
Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar. Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa...

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan
Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na...
Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe...
Wasu daga cikin tsoffin kansilolin da suka halarci tattakin sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Abba Kabir Yusuf. A nasa jawabin, Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila ya ce, shi ma yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta hana hakkinsu, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! “Sun ga gwamna Abba zai...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta...
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa...
Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya...
Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da...
Waɗannan bayanai duk suna ƙunshe ne a cikin jawaban da aka gudanar a gangamin wayar da kai game da wannan cuta, wanda ya gudana a Kaduna. Lokacin da ta ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan wannan gangami, Dr. Maimuna Lawal Garba, ƙwararriyar Likita a fannin hanci, kunni da maƙogwaro, ta fara bayanin...

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama
Kasar Sin ta sanar a yau Alhamis cewa ta yi nasarar kammala cikakken gwajin sauka da tashin kumbun binciken a duniyar wata mai dauke da bil adama, a wani yankin gwaji dake gundumar Huailai ta lardin Hebei. Gwajin da aka kammala ranar Laraba na nuni da wani muhimmin ci gaban da Sin ta samu...
’Yan bindiga ɗauke da makamai sun shiga ƙauyen Bimasa a Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato sun kashe mutum huɗu sun jikkata wasu da dama a daren ranar Laraba. Ɗaya daga cikin jagorori a ƙauyen ya yi wa Aminiya ƙarin bayani ya ce, a daren ranar Laraba da ƙarfe 12:40 na tsakar dare ɓarayi suka...
“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna...
Manoma sama da 500 daga gundumomi 15 na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu horo kan kiwon awaki na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi, a wani yunƙuri na rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar al’ummar karkara. An gudanar da wannan horo a Idofian karkashin...
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta bayyana alhinita kan kisan gilla da aka yi wa Umar Abdullahi Hafizi, dalibi da ke matakin karatu na 3 a Sashen Ilimin Zamantakewa (Sociology), wanda wasu masu kwacen waya suka daba wa wuka har lahira a gidansa da ke unguwar Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale. Wannan na ƙunshe...
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti ranar Litinin. An miƙa jaririn ga iyayensa, Mustapha Aliyu mai shekara 29 da kuma Salmatu Lawal mai shekara 22, bayan da jami’an ’yan sanda suka tsananta binciken lamarin. An kashe matafiya biyu da yin...
Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara. An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu...
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bada motocin aiki ga shugabannin hukumomi, jami’an tsaro da wasu manyan jami’an gwamnati a jihar. An gudanar da bikin mika motocin ne a Fadar Gwamnati da ke Minna. Gwamna Bago ya bayyana cewa wannan mataki na bayar da motocin aiki na da nufin tallafa wa harkokin sufuri da...
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar...
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar...