Kudaden Musanyar Kasashen Waje Da Sin Ta Adana Sun Kai Fiye Da Dala Tiriliyan 3.2 A Watanni 16 A Jere
Published: 8th, April 2025 GMT
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, ya zuwa karshen watan Maris na bana, yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana ya kai dala tiriliyan 3.2407, adadin da ya karu da kashi 0.42%, wato da dala biliyan 13.4 bisa na makamancin watan Fabrairu. Hakan ya sa yawan kudaden ya kai fiye da dala triliyan 3.
An kuma bayyana cewa, a watan da ya gabata, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, inda jerin manufofin da aka bullo da su bisa yanayin da ake ciki da wadanda za a dauka bisa sauye-sauyen da ake fuskanta, na ci gaba da nuna tasirinsu a kan yakini, kuma duba da ingantacciyar bunkasar da ake samu, matakan suna kara tabbatar da yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana a cikin yanayi mai dorewa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Yawan Wutar Lantarkin Da Sin Ke Iya Samar Ta Amfani Da Karfin Ruwa Ta Kai Matsayin Koli A Duniya
A gun taro karo na 28 na kwamitin madatsar ruwa na duniya da ake gudanarwa, an bayyana cewa kasar Sin ta cimma nasarar gina madatsun ruwa masu kunshe da fasahar zamani da dama, kuma ci gaban da take samu a bangaren kirkire-kirkire, da nasarorin da take samu a fannin gudanar da harkoki masu masaba da hakan na jawo hankalin kasa da kasa.
Ya zuwa yanzu, Sin ta riga ta kyautata aikin na’urorin sa ido kan kananan madatsun ruwanta dubu 51, da zummar kafa tsarin taurarin dan Adam, da jiragen sama marasa matuka, da na’urar rada, da tasoshin doron kasa, da na’urorin karkashin ruwa, da na’urorin sa ido bai daya. Ban da wannan kuma, Sin ta fara aikin gwaji a wurare 12, game da madatsun ruwa masu amfani da fasahar zamani, matakin da zai ciyar da aikin gina madatsun ruwa irin wadannan gaba.
Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 Sanata Adamu Aliero Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Tallafi Ga Ƙananan Hukumomi Takwas A KebbiAn ce, ya zuwa yanzu, yawan madatsun ruwa, da yawan wutar lantarki da za su iya samarwa, dukkansu ya kai matsayin koli a duniya, kuma Sin ta taka rawar gani wajen tinkarar bala’un yanayi, matakin da ya zama abun koyi ga dukkanin fadin duniya.
Ya zuwa karshen shekarar 2024, yawan madatsun ruwa da Sin ta gina ya kai fiye da dubu 94, adadin da ya kai matsayin koli a duniya, yayin da yawan wutar lantarki da za su samar ta amfani da makamashin ruwa zai kai kilowatts miliyan 435, kana yawan wutar lantarkin da za a samar a kowace shekara zai kai kilowatts duk sa’a tirilyan 1.42, adadin ya kai kashi 57% bisa dari da Sin za ta samar ta amfani da makamashi mai tsabta. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp