Gwamnati Ta Ware Wata 14 Don Kammala Aikin Hanyar Abuja Zuwa Zariya
Published: 18th, April 2025 GMT
Ya yi bayanin cewa aikin hanyar mai nisan kilomita 700 da ya tashi daga Abuja ya wuce Kaduna ya nufi Zariya zuwa Kano zai yi matukar rage yawan aukuwar hatsari da cunkoson ababen hawa da zarar aka kammala shi.
“Muna da sashe na 1, 2, 3. Sashi na 1 yana Abuja da Neja, sashe na 3 kuma yana Kano, kuma sashen Kano da ke tsakanin Zariya zuwa Kano tuni Julius Berger ya kammala shi, don haka gaba daya titin, 350, shi ne kilomita 240 da Julius Berger ya kammala.
“Sauran kilomita 140 da 2, 240 ta 2 shi ne 480. 140 ta 2 shi ne 280. Amma shugaban kasa ba kawai kammala 280 din ne ba, ya ma kara kusan sama da kilomita 11 a rukunin aikin da ke Kano domin jan titin har zuwa filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa ta Malam Aminu Kano. Kuma aikin na ci gaba da gudana a halin yanzu, tare da sauran dan kadan da ya rage a Jihar Kano.
“Shugaban kasa ya kuma bayar da umarnin a sanya turakun hasken wuta mai amfani da haske rana gaba daya. Kuma zuwa yau, shugaban kasa ya bayar da kwangilar karasa sashi na 1 da na 3 na aikin mai nisan kilomita 118 a kan kudi naira biliyan 252.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Barcelona Ta Farfaɗo Zuwa Matsayi Na Biyu Bayan Lallasa Valencia A Johan Cruyff
Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barcelona ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar La Liga ta Sifaniya bayan ta lallasa ƙungiyar Valencia a filin wasa na Johan Cruyff da ke birnin Barcelona.
Fermin Lopez, Raphinha da Lewandowski ne suka zura ƙwallaye shida a ragar Valencia a wasan da aka buga da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Da wannan nasara, Ƙungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tara maki 10 a cikin wasanni huɗu da ta buga a gasar.
Kano Pillars Ta Samu Nasarar Farko A Gasar Firimiyar Nijeriya Ta Bana Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin AroAn yi tsammanin Barcelona za ta fara buga wasan gidanta a sabon filin Spotify Camp Nou da aka gyara, amma sai mahukuntan Ƙungiyar suka yanke shawarar yin wasan a filin Johan Cruyff mai ƙarfin ɗaukar ‘yan kallo 6,000 kacal, wanda mafi yawan lokuta Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta mata Barcelona ke amfani da shi.
A gaba kuma, Barcelona za ta bakunci Newcastle United a filin wasa na St James’ Park a zagayen farko na gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) a ranar 18 ga Satumba. A gefe guda, Valencia za ta karɓi baƙuncin Atletico Bilbao a wasan mako na biyar na La Liga a ranar 20 ga Satumba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp