2025-09-18@02:16:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 987

«Malam Ibrahim Shekarau»:

    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hakimin Bagaji Odo a Karamar Hukumar Omala ta Jihar Kogi, David Wada. Rahotanni sun ce basaraken ya faɗa tarkon ’yan bindigar ne a ƙauyen Ojuwo Ugweche da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, yayin da yake dawowa daga taron sarakunan gargajiya...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yammacin Turai sun fara amfani da takunkumi kan kasar Iran bisa umarnin  ‘yan sahayoniyya da Amurka Dangane da matakin da kungiyar gungun Turai ta dauka na son sake dawo da takunkumin da ya shude kan kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana...
    Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da...
    Kasar Venezuela ta sami sakon tallafi daga kasar Iran a lokacinda ministan harkokin wajen kasar Vanezuela ya gaba da jakadan Iran a Caracas. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun bayyana cewa zasu kara karfafa dangantaka ta musamman dake tsakaninsu na tsaro da sauran bangariri masu musammancin...
    Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari....
    Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An...
    Shawarar da Iran ta gabatar ga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai zai durkusar da darajar kudin dalar Amurka A jawabin da ya yi a wajen taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a kasar China, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ba da shawarar kafa tsarin hada-hadar kudi ga kungiyar da rage dogaro da kudin dala....
    A cewar sa, yankin Arewa-maso-yamma ya samu kaso mafi girma na ayyuka da ya kai naira tiriliyan 5.97, Kudu-maso-kudu ya samu naira tiriliyan 2.41, Arewa-ta-tsakiya naira tiriliyan 1.13, Kudu-maso-gabas naira biliyan 407, Arewa-maso-gabas naira biliyan 400, yayin da Kudu-maso-yamma (ban da Legas) ya samu naira biliyan 604.   Idris ya ce dukkan waɗannan yankuna suna...
    Sojojin kasar Yemen sun bada labarin kai hari kan wani jirgin daukar man fetur na HKI a arewacin tekun maliya a safiyar yau litinin. Mai magana da yawun sojojin kasar ta Yemen Burgediya Yahyah Saree ne ya bada wannan sanarwan a wani jawabin da ya gabatar a faifai bidiya a safiyar yau Litinin, tare da...
    Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk...
    Sakatare-Janar na Majalisar Hadin Kan Kasashen yankin tekun Farisa ya  bayyana batun kafa Isra’ila babba a matsayin Baban hadari da ke barazana ga dukkanin kasashen larabawa. A wata hira da jaridar Al-Qabas ta Kuwaiti, Jassim Mohammed Al-Budaiwi ya fada a wannan  Lahadin  cewa, kasashe mambobin kungiyar (GCC) sun yi watsi da duk wani buri na...
    Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki...
    Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaɓen ciyammomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar. Jam’iyyar PDP wadda ke mulki a jihar ta samu nasara a ƙananan hukumomi uku ne kacal, a zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Jihar Ribas (RSIEC) ta gudanar. Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram...
      Amma Andrew na jihar Taraba, an kama shi ne a ranar Talata, 26 ga watan Agusta lokacin da jami’an NDLEA da hadin gwiwar jami’an Sojin Nijeriya, da Hukumar Tsaron Daji, da kungiyar matasan Mambila da ‘yan banga, suka kai farmaki a gonarsa mai fadin hekta 71.5 ta tabar wiwi da ke dajin Mayodoga, gundumar...
    Kungiyar Hamas ta yi maraba da Allah wadai da kasashen Turai 6 suka yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka kan Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi marhabin da matakin da wasu kasashen Turai shida suka dauka na yin Allah wadai da wuce gona da iri da...
    Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse. Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar. Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Dokar ta-ɓaci: Fubara...
    Shi yasa ta ce duk kowa daga ciki al’umma yana da irin gudunmawar da zai bada wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar da zai tafi makaranta, ta kuma kara jaddada tsarin nastressing TaRL yana bada dama ga Jihohi su samu kira da sa duk masu ruwa da tsaki. A tasu gabatarwar ta...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake...
    Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka...
    A cewarsa, jami’an NDLEA sun nuna kwarewa da kwarewa wajen gano yadda aka boye kwayoyin. “Wannan lamari ya nuna jajircewar hukumar wajen katse hanyar rarraba miyagun kwayoyi da tabbatar da tsaron al’umma.” Ya rawaito kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris-Ahmad, yana yaba wa jami’an hukumar bisa jajircewa da himma wajen gudanar da aikin....
    Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu.   Shugaban ya kuma koka kan yadda...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙara kuɗin fasfo. Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta ƙara kuɗin fasfo mai shafi 32 zuwa Naira 100,000, yayin da mai shafi 64 ya koma Naira 200,000. Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan...
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa...
    Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar.   Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki.   Masu shirya taron...
    Nafisa wacce ta wakilci Nijeriya a karkashin Kwalejin Tulip International ta Nijeriya, ta buge abokan karawarta fiye da 20,000 daga kasashe 69, ciki har da kasashen Turanci.   Gasar ‘TeenEagle’ babbar gasa ce ta duniya wacce ke bibiyar ƙwarewar ɗalibai cikin harshen Turanci, kaifin basira, da ƙwarewa a salon magana. Daga kanmu, magana ta...
    Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya...
    Rahoton yahudawan sahayoniyya ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa dakile hare-haren dakarun Yemen Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Jerusalem Post ta bayyana a cikin wani rahoto na baya-bayan nan cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fama da babbar matsala ta soji da tsaro, bayan da ta kasa dakatar da hare-haren da Yemen ke...
    A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka...
    A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka...
    Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina. An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina. DAGA LARABA: Abin...
    A yau Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya isar da sako zuwa ga Nestor Ntahontuye, don taya shi murnar zama sabon firaministan kasar Burundi. A sakon nasa, firaminista Li ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, wato Xi Jinping da Evariste Ndayishimiye, an cimma manyan nasarori...
    Hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da duk wasu munanan ɗabi’u da ake gudanarwa a otal-otal, wuraren casu da duk wasu cibiyoyin nishaɗi a Jihar Bauchi. Babban Kwamishinan Hisbah, Barista Aminu Balarabe Isah, ya bayyana haka ne a yayin wani taron tattaunawa da masu otal-otal da wuraren shaƙatawa a Bauchi. Trump ya yi barazanar korar Gwamnar...
    A halin yanzu Sarkin Daura, ya hallara a filin gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya da a bana ake gudanarwa a fadarsa, inda za a gudanar da hawan daba na musamman. Sarkin Daura ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Damagaram daga Jamhuriyar Nijar, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou a fadarsa, albarkacin...
    Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa,...
    Kafofin yada labarai na yahudawan sahayoniyya sun yarda da gazawar dakile Yemen daga ci gaba da ayyukan soji kan Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, wadanda tashar 12 da tashar ta 13 ke wakilta, sun amince da cewa: Hare-haren da makiya ke kaiwa kasar Yemen, ya gaza hana sojojin Yemen harba makamai masu linzami zuwa yankunan...
    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar. Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar...
      Wannan yana samar da lantarki da rage asarar makamashi da kuma samar da kaso 25 na bukatun makamshi na ginin. Haka kuma zai kai ga rage fitar hayakin Carbon tan 500 a shekara.   Baya ga haka, ginin na amfani da tsoffin baturan motoci masu amfani da lantarki, wajen adana makamashi. Ana amfani da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa mafarkinn da HKI take yi dangane da ‘Isra’ila babba” wani rudu ne, wanda ba zai je ko ina ba, amma kuma zai haddasa rashin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya dama duniya gaba daya. Don haka akwa bukatar daukan mataki mai kwari don dakile...
    Gwamnatin Tarayya ta rage farashin jinyar ciwon ƙoda daga kimanin N50,000 zuwa N12,000 a Asibitocin Tarayya — ragin da ya kai kashi 76 cikin 100. Wannan saukin farashi ya samu ne bayan amincewar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda mai ba shi shawara kan harkokin sadarwa da manufofi, Daniel Bwala, ya bayyana a cikin...
    Allah Ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na Jihar Kogi, rasuwa yana da shekara 83 a duniya. Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo, ya sanar da rasuwar a yammacin ranar Litinin, 18 ga Agusta, 2025. Gwamnatin jihar ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian na gudanar da ziyarar aiki a kasar Armeniya domin sanya hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyin da suka dace da moriyar kasashen biyu, da kuma tattauna muhimman batutuwa dangane da kasantuwar Amurka a yankin. Yayin da yake jagorantar wata babbar tawaga, Pezeshkian ya isa Yerevan a ranar litinin a matakin farko...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya barazana ce ga wanzuwar tsaron yankin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya suna wakiltar wata barazana ga wanzuwa tsaro da zaman lafiyar yankin da kuma kasashensu. Idan ba a dakile wannan barazanar ba, to babu shakka yankin zai...
    Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wata barazana da makarkashiyar ‘yan sahayoniyya da Amurka Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwa a ranar 16 ga watan Agusta na tunawa da dawowar fursunonin da aka ‘yantar zuwa mahaifar ta daular...
    Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta ki amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta sanar da kin amincewa da nadin sabon karamin ofishin jakadancin Kenya a birnin Goma da ke gabashin kasar, duba da matakin da ya saba wa ka’idojin diflomasiyya, duba da yadda Kongo ke ganin ci...
    Sarkin Zuru na Jihar Kebbi, ritaya Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami, ya rasu yana da shekaru 81 a duniya. Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Garba Umar-Dutsinmari, ne ya tabbatar da rasuwar mai martaba a cikin wata sanarwa da aka fitar a Birnin Kebbi ranar Lahadi. Ya bayyana cewa Sarkin ya rasu ne...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk. Ya kara...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi haɗin gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci. Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da...
    Kasashe 31 na duniya sun yi Allah wadai da kalaman fira ministan Isra’ila na shirin mamaye yankunan kasashe don kafa ‘Babbar kasar Isra’ila Kalaman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbare kasar Isra’ila” ta janyo suka daga Larabawa da Musulunci. Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen...