Putin ya rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da Iran
Published: 22nd, April 2025 GMT
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta hadin gwiwa daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare da Iran a hukumance, a cewar wata takardar aiki da aka wallafa a yanar gizo a jiya Litinin.
Shugaban kasar Rasha da takwaransa na Iran Masoud Pezeshkian sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a ranar 17 ga watan Janairu bayan wata tattaunawa da bangarorin biyu suka yi a birnin Moscow.
Yayin da a ranar 8 ga watan Afrilun nan majalisar dokokin Rasha ta Duma ta amince da yarjejeniyar kana majalisar dattawan tarayyar kasar suka amince da yarjejeniyar a ranar 16 ga Afrilu.
Bisa yarjejeniyar da aka cimma, kasashen biyu na da burin zurfafa da fadada dangantakarsu a dukkan fannonin da suka shafi moriyar juna, da karfafa hadin gwiwa a fannin tsaro, da hada kai wajen gudanar da harkoki a matakin shiyya-shiyya da na duniya baki daya, wanda ya dace da cikakken kawance bisa manyan tsare-tsare kuma na dogon lokaci.
Kazalika, Putin ya jaddada muhimmancin yarjejeniyar, yana mai cewa, ta zayyana “manufar da aka sanya gaba” na zurfafa hadin gwiwa na dogon lokaci.
Kuma an tsara yarjejeniyar ne domin samar da kwanciyar hankali ga dorewar ci gaban kasashen biyu da ma daukacin yankin Eurasia.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hadin gwiwa
এছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA