Firaministan Senegal: Yadda Sinawa Ke Girmama Tarihi Da Kiyaye Labarun Abubuwan Da Suka Faru Da Su Na Da Matukar Burgewa
Published: 3rd, September 2025 GMT
Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi.
Sonko ya ce, duk kasar da ba ta iya tuna abubuwan da suka faru da ita a tarihi za ta yi matukar wahala ta dauki darasi daga abin da ya gabata, kuma tana iya saurin maimaita kura-kurai da kuma shan wuyar tashin hankalin da aka shiga a tarihi.
Sonko ya ce, al’ummar kasar Sin sun tuna da tarihinsu, wanda hakan ya sa ya zama sinadarin hadin kan kabilu, kuma wani muhimmin karfi da ke kara zaburar da jama’ar kasar Sin su kai ga kokarin bunkasa kasarsu, kana ya ce, hakika wannan yana da matukar muhimmanci. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Sin su
এছাড়াও পড়ুন:
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoShugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.
Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.
Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.
Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.
NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.
Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.
Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.
Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.