Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Ribas a ranar Litinin sun harba tiyagas (barkonon tsohuwa) kan masu zanga-zangar lumana don nuna adawa da abin da suka kira rashin shugabanci nagari a kasar. Masu zanga-zangar karkashin kungiyar ‘Take It Back’ sun kuma gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da kuma yadda ‘yansandan Nijeriya ke amfani da dokar leken asiri ta yanar gizo ba ta yadda ya dace ba.

Fedpoly Bauchi Ta Sanya Na’urorin Ɗaukan Hoto ‘CCTV’ Don Daƙile Satar Jarabawa Da Inganta Tsaro Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci Sun zargi ‘yansanda da yin amfani da dokar aikata laifuka ta yanar gizo wajen kai hari ga masu fafutukar kare hakkin dan Adam, ‘yan jarida, da masu tasiri a shafukan sada zumunta a kasar. LEADERSHIP ta lura cewa, rikicin ya fara ne a lokacin da ‘yansandan da suka ajiye motocinsu a kofar filin shakatawa na Isaac Boro da ke Fatakwal, suka umurci masu zanga-zangar da su tarwatse daga wurin taron amma masu zanga-zangar suka ki tarwatsewa daga wurin, inda suka nace cewa, hakkinsu ne da tsarin mulki ya ba su na gudanar da zanga-zangar lumana. Da yake zantawa da manema labarai bayan faruwar lamarin, shugaban kungiyar ‘Take It Back’ a jihar Ribas, Amaye King Amaye ya ce kungiyar za ta sake haduwa domin ganin an ji koken mutanen Ribas.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: masu zanga zangar

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

 

A yayin samamen, kakakin ‘yansandan Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.

 

Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
  • Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A  HKI
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin