Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE).

A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), LEADERSHIP ta Lahadi ta gano cewa har yanzu Gwamntin Jihar bata fara biyan mafi karancin albashin ba.

An samu tsaikon yin hakan ne saboda niyyar ita gwamnatin ta dauki su Malaman makaranta matsyin kwararru ta cire daga tsarin albashi na ma’aikatan gwamnati,inda za ta fara biyansu da tsarin albashi na Malaman makaranta(TSS).

Kamar yadda Shugaban kungiyar kwadago na Jihar NLC,Okoro Ogbonnaya, ya ce kungiyar da bangaren Malaman sun amince tare da gwamnati cewar tsarin albashi na Malaman makaranta wato TSS shi ne abu mafi dacewa ga mabobinsu na kungiyar.

Ya ce gwamnati tana son ta kaucewa yanayin da za’a iya shiga na bayan ta fra biyan mafi karancin albashin, kungiyar kuma ta fara maganar a biya su da tsarin albashin Malaman makaranta na TSS.

A Sakatariyar Kungiyar an samu labarin cewa ranar Jumma’a Shugaban Madu,ya yi wata tafiyar data shafi tsarin albashin Malaman makaranta wanda sun dade da bukatar a biya su da shi wato TSS.

Wata majiyar da bata bukaci a bayyana ta ba, ta ce lamarin biyan sabon tsarin albashi na Malaman makaranta gab ake da a fara shi.”

Hakanan ma, gwamnatin Jihar Kaduna ta bada dalilan da suka sa bata fara biyan sabon mafi karancin albashi ga Malaman makarantar Firamare ba a Jihar Kaduna.

Da yake zantawa da wakilinmu mai ba gwamna shawara na musamman kan kan harkokin ma’aikata,Adamu Samaila,ya bayyana dalilin da yasa ba a fara biyan sabon albashin ba,akan yadda ake tantance su Malaman.

Samaila ya ce, “A yanzu dai ba mu fara biyan sabon ga Malamn Firamare saboda lamarin tantance Malamai da ake yi mafi karancin albashin ba.Muna tantance Malaman Firamare; saboda hakan ne zai sa mu san adadin Malaman da muke da su.

“Bayan duk mun kammal abinda muke yi yanzu za mu samu Kungiyoyin NLC, da NUT da sauran wadanda suke da ruwa da tsaki saboda biyan sabon mafi karancin albashi.”

Daya daga cikin Malaman makarantar da yace sunasa Sani ya yi kira da gwamnati ta duba irin halin da Malaman suke ciki,saboda cire tallafin mn fetur.

“Ya ce a matakin albashi na 7, a mu wadanda muke da satifiket na NCE, ana biyanmu albashin Naira30,000 kafin a kara mana Naira15,000 albashin ya kaitotaling Naira 45,000 yayin da kuma wanda ya kammala Jami’a da ke matakin albashi na 8 yana amsar albashin Naira 49, kowane wata a Jihar kaduna.Don Allah ba a biya mu sabon mafi karancin albashi ba. Don Allah ku fadawa gwamnati ta yi hanzarin yin hakan kamar yadda ya ce,”.

A Jihar Yobe ,Malamin makarnta ya ce Kananan Hukumomin 17 basu biya su albashin shekara biyu ba’.

Kamar yadda daya daga cikin Malaman da abin ya shafa da baya son a ambaci sunansa cewa ya yi, “Muna da yakinin Gwamna Buni saboda kulawar da yake da lamarin ilimi da ci gaban matasa, muna sa ran zai shiga cikin lamarin ba da dadewa ba.”

A takardar korafin da suka rubutawa Gwamna sun ce, “Mu Malamai 25 da muka sa hannu a wannan takarda muna bayyana maka irin cikin halin kuncin da muke ciki.Duk da yake an dauke mu a matsayin Malaman makaranta a karkashin Hukumar kula da ilimin bai daya ta Jiha tun ranar 31 ga watan Mayu 2022, har yanzu ko kwabo ba a bamu ba da sunan albashinmu.

“A matsayin mu na Malaman makaranta, mun maida hankalin mu ne kan samarwa ‘yaran Jihar Yobe ilimi mai nagarta,sai dai kuma bajintar ta mu tana dusashewa saboda rashin biyan mu albashi.

“Mun yi hakuri har zuwa shekaru biyun da suka gabata,lamarin karancin kudi da tsadar rayuwa abin na matukar damunmu .Yawancin mu da kyar muke iya tafiyar da rayuwa, yayin da wsu daga cikinmu suna yin wasu ayyukan domin su taimakawa iyalansu kamar yadda ya bayyana,”.

Malaman sun yi kira da gwamnan yayi amfani da mukaminsa domin yasa ayi bincike akan lamarin ya kuma tabbatar,da cewar an biya su albashin shekara biyu da suke bin bashi.A namu ganin wannan mgana ba wadda za ayi wa rikon sakainar kashi ba, kamata ya yi a dauki matakin da ba dadewa zai yi ba domin mu kadai muka san matsalolin da muke fuskanta.

“Ina son in yin amfani da wannan dama mu sanar da kai,ya mai girma, muna son nuna jin dadinmu akan yadda kake sauararen kukan wadanda suke neman taimako.Muna da yakinin za ka dauki mataki bada dadewa ba domin ka ceto ‘ya’yan al’ummar wannan babbar Jihar.”

Da aka tuntube shi Shugaban Kungiyar Malaman makaranta ta Jihar, Honorabul Ado Idriss, abinda ya ce shi ne, “Sun tuntubi Shugabannin Kananan Hukumomi akan yiyuwar biyan albashin Naira30,000 a lokacin amma sai suka ce basu da isassun kudaden da za su fara biyan albashin.

“Amma kamar ya ce idan suka ci gaba da, yin maganar sai an fara biyan sabon albashin, za su yi maganar tntance ma’aikata.Amma kuma takwararmu ta (NULGE), maganar gaskiya sun ki amincewa da hakan,saboda suna tsoron bayan an kammala binciken abin zai shafi ma’aikatansu.

“Don haka sai suka ce maimakon ita tantancewar,su ci gaba da biyan Naira 18,000 a matsayin mafi karancin albashi lamarin da mu bamu da cewa in banda mu amince da shi zabin na su.”

Kungiyar a Jihar Borno ta bayyana gwamnatin a shekaru shida da suka wuce tana biyan Naira 30,000 mafi karancin albashi ga Malaman makaranta, ba da dadewa bane ta fara biyansu Malaman makaranta Naira70, 000 a matsatin mafi karancin albashi.

Wani babban jami’I na Kungiyar NUT a Jihar da bai son a ambaci sunansa, ya bayyana sauran Malaman makarantar da ba a fara biyansu Naira 70,000 wadanda gwamnatin Jihar ta dora kan sai sun samu horo na wata uku,daga nan kuma sai a fara biyansu mafi karancin albashi.

A Jihar Neja Shugban Kungiyar Malaman makaranta NUT, Mohammed Akayago, ya ce an fara biyansu sabon mafi karancin albashi na Naira 80,000.

Ya bayyanawa Jaridar LEADERSHIP ta Lahadi ya ce sabon mafi karancin albashi kamar yadda Gwamnan Jihar ya sanar an fara biyan Malaman makaranta na kowane bangare na Malamai Naira 80,000.

Kungiyar Malaman makaranta NUT a Jihar Imo ta ce ta yi tarurruka da gwamnatin Jihar wanda suke fatan hakan zai sa ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 70,000.

Kamar yadda Shugaban Kungiyar NUT Chigozirim Emeakayi ya bayyana, da akwai alamun tattaunawar da aka fara a watan Fabrairu zai iya haifar da dai mai ido.

Shugaban Kungiyar kwadago ta kasa NLC, Uche Nwaigwe, shi ma ya yi magana kan irin ci gaban da Kungiyar Malaman makaranta ta samu.

Kwamishinan ilimi Farfesa Bictor Nwachukwu, ya ce a matsayin gwamnatinsu da ta san abinda ya dace ta yi musamman ma ma’aikata da suka hada da Malman makaranta, cewa ya yi ko shakka babu ba za su ba mara da kunya ba.

Kungiyar Kwadago reshen Jihar Sakkwato ta musanta bayanan da suke nuna Gwamnatin Jihar bata fara biyan mafi karancin sabon albashi ban a Naira70,000, maganar da kungiyar tace abin babu kanshin gaskiya domin haka ayi watsi da shi.”

Shugaban Kungiyar kwadago na Jihar, Aliyu Abdullahi Jangale, ya yi watsi da lamarin da ake ta’allaka shi da Shugaban Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi na kasa NULGE, Ali Haruna Kankara,wanda ya ce Jihar Sakkwato na daga cikin Jihohin da basu fara biyan mafi karancin albashi ba.

“Ya ce Jihar Sakkwato ita ce Jiha ta farko data fara biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000 a duk fadin Nijeriya.Ta fara biya ne a watan Janairu na wannan shekarar kamar yadda Jangale ya bayyana “.

An fara biyan sabon albashin inda aka biyan Makaman makarantar Sakandaren ‘yanmata daga Nana Asma’u,sai makarantar Sakandare ta Sultan Atiku,da kuma makarantar Yahaya Gusau da aka tattauna da wakilinmu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: sabon mafi karancin albashi biyan mafi karancin albashi Kungiyar Malaman makaranta fara biyan mafi karancin na Malaman makaranta tsarin albashi na ma Shugaban kungiyar Shugaban Kungiyar kungiyar kwadago biyan sabon mafi fara biyan sabon Kungiyar kwadago gwamnatin Jihar a fara biyansu albashin Naira ta fara biyan an fara biyan a fara biyan Kungiyar ma kamar yadda da gwamnati

এছাড়াও পড়ুন:

NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan ƙasar Indiya tare da wasu mutane uku bisa zargin shigo da ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta darajarsu ta kai naira biliyan uku (N3bn) zuwa cikin ƙasar.

A cewar NDLEA, wannan shi ne kamen ƙwayoyi mafi girma da hukumar ta yi a cikin shekarar nan, lamarin da ke nuna yadda safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙaruwa a ƙasar.

Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa jami’anta sun kama mutanen ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, bayan sun samu bayanan sirri da suka taimaka wajen gano su.

NDLEA ta bayyana cewa ƙwayoyin Tramadol ɗin da aka gano an shigo da su ne cikin kwalaye a matsayin maganin multivitamins, yayin da ake ƙoƙarin fitar da su daga filin jirgin a wasu manyan motoci.

“Ƙwayoyin da aka kama ba su da wata alaƙa da amfani na lafiya, waɗanda aka shigo da su a ɓoye a matsayin maganin rage kasala da ƙara kuzari (multivitamins),” in ji sanarwar NDLEA.

Rahotanni sun nuna cewa a da likitoci na bayar da Tramadol ne don rage zafi da raɗaɗin ciwo, amma yanzu ta zamo annoba musamman a tsakanin matasa, wadda ke haddasa mummunan maye da illa ga lafiya.

Hukumar ta nuna damuwa game da yadda yawan masu amfani da Tramadol ke ƙaruwa ba wai a Najeriya kaɗai ba, har ma a wasu ƙasashen Afirka, duk da illolin da ƙwayar ke haddasawa, kamar matsalolin taɓin hankali ko ma rasa rai gaba ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • Bida Poly ta kawo sojoji su kula da jarrabawar ɗalibai
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • Kundin Bajinta na Guinness ya taya Hilda Baci murna