Kasashen Turai na E3 sun goyi bayan tattaunawar Iran da Amurka
Published: 14th, April 2025 GMT
Kasashen turan nan guda uku da ake wa lakabi da E3, sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake tsakanin Iran da Amurka.
Ministan Birtaniya mai kula da yammacin Asiya Hamish Falconer ne ya bayyana hakan inda ya ce Birtaniya tare da Faransa da Jamus na goyon bayan sasanta batun nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya.
A cikin sakon da ya wallafa, Falconer ya yaba da tattaunawar da akayi a babban birnin kasar Oman na Muscat a matsayin “muhimmiyar mataki na farko.”
Kuma a cewarsa “Birtaniya, tare da kawayenta na E3, a shirye suke don tallafawa tattaunawar.
A cikin 2018 a lokacin mulkinsa na farko, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma a baya kan shirin nukiliyar Iran da kuma lafta mata tsauraren takunkumai amma kuma ya nuna aniyar kulla sabuwar yarjejeniya don maye gurbin waccen ta 2015.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
Daga Bello Wakili
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi.
’Yan ta’addan sun kai hari makarantar ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar.
Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja.
An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu.
Shugaba Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an kubutar da dukkan mutanen da ’yan ta’adda suka sace.
Ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.
“Ina farin cikin cewa an samu dukkan ’yan mata 24. Ya zama wajibi mu ƙara tura jami’an tsaro yankunan da ke da rauni don hana sake faruwar irin wannan lamari. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafin da ake buƙata don cimma haka,” in ji Shugaba Tinubu.