Aminiya:
2025-09-17@23:28:30 GMT

Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi

Published: 19th, April 2025 GMT

Dubban jama’a ne suka hallara domin ɗaurin auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi a Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Ministan Lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, da Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar.

Cikin baƙi akwai Shugaban Kamfanin rukuin Media trust Malam Kabiru Yusuf da sauran manyan baƙi suka hallara a birnin domin ɗaurin auren da kuma naɗin sarautar “Makama Babba I da aka yi wa  tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar.

Masu garkuwa za su mutu ta hanyar rataya a Edo – Okepebolo An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja

Alhaji Bala Ahmad babban limamin Bauchi ne ya jagoranci ɗaurin auren,  wanda Shettima ya kasance a matsayin waliyyin ɗiyar tsohon gwamnan yayin da Yusuf Yakubu Wanka, Chigarin Bauchi, ya kasance waliyyin angon, Sadiƙ Mohammed Wanka a wajen ɗaurin auren.

Bayan ɗaurin auren, Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Suleimanu Adamu ya naɗa wa tsohon gwamnan rawani a matsayin Makama Babba na farko, sannan ya sa baƙar Alkyabba.

 Tun da farko mataimakin shugaban ƙasar, wanda ya sauka a filin jirgin sama na Sa Abubakar Tafawa Balewa ya samu tarba daga gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed da gwamnan Jihar Gombe Mohammed Inuwa Yahaya.

Haka kuma, taron ya samu halartar wasu manyan baƙi da dama, ciki har da tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmadu Mu’azu, mataimakin gwamnan Yobe, Shugaban Kamfanin Media Trust Malam Kabiru Yusuf da sarakunan gargajiya da jama’a daga kowane fanni.

Fadar Sarkin dai ta cika maƙil a yayin da sauran manyan baƙi daga sassa daban daban su ma suka halarci bikin, inda aka ɗaura auren Sadiƙ Mohammed Wanka, da Khadijatu Mohammed Abdullahi Abubakar akan sadakin Naira 300,000.

 A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya bayyana godiyarsa ga Shettima, Pate, Tuggar da Gwamnan Jihar Gombe da sauran manyan baƙi bisa halartar ɗaurin auren da kuma bikin naɗin sarautar tsohon Gwamna a matsayin Makama Babba na Bauchi na farko.

 Ya kuma taya tsohon Gwamnan murna kan abin da ya bayyana a matsayin mafi kyawu kuma wanda ya cancanta saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sadiƙ Mohammed Wanka tsohon gwamnan tsohon Gwamnan Gwamnan Jihar ɗaurin auren gwamnan Jihar manyan baƙi

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Manyan Ma’aikatan FIRS 4 Sun Rasu Sakamakon Gobarar Da Ta Tashi A Ginin Afriland A Legas 
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • An Karrama Farfesa Adamu Gwarzo Kan Gudummawarsa Ga Bunƙasa Ilimin Jami’a A Nijeriya
  • Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
  • Dole sai mun tantance wa’azi kafin a yi —Gwamnan Neja
  • Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin