Jami’an Iran sun yaba da nasarorin da aka samu a yayin halartar Pezeshkian a taron SCO
Published: 3rd, September 2025 GMT
Jami’an Iran sun yaba matuka da irin nasarorin da aka samu a yayin halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian a taron kungiyar Shanghai (SCO) a kasar China.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran ta yi amfani da tsarin diflomasiyya a bangarori daban-daban a yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekara-shekara a kasar Sin.
Gharibabadi ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon shafin Twitter a jiya Talata, inda ya yi bayani kan abubuwan da suka shafi taron, wanda shugaba Masoud Pezeshkian, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin ya aiwatar da su.
A cewar jami’in diflomasiyyar, halartar babban jami’in gudanarwa na kasar Iran a taron ya nuna yadda kasar take aiwatar da irin wannan salon a sahihiyar diflomasiyya.
Ya kara da cewa, Pezeshkian ya gabatar da jawabai daban-daban guda biyu a taron SCO da SCO Plus, inda shugaban ya jaddada kyakkyawar rawar da Iran ke takawa wajen karfafa hadin gwiwar yankin ta hanyar gabatar da sabbin tsare-tsare.
SCO tana aiki a matsayin babbar ƙungiyar gwamnatocin yanki da ke mai da hankali kan haɗin gwiwar siyasa, tattalin arziki da tsaro.
Kasashen da suka kafa kungiyar a shekarar 2001 sun hada da China, Rasha, Kazakhstan, Kyrgyzstan, Tajikistan, da Uzbekistan. Iran ta shiga kungiyar ne a watan Yulin 2023.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Yemen sun kai hare-hare a kan babbar hedikwatar tsaro ta Isra’ila September 3, 2025 Masar ta yi watsi da wasan sada zumunta da Zambia kan Isra’ilawa na horar da ‘yan wasan kasar September 3, 2025 Pezeshkian: Idan Ba A Hada Kai Ba, Munanan Manufofin Amurka Zasu Hada Har Da Kasar China September 2, 2025 Baqa’i: Tawagar Turai Sun Fara Amfani Da Tsoffin Takunkumai Kan Kasar Iran September 2, 2025 Majalisar Shawarar Musulunci Ta Yi Zaman Na Musamman Kan Shirin Tawagar Turai September 2, 2025 Batun Kwance Makaman Kungiyar Hizbullahi Kokarin Kunna Wutar Fada Ne A Kasar Lebanon September 2, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Kiyashi A Zirin Gaza Cikin Sa’o’i 24 Kacal September 2, 2025 Aragchi Yayi Tir da Kissan Firaiministan Kasar Yemen Da Wasu Ministocinsa September 2, 2025 Fiye Da Mutane 1000 Ne Suka Rasa Rayukansu A Yammacin Sudan Saboda Zaizeyar Kasa September 2, 2025 MDD Tace Yara Kimani 660,000 Ne Aka Hanawa Karatu A Gaza September 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi a kasar labanon a jiya ma ta kai hari a kudancin kasar kuma ta yi sanadiyar mutuwar mauta 4 tare da jikkata wasu guda 3,
Isra’ila ta kai hari da jirgin sama mara matuki kan wata mota a kauyen kafr rumman , kana kuma ta sake kai wani harin a garin kafr sir kamar yadda rahotanni suka bayyana, kuma wadannan hare haren suna zuwa ne kwanaki 3 bayan da sojojin israila suka kai samame ta kasa a kudancin labanon a yankin Nabatiya inda suka kai hari a jiya,
A ranar jumaa da ta gabata ne shugaban kasar ta labanon joseph Aun ya nuna damuwarsa game da ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra’ila ke yi, inda yayi tir da tel aviv game da irin mataken da take dauka na karya yarjejeniyar.
A yan kwanankin nan sakatare janar din kungiyar hizbullah na kasar labanon shaikh Naim Qassem ya jaddada cewa tsayin daka ne karfin labanon, don haka Amurka na matsin lamba ne don ganin an danneta an tauye mata yanci da raunata ta don biyan muradun gwamnati.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci