Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya
Published: 23rd, April 2025 GMT
Wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ake kira Mahmuda tana ci gaba da kafuwa da ƙara ƙarfi tare da addabar jama’a a wasu garuruwa na ƙananan hukumomin Ilesha Baruba da Kemaanji da Kaiama da Baruten na Jihar Kwara.
Bayanai sun ce ’yan ƙungiyar sun sami mafaka ne a gandun dajin Kainji Lake National Park, kuma daga can ne suke kai hare-hare a garuruwan da ke makwabtaka da dajin har ma da wasu sassa na Jihar Neja.
Bayanai sun ce ko a Juma’ar da gabata sai da mayaƙan suka kashe wasu fulani huɗu, ɗan sa-kai da wani saurayi mai shekaru 19.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan ta’addan da suka yi shiga ta kakin soji haye a kan babura sun kai harin ne yayin da ake tsaka da cin wata kasuwar dare, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi sannan suka arce.
Rahotanni na cewa sabuwar ƙungiyar tana kashe-kashe da garkuwa da mutane a ƙauyukan Kemaanji, Tenebo, Baabete, Nuku, da Nanu a ƙananan hukumomin Kaiama da kuma yankunan Yashikira na Ƙaramar Hukumar Baruten gami da yankunan Babana da Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.
‘Za mu tabbatar da tsaro a yankin Gandun Daji na Kainji’Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq yayin wata ziyara da kai wuraren da abin ya shafa tare da manyan jami’an tsaro, ya ce ’yan ta’addan na kai wa ’yan sa-kai harin ne a matsayin ramuwar gayya saboda matsin lambar da suke yi musu.
Da kuma yake jawabi a fadar Sarkin Kaiama, Alhaji Muazu Shehu Omar, gwamnan ya ce za su yi duk mai yiwuwa tare da sojoji da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya a yankin Gandun Daji na Kainji.
Yanzu haka dai mutanen garuruwan da abin ya shafa suna ta yin hijira zuwa wasu wurare, domin guje wa ƙwazzabar ’yan ƙungiyar ta Mahmuda.
Mazauna yankin sun ce dama can ’yan ƙungiyar ta Mahmuda ta taɓa kafa sansani a ƙananan hukumomin Kaiama da Baruten, inda suka nuna cewa babu ruwansu da mutanen gari kuma hakan ya sa mutanen suka saki jiki da su.
Mazauna sun ce da farko Mahmudawan sun soma yaɗa da’awa ta Musulunci, amma daga baya suka fara ɗaukar wasu matasa a matsayin mayaƙa da masu tattaro musu bayanai.
Wani mazaunin yankin ya ce daga baya ne Mahmudawan suka fara yawo da makamai suna kama mutanen gari da kuma yanke musu hukunci har ma da kashe wasu. “Sun fi shekara 5 da fara bayyana”
Ya ƙara da cewa a wannan karon da suka dawo ”Daga gabas da gari zuwa yamma, mutum baya da halin zuwa gona mai nisan kilomita biyu haka.
“Gaba ɗaya na tsorata, kashi 50 cikin ɗari na mutanen gari sun gudu.”
Haka nan kuma ƙungiyar ta Mahmuda ta haramta wa mutanen Kaiama da Baruten noma “kashi 95 cikin 100 na mutanenmu manoma ne.
“To yanzu sun ce ba mu da damar yin noman ka ga dai yanzu mutuwa ta fuskance mu, ba ma yunwa ba.”
“Mun sha ankarar da mahukunta kan ayyukan ’yan ƙungiyar amma ba a ɗauki mataki ba, amma sai a kwanan ne sojoji suka yi musu ruwan wuta a maboyarsu, in ji wani mazauni, Haruna Idirissa.
Wasu rahotanni na cewa ’yan ƙungiyar wani tsagi ne na ƙungiyar Boko Haram da Abubakar Shekau ya jagoranta, da suka fito daga wani sashe na ƙasashen Benin da Nijar, sai dai suna da sassaucin tsaurin ra’ayi.
Mun tanadi tsaro — ’Yan sandaTuni dai Kakakin rundunar ’yan sandan Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi a wata sanarwa da ya fitar, ya musanta ɓullar ƙungiyar, yana mai cewa ko labarin da ake yaɗawa na cewa sun kashe ’yan sa-kai 15 ba gaskiya ba ne.
Sai dai rundunar ta bai wa mazauna tabbacin tanadar tsaro ingantacce domin wanzar da zaman lafiya.
Rundunar ta kuma buƙaci mazauna da su ci gaba da bayar da haɗin kai ta hanyar kiyaye duk wata doka, tana mai kiran da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.
Muna zaune cikin fargaba —BasarakeSarkin Yashikira, Alhaji Umaru Seriki, ya bayyana cewa a yanzu haka suna zaune cikin fargaba saboda ta’adar sabuwar ƙungiyar da ke musu barazana a kodayaushe.
Tun a shekarar 2022 Majalisar Dattawa ta bayyana fargabaA shekarar 2022 ce Majalisar Dattawa ta yi iƙirarin cewa sabuwar ƙungiyar ta samu mafaka a wasu ƙananan hukumomi uku na jihohin Kwara da Neja.
Majalisar Dattawan a wancan lokacin ta yi kira da babbar murya, inda ta nemi hukumomin tsaro da su ɗauki ƙwararan matakai kan ’yan bindigar da duk wani ɓurɓurshi na miyagu da ke addabar yankin Gandun Daji na Kainji.
Aminiya ta ruwaito cewa, Sanatan Kwara ta Tsakiya, Sadiq Umar tare da Mataimakin Bulaliyar Majalisar, Sanata Aliyu Abdullahi mai wakiltar Neja ta Arewa ne suka gabatar da wannan ƙudiri.
A watan jiya ne ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, ya ba da rahoton cewa ’yan sa-kai sun kama wani ɗan bindiga da ya bayar da bayanan sirri kan ayyukan ƙungiyar.
A halin yanzu dai bayan ɓullar Mahmudawa, ƙungiyoyin ta’adda masu tayar da ƙayar baya na ci gaba da ƙaruwa a ƙasar.
Ƙungiyoyin ta’addan da ake fama da su a Nijeriya sun haɗa da Boko Haram, ISWAP, Lakurawa, Ansaru da kuma ta bayan nan Mahmuda.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ISWAP Lakurawa yan ƙungiyar ƙungiyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
“Ana kiransa da suna dokar binciken tntanet ta tsoratarwa, wadda kasashen da suka ci gaba da dama suka dade da yin watsi da ita. A karni na 21, ba za a iya tunanin cewa gwamnatin Nijeriya za ta tauye ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda shi ne ginshikin mulkin dimokuradiyya.”
Atiku ya ce duk wata doka da ke take ‘yancin ‘yan kasa na yin tsokaci mai muhimmanci game da shugabanninsu ko a hanyoyin sadarwar zamani ko ta hanyar magana ba dimokuradiyya ba ce kuma kai tsaye take hakkokin Dan’adam ne.
“A cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata tun bayan da gwamnatin Tinubu ta fara daukan matakan da ke janyo kuncin tattalin arziki da yunwa da bakin ciki ga mutanen Nijeriya, mun shaida zanga-zanga da koke-koke daga ‘yan kasa da ba za su iya daukar mulkin rashin gaskiya ba. Duk da haka, maimakon sauraron ‘yan kasa sai gwamnatin ta zabi hanyar amfani da karfin hukumo da tsoratarwa wadda ta juya lamarin zuwa wani abu daban.
“Lallai abin bakin ciki ne na ganin ana take hakkin ‘yan kasa da kundin tsarin mulki ya tabbatar a lokacin da ya kamata dimokuradiyyarmu ta kasance mai bin tsari. Dole ne mu tunatar da gwamnatin Tinubu cewa babu gwamnati a lokacin da ta kasa kare ‘yancin ‘yan kasarta, komai karfinta kuwa. Yin haka abun ta da hankali ne kuma hakan yana nuna gazawar gwamnati a fili.”
Atiku ya ce tabbas gwamnati na da alhakin kula da doka da oda, babu ingantacciyar gwamnati da za ta harbi masu zanga-zangar lumana da harsashi mai rai ko ta boye a bayan dokoki tana musguna wa ‘yan kasa.
Ya ce rashin kulawar gwamnati Tinubu ga dokar kasa da kuma ci gaba da kin bin umarnin kotu sun zama shahararrun siffofinta mafiya suna a kasar nan a halin yanzu.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kara da cewa tun farkon wannan gwamnati, kungiyar kare hakkin Dan’ada ta Amnesty ta soke wannan gwamnatin da take hakkin Dan’adam.
Ya ce haka ma wasu kungiyoyi masu muhimmanci kamar irinsu kungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya da kungiyar kare ajandar kafafen yada labarai sun yi korafi kan cin zarafin ‘yan jarida da ‘yan kasa ta hannun jami’an gwamnati.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA