ACF Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Da Ta Kawo Karshe Tashe-Tashen Hankula Filato
Published: 7th, April 2025 GMT
Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato.
Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da kananan yara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da wadannan hare-hare tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin jama’ar Jihar Filato.
ACF ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-baci a wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga tare da hada kai da al’ummomin yankin domin dakile barazanar tsaro.
Haka kuma, kungiyar ta nemi gwamnati ta kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma kama wadanda ke da hannu a ta’asar.
Kungiyar ta jaddada bukatar wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato tare da bukatar a hada kai da shugabannin gargajiya, dattawa, kungiyoyi da sauran masu ruwa da tsaki domin dakile lamarin.
ACF ta kuma bukaci al’umma su rika bai wa jami’an tsaro bayanai kan duk wani abu da ka iya kawo matsala.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta sanar da cewa, an kawo karshen Ebola da ta bulla a kasar bayan da aka dauki kwanaki 42 ba tare da an sami mutum daya wanda ya sake kamuwa da ita ba.
A wani bayani da ya fito daga hukumar kiwon lafiya ta duniya ( WHO), ta bayyana cewa, a lokacin bullar cutar an gabatar da mutane 14 masu dauke da ita, an tabbatar da 12 daga cikinsu, sai wasu biyu da ba a same ta a tare da su ba.”
Haka nan kuma hukumar lafiyar ta ce, an sami mutuwar mutane 4 daga cikin wadanda su ka kamu da cutar ta Ebola, wasu mutane 10 kuma sun warke.”
Watanni 9 da su ka gabata ne dai aka tabbatar da bullar cutar a birnin Kamfala bayan da wani mutum da yake dauke da ita ya rasu.
Dajukan da kasar ta Uganda take da su, suna a matsayin matattarar cutar ta Ebola ce, wacce a karon farko ta bulla a cikin kasar a 2000.
A yankin yammacin Afirka cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 11,000 a tsakanin 2013 zuwa 2016.