Hamas Ta Yaba Da Ma’aikaciyar Kamfanin Microsoft Wacce Ta Fallasa Yadda Kamfanin Yake Taimakawa HKI
Published: 6th, April 2025 GMT
Hamas Ta Yaba Da Ma’aikaciyar Kamfanin Microsoft Wacce Ta Fallasa Yadda Kamfanin Yake Taimakawa HKI
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yabawa ma’aikaciyar kamfanin kayakin lantarki da kuma sadawar ta Microsof mai suna Ibtihal Abussad wacce ta fallasa kamfanin a bikin cika shekaru 50 da kafa shi, a dai dai lokacinda daractan kamfanin mai kula da sashen AI kirkirerren fasaha Mustafa Sulaiman yake jawabi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa Abussad ta tilastawa daraktan yanke maganarsa, inda ta fara cewa abun kunya ne kamfanin Microsuft yana taimakawa HKI da fasahar Ai ko kirkirerren fasaha a kissan kiyashin da take yi a gaza. Ta kuma fallasa yadda manya manyan kamfanonin sadanarwan da kuma kayakin lantarki suke da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ke faruwa a Gaza.
Daga karshen kungiyar Hamas ta bukaci sauran masana irin Ibtihal su koyi jarunta wajenta su kuma fallasa wadanda suka tabbatar da suna da hannu a yakin gaza.
Ya zuwa yanzu dai HKI ta kashe falasdinawa kimani 50,700 tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HOTUNA: Yadda aka dawo da ’yan Najeriya 203 daga Libya
Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya.
(Hoto: Onyekachukwu Obi).