Dakarun Gwagwarmayar Yemen Sun Kai Hare-Haren Daukan Fansa Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 19th, April 2025 GMT
Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila
Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da Vinson, gami da harbo jirgin sama kiran MQ-9.
Dakarun gwagwarmayar sun bayyana a cikin wata sanarwa da Birgediya Janar Yahya Sar’ie ya bayyana a tsakanin miliyoyin mutane a dandalin Al-Sabeen a ranar Juma’a cewa: Sun kai wani harin soji a kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Zulfiqar”. Dakarun kasar ta Yemen sun tabbatar da cewa suna ci gaba da gudanar da mummunan arangama a tsawon kusan watanni biyu da kuma kalubalantar hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen a matakin mayar da martani da kalubalantar hare-haren wuce gona da iri kan kasarsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Ta Ci Gaba Da Kai Hare-Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon
A dai-dai lokacinda jiragen yakin HKI suke ci gaba da kai hare-hare kan mutanen kudancin Lebanon sannan suka ci gaba da keta hurumin yarjeniyar da aka cimma da kungiyar Hizbullah, tana kashe mutanen kasar Lebanon. A wani bangare kuma Sojojin UNIFEL suna fuskantar turjiya daga mutanen kudancin kasar ta Lebanon.
Jaridar Arba News ta kasar Saudia ta bayyana cewa mutane a yankin sun hana sojojin UNIFEL shiga wasu unguwanni a yankin don gudanar da bincike a cikin gidajen mutane.
Labaran da suke fitowa daga irin wadannan yankuna sun nuna cewa muatne sun hana sojojin nUnufel shiga wasu unguwanni, sai sun kawo sojojin kasar Lebanon .
Sojojin sun dage saisun shiga amma mutane sun hansu shiga a sannane suka fara amfani da teas gas ko iska mai sa hawaye don tarwatsa su. Wannan bai yi amfani ba.
Gwamnatin kasar Lebanon ta bukaci a tsawaita lokacin wanzuwar sojojin UNIFEL a kudancin Lebanon amma ta bayyana a fili sojojin suna aiki wa HKI da Amurka ne.