Aminiya:
2025-08-16@23:19:18 GMT

’Yan sanda sun kama matashin da ya yi garkuwa da kansa a Ondo

Published: 17th, August 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani matashi mai suna Azeez Bello, mai shekaru 29, wanda ya kitsa garkuwa da kansa domin karɓar kuɗin fansa Naira dubu 500 daga hannun iyayensa.

Kakakin rundunar, Ayanlade Olushola, ya bayyana cewa Bello, ɗan asalin garin Ipele da ke Ƙaramar Hukumar Owo, ya yi haka ne bayan mahaifinsa ya ƙi ba shi kuɗin da ya nema don yin kasuwanci.

Majalisar dokokin Gombe ta fara duba ƙudirin ƙirƙirar sabbin gundumomi 13 Zaɓen cike gurbi: An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a Zariya

A ranar 11 ga watan Agusta, Bello ya shaida wa iyayensa cewa zai tafi Ibadan, amma maimakon haka ya ɓoye kansa a Ipele.

Daga nan ya riƙa kiran iyayensa da abokansa yana cewa an yi garkuwa da shi kuma sai an biya kuɗin fansa kafin a sake shi.

Bello, ya ba da lambar asusun banki domin a saka kuɗin fansar.

Amma kafin a biya kuɗi , iyayensa suka sanar da jami’an ’yan sanda.

Jami’an tsaro sun bi diddgin lambar waya, inda suka gano wajen da ya ɓuya, sannan suka cafke shi.

Olushola, ya ce Bello ya amsa laifinsa, kuma idan aka kammala bincike, za a gurfanar da shi a kotu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Garkuwa iyaye

এছাড়াও পড়ুন:

An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna.

Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INEC HOTUNA: Yadda zaɓen cike gurbi ke gudana a sassan Najeriya

Ya bayyana cewa an yi wannan kamen ne domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da zaɓen.

Ya ce suna ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar na da laifi za a gurfanar da shi a kotu.

Kiyawa, ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda.

A gefe guda kuma, ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ra lamunci tashin hankali ko rikicin siyasa a Kano ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano
  • Muhimman Batutuwan Da Za Mu Yi La’akari Da Su Kafin Amincewa Da Bukatun Kirkirar Sabbin Jihohi — Majalisar Dattawa
  • An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza
  • An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi
  • An Biya Falcons Duk Kuɗin Alawus, Kyautar $100,000 Da Gidaje Ga Super Falcons
  • An kama Mai Unguwa kan yi wa yarinya fyaɗe a Gombe
  • An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun
  • Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ
  • ’Yan sanda sun kama matashi kan zargin aikata fashi a Gombe