Aminiya:
2025-11-27@21:55:07 GMT

Mutum 7 sun rasu yayin da tirela ta murƙushe motoci a Madalla

Published: 27th, September 2025 GMT

Aƙalla mutum bakwai ne suka rasu, yayin da wasu guda biyar suka ji rauni bayan wata tirela ta murƙushe motoci biyu a yankin Madalla, da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, a Jihar Neja.

Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar ranar Juma’a, lokacin da wata tirela ta samu matsalar birki, ta yi awon gaba da wasu motoci biyu.

’Yan uwa sun samu Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a fanni iri ɗaya  Matatar Ɗangote ta dakatar da sayar da fetur a farashin Naira

Wani ganau, Saleh Haruna, ya ce kafin aukuwar hatsarin, direban wata motar bas ya bugi wata mota a gabansa, wanda hakan ya haddasa hatsaniya.

A cewarsa, a lokacin ne tirelar ta taho da sauri ta murƙushe su, hakan ya sa wani ɓangare na bas ɗin ya kama da wuta.

A sakamakon haka, mutum huɗu da ke cikin bas ɗin sun ƙone ƙurmus, yayin da sauran suka samu rauni.

An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Lukas da ke Madalla, inda Dakta Ugwoegbu Valentine, ya tabbatar da rasuwar ƙarin mutum uku daga cikin waɗanda suka ji rauni.

Direban tirelar, Sulaiman Rabiu, ya shaida cewa ya taso daga Warri, a Jihar Delta, yana ɗauke da buhun alkama waɗanda zai kai Kano.

Ya ce lokacin da yake saukowa daga Madalla ne birkin motarsa ya ƙi aiki, lamarin da ya janyo hatsarin.

Rundunar ’yan sandan yankin Madalla ta tabbatar da rasuwar mutum bakwai a hatsarin.

Sai dai jama’a a yankin sun koka kan yadda aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kaduna ke tafiya.

Sun zargi kamfanin da ke aikin da gazawa wajen saka alamomi da samar da wuraren tsayawar fasinjoji da motoci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Hatsari

এছাড়াও পড়ুন:

An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia

Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies.

Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci.

An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba

Dokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci gaba ɗaya.

Indonesia na daga cikin ƙasashen da har yanzu ake cin naman karnuka da kyanwa, duk da cewa wasu birane sun daina wannan al’ada a ’yan shekarun nan.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dabbobi sun yaba da sabon matakin, suna mai cewa ya dace da manufofin kare lafiyar al’umma.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce mutane da dama kan mutu da cutar rabies a kowace shekara a Indonesia, inda rahoton Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa mutane 25 suka mutu daga watan Janairu zuwa Maris 2025.

Duk da cewa a yawancin yankunan Indonesia ana kallon karnuka a matsayin dabbobin da ba su da tsabta, wasu ƙananan ƙabilu na ci har yanzu, musamman ma saboda samun naman a farashi mai sauƙi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra
  • Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
  • Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
  • Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano