Aminiya:
2025-09-18@00:43:38 GMT

Mutum 6 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Sakkwato

Published: 24th, August 2025 GMT

Aƙalla mutane shida sun rasa rayukansu, yayin da har yanzu an nemi wasu uku an rasa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Garin Faji na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.

Lamarin ya faru ne lokacin da mazauna yankin ke tsere wa wani harin ‘yan bindiga da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar Alhamis, 21 ga watan Agusta.

An tsinci gawar saurayi a gefen kudiddifi a Kalaba Sarkin Musulmi ya ayyana Litinin 1 ga watan Rabi’ul Awwal

Wannan shi ne karo na biyu cikin kasa da mako guda da irin wannan ibtila’i ya faru, domin a kwanaki shida da suka gabata, mutane huɗu sun mutu a hatsarin kwale-kwale makamancin wannan a Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, waɗanda abin ya rutsa da su sun gaggauta shiga kwale-kwalen ne a ƙoƙarin tsere wa ‘yan bindigar da suka hango sun yi kwanton ɓauna.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Saboda fargaba, mutane da yawa ba sa kwana a gidajensu. Sukan kwana a daji, sai safe su dawo gida. To, a ranar da abin ya faru, suna dawowa ne kwale-kwalen ya kife.”

Kazalika, wani mazaunin ya ce an shiga zaman ɗar-ɗar ne lokacin da suka hangi ‘yan bindigar na tunkaro su, lamarin da ya sa suka yi gaggawar shiga kwale-kwalen da ta kife a tsakiyar ruwa saboda an yi masa lodin da ya fi ƙarfinsa.

Ɗan majalisar dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rashin tsaro ya tilasta mazauna da dama barin gidajensu suna kwana a jeji.

Ita ma Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Sakkwato (SEMA) ta tabbatar da faruwar hatsarin, wadda ta ce jami’inta sun ceto mutum 19 daga cikin ruwa, yayin da ake ci gaba da neman ragowar wasu mutum uku waɗanda suka ɓace.

Wannan mummunan lamari ya sake jaddada tsananin da mazauna Sakkwato ke ciki, inda wasu ƙauyuka suka zama kufai, yayin da ‘yan gudun hijira ke ƙaruwa sakamakon hare-haren ‘yan bindiga akai-akai.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Kwale kwale Sakkwato kwale kwale

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato

Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.

An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.

Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB

“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.

Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.

Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”

Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.

“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”

Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.

“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”

Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC Na Nasarawa, Aliyu Barde, Ya Rasu
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara