Leadership News Hausa:
2025-11-27@21:36:13 GMT

Kuri’ar Jin Ra’ayi Ta CGTN: Ya Kamata Japan Ta Martaba Tarihi

Published: 15th, August 2025 GMT

Kuri’ar Jin Ra’ayi Ta CGTN: Ya Kamata Japan Ta Martaba Tarihi

A yau Juma’a ne kasar Japan ta gudanar da gangamin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na biyu, sai dai yayin da yake jawabi albarkacin taron, firaministan kasar Shigeru Ishiba, bai tabo batu kan alhakin dake rataye a wuyan kasarsa ba, a matsayinta na wadda ta mamayi wasu kasashen nahiyar Asiya.

A hannu guda kuma ya gabatar da addu’a ga wurin ibadar nan na Yasukuni, a matsayin girmmawa ga wurin ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki yayin yakin duniya na biyu. Kazalika, wasu ministocin kasar sun kaiwa wurin ibadar na Yasukuni ziyarar girmamawa.

Jerin wadannan matakai dai na shan suka, da adawa daga sassan kasa da kasa. Inda wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar game da hakan ta nuna cewa, kaso 64.4 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na adawa da ziyarar ‘yan siyasar na Japan zuwa wurin ibadar. Kana kaso 55.3 bisa dari sun soki lamirin Japan bisa yadda ta kawar da kai daga abun da ya auku na tarihin wurin. Kazalika, kaso 65.2 bisa dari sun soki matakin Japan na sauya bayanai dake kunshe cikin litattafan tarihi masu nasaba da batun. Sai kuma kaso 65.7 bisa dari da suka yi kira ga gwamnatin Japan da ta nemi afuwar kasashen da mamayarta ta cutar tare da biyansu diyya.

Wannan dai batu ya haifar da bayyana matukar rashin jin dadi tsakanin al’ummun nahiyar Asiya, ciki har da al’ummun Koriya ta Kudu, da sukarsu game da hakan ya haura kaso 90 bisa dari. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: wurin ibadar

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano

Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin.

Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon gaba da maza biyu da mata shida.

’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai

Wani ɗan uwa ga waɗanda aka sace, Kabiru Usman, ya ce maharan sun zo ne a ƙafa ɗauke da makamai, suka kuma yi garkuwa da matarsa Umma, ɗiyarsa mai shekara 17, da matar ɗan’uwansa da wasu mata biyu daga Tsundu mai makwabtaka.

Ya ce al’ummar garin sun yi ƙoƙarin daƙile harin amma suka kasa saboda ƙarancin makamai, duk da cewa sun sanar da ’yan sanda da sojoji tun kafin faruwar harin bayan samun bayanan cewa ’yan bindigar na dosar yankin.

Ya roƙi gwamnati ta ɗauki mataki wajen ceto mutanen da aka sace da kuma kare rayukan mazauna yankin.

Aminiya ta yi ƙoƙarin ji ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, sai da har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Isa Chiroma Mafaka Ta Wucin Gagi
  • China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan