Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas
Published: 20th, April 2025 GMT
Kawo yanzu an samu aƙalla mutum biyar da suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar ruftawar wani bene mai bene mai hawa uku da ya ruguje a unguwar Ojodu-Berger da ke Jihar Legas.
Haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe 09.45 na safiyar ranar, inda hukumar kai ɗauki gaggawa tare da taimakon ’yan sanda suka gano cewa wani gini mai hawa uku ɗauke da gidan abinci da mashaya ne ya ruguje.
Jami’in hukumar bayar da agajin, Ibrahim Farinloye, ya ce daga faruwar lamarin zuwa yanzu an ceto mutane 20 jimilla da suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.
“Sai dai abin takaicin shi ne cikin gawawwakin mamatan biyar da aka samu akwai mata uku da maza biyu.”
Shi ma da yake nasa jawabin a ranar Lahadi, babban Sakataren hukumar LASEMA, Olufemo Oke-Osanyintolu, ya ce mamatan biyar da aka samu an killace su a ɗakin ajiyar gawawwaki na asibiti.
Da farko dai babu labarin mutuwa, sai dai an samu asarar dukiya, amma yanzu bayan ci gaba da aikin ceto, an gano gawawwaki a cikin waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin baraguzai.
’Yan sanda da hukumar kai dauƙin gaggawa sun ci gaba da bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.
Jami’ai na hukumar LASEMA na ci gaba da binciken baraguzan ginin da nufin gano ko da sauran mutane a ciki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Legas Ruftawar gini
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp