Ambaliya Ta Hallaka Mutum 30 A Birnin Kinshasa Na Jamhuriyar Demokradiyar Congo
Published: 7th, April 2025 GMT
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa.
Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama.
A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilastawa wasu mazauna ƙasar yin hijira a yayin da wasu suka yi amfani da kwale-kwale kamar yadda jam’in kamfanin dillancin labaran AFP ya shaida.
Wasu daga cikin waɗanda abun ya shafa, sun maƙale a saman gidajensu bayan da ruwan ya mamaye matakalar shiga gidanjensu.
Bugu da ƙari, Ambaliyar ya haifar da cunkoson ababen hawa a birnin da ake fama da yawan zirga zirga.
Mazauna yankin da abin ya shafa sun shaidawa manema labarai cewa sun fusata bayan da gwamnati ta ƙi kawo musu agajin gaggawa.
rfi
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Ambaliya
এছাড়াও পড়ুন:
Kwale-kwale Ya Kife Da Fasinjoji 16 A Karamar Hukumar Taura
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin.
Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen.
Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa.
Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama.
Dr Shuaibu ya bayyana cewa, sauran mutane 9 da ke cikin jirgin har yanzu ba a same su ba a lokacin da ake bayar da wannan rahoto.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, ba a fitar da sunayen waɗanda abin ya shafa ba, amma lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da baƙin ciki.
Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana cewa, za a raba rigunan kariya (life jacket) ga fasinjoji a nan gaba kadan domin kiyaye sake afkuwar lamarin nan gaba.
Ya kuma gargadi matuka kwale-kwale da su kiyaye ƙa’idojin tsaro da kaucewa cunkoson fasinjoji, musamman da yamma a lokacin damina, inda ruwa ke ƙaruwa a kowane lokaci.
Dr Hambali, wanda ya isa wurin da abin ya faru, ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.
Wasu daga cikin mazauna yankin da Rediyon Najeriya ta tattauna da su, sun nemi gwamnatin ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace, tare da inganta hanyoyin sufuri ta ruwa.
Usman Muhammad Zaria