2025-07-08@11:57:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 813
«a safiyar yau»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
A kalla sojojin Najeriya 20 ne su ka kwanta dama daga cikinsu har da kwamanda a wani hari da ake dangantawa kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP. ‘Yan ta’addar sun kai harin ne dai a ranar Juma’ar da ta gabata a kan sansanin bataliya ta 146 dake Malam-Fatori a akan iyakar Najeriya da Nijar a jihar Borno. Wani soja da ya tsira daga wannan harin ya fadi cewa harin ‘yan ta’addar ya dauki sa’oi 3, kuma sun je wurin ne a cikin manyan motoci tare da shammatar sojojin. Kamfanin dillancin labarun Reuters wanda ya ambato sojan ya ce, maharan sun rika harbinsu ta kowace kusurwa, sai dai sun mayar da wuta.Haka nan kuma ya tabbatar da cewa an kashe kwamandnsu. Mazaunan...
Shugaban kasar Kenya William Ruto a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, zai gudanar da wani babban taro na musamman na kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC a cikin sa’o’i 48 masu zuwa tare da halartar shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi da shugaban Rwanda Paul Kagame. Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan tawayen M23 ke ci gaba da dannawa kan birnin Goma inda ake ta musayar wuta. A cewar wasu majiyoyin MDD da na tsaro, sojojin Rwanda da mayakan M23 sun shiga birnin a ranar Lahadi, in ji kamfanin dillancin labaran Faransa. Yakin da ake gwabzawa a kusa da Goma da kuma harbe-harbe da aka yi a birnin ya kuma sa mazauna babban birnin...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare kasar Lebanon daga ha’incin makiya ba wai kawai tawada ne a takarda ba, don haka sun daurawa kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen da suke daukar nauyin yarjejeniyar da aka cimma alhakin take hakki da laifuffukan makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta mata ficewa gaba daya daga yankin Lebanon. Tun daga shekara ta 2000 har zuwa yau, lamarin ya ci gaba da maimaita kansa, domin al’ummar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ci-gaban zamani ya zo da sauye-sauye da dama a fannonin rayuwa daban-daban ciki har da kasuwanci. A yanzu hanyar sadarwa ta zamani, ko intanet, tana taka muhimmiyar rawa wajen tallata haja ko saye da sayarwa da ɓangarori da dama. Tuni ’yan Najeriya da dama suka yi balaguro suka koma intanet da kasuwancinsu. NAJERIYA A YAU: Matakan Samar Da Abinci A Kan Farashi Mai Rahusa A Najeriya DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a? Shrin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan ƙalubale da ke tattare da wannan harka, da damar da ake samu idan an rungume ta, da kuma dabarun yin nasara...

Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar UYemen Sayyed Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi, ya yabawa mutanen kasar kan jajircewarsu wajen yakar makiya Amurka da HKI da kuma saudiya, har zuwa nasarar da suka samu a kansu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Al-huthi yana fadar haka a yau Lahadi, a wani jawabin da aka watsa a kafafen yada labarai na masu gwagwarmaya. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu yakamata mutanen kasar su maida hankali wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da kuma dogaro da kai kan dukkan abubuwan da yakamata ba zasu nemi shi nan gaba daga wajen makiya ba. Mutanen kasar Yemen karkashin kungiyar dai ta yaki kasar Saudiya da kawayenta na tsawon shekaru 8 ba tare da...
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya. SERAP, ta ce wannan karin an yi sa...
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26. Ga jerin rashin ƙoƙarin ƙungiyar a shekarun baya: Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94. United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta...
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Kungiyar kwamishinonin kudi ta kasa ta jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa Ilmin ya’ya mata. Shugaban kungiyar kuma kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Mr Akim Oyebode ya bayyana hakan a lokacin da suka ziyarci Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse. Mr Akim Oyebode ya ce kungiyar tana alfahari da ayyukan raya kasa da Gwamna Umar Namadi ya aiwatar tun hawansa karagar mulki, a sassan jihar ta Jigawan. Yana mai cewar sun ziyarci jihar Jigawa ne domin yi wa Gwamnan ta’aziyyar rashin da aka masa. A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba musu bisa wannan ziyara tare da fatan za su koma jihohinsu lafiya. Usman Mohammed Zaria
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa. Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin. A cewarta gwamnatin ta amince da biyan Asusun Horar da Likita masu neman kwarewa da sauran abubuwan karawa likitoci gwarin gwiwa. Dokta El-Imam ta bayyana cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen ganin dukkan ma’aikatan jinya sun yi fice a aikin da suka zaba, domin dakile yawan barin kasan nan da likitoci ke yi zuwa kasashen waje. Kwamishinan, ya yi kira ga kungiyar da ta ziyarce ta, da ta fahimci...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025. Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan...