Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja
Published: 21st, April 2025 GMT
An tabbatar da rasuwar mutum uku tare da asarar gonakin shinkafa da faɗinsu ya kai hekta dubu 10 a Jihar Neja a sakamakon mummunar ambaliyar ruwa.
Wannan ibtila’i ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mikawa, sakamakon sakin ruwa daga Madatsar Ruwa ta Jebba.
Shaidu sun bayyana cewa ambaliyar ta yi ɓarna sosai a gonakin yankin.
Shugaban Ƙungiyar Raya Yankin Kede, Abdulraham Abdulƙadir Kede-Wuya, ya ce gonar shinkafarsa mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda suka salwanta a ambaliyar.
Gobara ta ƙone gidaje sama da 100 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar ChadiYa ce, “gonata mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda ruwan ambaliyar ya shanye, Sannan akwai sauran masu gonaki. Duk gonakin da bain ya shafa sun kai lokacin girbi. Ba mu san abin da ya da suka saki ruwan a irin wannan lokaci ba tare da sanar da al’umma ba.”
Wani manomi a yankin, Ibrahim Ndako, ya bayyana ambaliyar a matsayin bala’i, yana mai kira ga hukumomi su kawo musu ɗauki.
Ibrahim ya bayyana cewa, “Irin asarar asarar rayuka da maƙudan kuɗaɗe da wahalhalun da manoman rani suka tafka a sakamakon wannan abu, da wuya a iya mayar da shi.”
Ya ce yawancin manoma sun zo yankin ne daga jihohi Kebbi, Sakkwato, Zamfara Kano da Borno, domin yin noman rani a yankin, amma yanzu an jawo musu asarar.
Aminiya ta samu labarin cewa wasu daga cikin manoman sun fara girbi a lokacin da ambaliyar ta auku.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Ibrahim Aufu Hussaini ya ce an samu asarar rayukan ne a lokacin da wani kwalekwale ɗauke da su yake ƙoƙarin tsallake kogi da su bayan ambaliyar.
Ya bayyana cewa hukumar tana ci gaba da bincike domin tantance girman asarar da aka yi a sakamakon ambaliyar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya asara Manoman rani ruwa a ambaliyar
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria