An kashe mutum 3 a faɗan ƙungiyoyin asiri a Legas
Published: 28th, August 2025 GMT
Aƙalla mutum uku ne sun rasu, yayin da wani ɗan sanda ya ji rauni a wani rikicin ƙungiyoyin asiri da ya auku a kasuwar Owode Onirin da ke Jihar Legas.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta bayyana cewa tana neman Abiodun Ariori, Shugaban Kamfanin Golden Venture Limited, bisa zarginsa da hannu a rikicin.
HOTUNA: Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki a Japan da Brazil Kotu ta daure dan Shugaban Equatorial Guinea kan sayar da jirgin saman kasarShaidu sun ce ƙungiyoyin asirin biyu sun yi artabu da bindigogi, adduna da kwalabe.
Ɗan sandan da ya ji rauni an garzaya da shi asibiti, inda yake cikin mawuyacin hali.
Kakakin rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Amma ta ce komai ya daidaita tare da wanzar da zaman lafiya bayan da jami’an tsaro suka isa yankin.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Olohundare Jimoh, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa kasuwar, inda suka buɗe hanyoyin da aka toshe yayin rikicin.
“A lokacin rikicin, mutane uku sun mutu a asibiti sakamakon raunukan da suka samu, yayin da wani ɗan sanda ɗaya ke cikin mawuyacin hali a asibiti,” in ji Hundeyin.
Rundunar ta kuma ƙaryata jita-jitar cewa rikicin ƙabilanci ne ya tashi a kasuwar Balogun.
Ta tabbatar da cewar faɗa ne tsakanin wasu ’yan daba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya, kuma ba shi da alaƙa da ƙabilanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ɗan Sanda Faɗa kasuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp