Sin Ta Dade Tana Aiki Tukuru Kan Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Na Yanki
Published: 31st, July 2025 GMT
Dangane da tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka da aka gudanar a kwanan nan, Guo Jiakun ya bayyana cewa, ana fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da Sin wajen amfani da tsarin tattaunawa kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, don sa kaimi ga bunkasa dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka cikin kwanciyar hankali.
Dangane da batun Falasdinu kuwa, Guo Jiakun ya ce, “manufar kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo ta hakika ta warware matsalar Falasdinu, kuma kasar Sin tana goyon bayan al’ummar Falasdinu wajen kafa kasa mai cin gashin kanta.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.