2025-09-18@02:13:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 887

«Mawaƙiya»:

    ’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta...
    Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.   Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan...
    Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya. Ali...
    Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa:...
    Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. ‎A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake...
    Harshen Hausa shine kan gaba a yawan masu magana a Afrika ta Yamma ta yadda yake da karbuwa a Nijeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Benin, Gabon, Togo, Afrika ta Tsakiya, Sudan da Saudiyya da sauran su. Hasalima kowace nahiya ta duniya akwai jami’ar da ake koyar da harshen Hausa da Hausanci. Bunkasar Harshen Hausa ya sa...
    Tawagar Sudan karkashin jagorancin babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NISS) Manjo Janar Ahmed Mufadal ta isa Mogadishu babban birnin kasar Somalia a wata ziyarar aiki da ta kai kasar, inda ta gana da shugaban kasar  Hassan Sheikh Mohamud a fadar shugaban kasa dake Mogadishu. Jagoran tawagar ta Sudan Mufadal Sheikh Mohamud ya aike...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD (OHCHR) ta bayyana cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 982 a yankin yamma da kogin Jordan tun cikin watan Octb. Shekara ta 2023. Wannan banda wasu 42,000 da suka tilastawa barin gidajensu daga yankin. Banda haka sun rusa gidajen shaguna da sauran abinda Falasdinawa suka mallaka. Banda haka yahudawan...
    Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba...
    Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa dawowar Jonathan ko Obi na iya sauya tsarin PDP wajen fafatawa da jam’iyyar mai mulki ta APC. Jonathan na da magoya baya masu tsayi da suka daɗe a PDP, yayin da Obi kuma ya fi jan hankalin matasa. Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko za...
    shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita...
    Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa. A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen...
    Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da Shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a birnin Abuja Rahotanni sun suna jami’an tsaro sun kama Abu Ramzi Ibrahim me a gidansa da ke Abuja tun ranar Juma’a. Majiyoyi daga cikin al’ummar Falasɗinu sun ce Ibrahim, wanda dasn Bafalasɗine ne kuma ya yi karatu a...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya isa kasar Saudiyya domin halartar wani babban taro na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi. A yayin da yake jagorantar tawagar diflomasiyya ta kasar Iran, Araghchi ya isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya a jiya Lahadi domin halartar taron kungiyar OIC da za a bude...
    Aƙalla gidaje 70 ne suka ruguje wasu da dama suka lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya a Ƙaramar Hukumar Malam Madori ta Jihar Jigawa. Yankunan da ibtila’in ya shafa sun haɗa da Tonikutara, Gandun Sarki, Gandun Bundugoma da rukunin gidajen Shagari Quarters, bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i...
    Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure. Ya ce gwamnatin jihar ta...
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar. Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa....
    Mutane kimani 60 ne zasu gurfana a gaban kotu a kasar Burtaniya, saboda goyin bayan kungiyar mai goyon bayan Falasdinu, wata :frre Palastine’ wacce kuma gwamnatin ta bayyanata a matsayin kungiyar yar ta’adda. Labarin ya kara da cewa wannan shi ne zanga zangar da aka fi kama mutane tun lokacinda aka fara zanga-zangar goyon bayan...
    Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da...
    “Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a....
    Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa.   Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin...
    Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A...
    Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su....
    Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya...
    An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.   Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida...
    Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara. Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen yi wa masu adawa da ita barazana. Saƙon da ɗan takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023 ya wallafa wannan Talatar a shafinsa na X, na zuwa ne bayan tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da EFCCn...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da gargadi game da hawan keken masu kananan shekaru da rashin biyayya ga fitilun ababen hawa a cikin babban birnin Kano.     Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Samun matasan da ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’ummominsu abu ne da ba kasafai ake samu ba a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bayar da gudunmawarsu wajen ci-gaban al’ummarsu. NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim. Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya  yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.” A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar  Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abba Aragchi ya bayyana cewa kara karfin da dangantaka tsakanin Iran da Saudia yake yi, yana taimakawa zaman lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya kara da cewa Aragchi ya bayyana haka ne a lokacinda ya gana da jakadan kasar Iran a Saudiya Ali Reza Enayati...
    Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da shirin kara kai hare-hare da kuma mamaye birnin Gaza. Masu zanga-zangar dai na dauke da allula da kuma hotunan wadanda ake tsare da...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar.   Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran....
    Yansanda a kasar Burtaniya ta kama mutane fiye da 200 wadanda suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin London. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai a birnin London na cewa mutane kimani 600-700 ne suka fito suka kuma tsaya a wani wuri kusa da majalisar dokokin kasar wanda...
    Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin...
    Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun.   ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke...
    Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da...
    Falasdinawa masu yawa ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin ‘yan sahayoniyya suka kai kan tantuna da gidaje da ‘yan gudun hijira a Gaza Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu masu yawa da sanyin safiyar yau Alhamis a wasu munanan hare-hare da jiragen yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka...
    Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kausasan kalamai kan rahotannin dake cewa tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ziyarci yankin Taiwan na Sin da kiran da ya yi wa kasashen yamma su kulla huldar tattalin arziki da yankin. Wani kakakin ofishin jakadancin ya bayyana a jiya cewa, suna adawa matuka da...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni. Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da...
    Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani zama na gaggawa a jiya Talata, domin tattauna mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza, inda ya mayar da hankali musamman kan fursunonin Isra’ila da ke hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinu. A tsakiyar zaman dai batutuwa biyu ne suka dauki hankali: daya daga kasashen yammacin turai...