An kashe ’yan bindiga 19 yayin daƙile wani hari a Kano
Published: 3rd, November 2025 GMT
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan.
Bayanai sun ce sojojin ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri kan motsinsu a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse.
A sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar, sojojin sun gaggauta kai samame yankin bayan samun rahoto, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar.
“A yayin arangamar, an hallaka ’yan bindiga 19, kuma an ƙwato babura da dama da wayoyin salula guda biyu daga hannunsu,” in ji Kyaftin Zubairu.
Sai dai ya tabbatar da cewa sojoji biyu da ɗan sa-kai guda ɗaya sun rasu yayin fafatawar.
Kyaftin Zubairu ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da sintiri a yankin don kare al’ummomin da ke cikin haɗarin hare-haren masu satar shanu da sauran laifuka.
Rundunar ta kuma shawarci jama’a su kasance cikin shiri da lura, tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargin ba na halas ba ga jami’an tsaro mafi kusa.
A cewar kwamandan rundunar, Birgediya Janar Ahmed Tukur, Rundunar Sojin Najeriya na ƙoƙari wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Kano, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
An bayyana wannan aikin a matsayin wani ɓangare na ci gaba da kare yankunan karkara domin bai wa mazauna ƙwarin gwiwa a wuraren da ake fama da hare-haren ’yan bindiga.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha
Kungiyar likitocin kasar ta Sudan ta kara da cewa; Har ya zuwa yanzu mayakan RSF suna ci gaba da garkuwa da dubban fararen hula a cikin birnin Al-Fasha, sun kuma hana su fita daga ciki.”
Har ila yau kungiyar likitoci ta ce, mayakan na RSF sun kwace motocin da ake amfani da su domin jigilar ‘yan hijira, kuma ta tilastawa wadanda suke kokarin ficewa komawa.
Daga cikin wadanda aka tilastawa komawa cikin birnin na Alfasha alhali da akwai albarusai a cikinsu,wasu kuma suna fama da yunwa.
A ranar Asabar din da ta gabata gwamantin Sudan ta bakin ministar ma’aikatar kula da rayu’ar al’umma, Sulaimi Ishaka tana cewa: Mayakan a RSF sun kashe mata 300, sun kuma yi wa mata 25 fyade.
Haka nan kuma ta kara da cewa; mayakan na RSF suna daukar hotunan laifukan da suke aikatawa suna kuma daga ‘yan yatsu alamar samun nasara.
Ishak ta kuma kwantanta laifin da RSF su ka aikata da cewa ya yi daidai da laifukan “Jinenah’ a 2023 da mutane fiye da 10,000 su ka kwanta dama.
MDD kuwa ta bayyana cewa; Dubban mutanen garin na Al-fasha ne suke gudu a kafafunsu, zuwa wani wuri mai nisan kilo mita 60,cikin yunwa da kishiruwa da kuma cin zarafinsu da ake yi.
A garin Qulu dake yammacin Al-fasha ma mutane sun fada cikin mawuyacin yanayi saboda rashin abinci.
Gwamnatin Sudan da wasu kungiyoyin fararen hula masu zaman kansu,suna zargin HDL da cewa ita ce take taimakawa mayakan na RSF da makamai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza November 3, 2025 Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza November 3, 2025 Girgizar kasa ta yi ajalin gomman mutane a Afghanistan November 3, 2025 Najeriya : tun kafin kalamman Trump muka dauki matakai November 3, 2025 Sudan : Mutane 1,500 sun rasa matsugunansu sakamakon tashin hankali November 3, 2025 UNICEF Tayi Gargadi Game Da Mawuyacin Hali Da Yara Ke Ciki A Gaza November 3, 2025 Hamas Ta yi Watsi Da Zargin Da Amurka Tayi Mata Kan Batun Motocin Agaji A Gaza November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci