An Kashe Mutane Da Dama A Tsakiyar Najeriya
Published: 15th, April 2025 GMT
Wasu masu dauke da makamai sun kai hari a wasu kauyuka biyu dake jihar Filato inda su ka kashe mutane 52.
Rahotannin da suke fitowa daga jihar ta Filato sun ambaci cewa wasu makiyaya ne su ka kai harin na ranar Litinin din da ta gabata an kai shi ne a kan yankin Bassa.
Kamfanin dillancin labarun Reuters da ya dauki labarin ya ambaci cewa,an gano gawawwaki 51 daga cikin wadanda aka kashe din, kuma wani adadi mai yawa na mutanen kauyukan sun jikkata.
Ita kuwa kungiyar “Amnesty International” ta ambaci cewa maharan sun kuma rusa gidaje, tare da wawashe kayan da suke cikinsu. Kungiyar ta zargi jami’an tsaron kasar da gajiyawa wajen tabbatar da tsaro.
Jahar Filato ta dade tana fuskantar fadace-fadace a tsakanin makiyaya da mazauna kauyuka, duk da cewa daga baya an sami lafawar al’amurran,amma daga baya ya sake dawowa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi
Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi.
Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya bar Haruna cikin rashin hayyacinsa.
Tinubu ya naɗa tsohon kantoman Ribas da Dambazau a matsayin Jakadun Najeriya ’Yan sandan Borno sun kama matashin da ake zargi da kashe makwabciyarsa da wuƙa“Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata, Karamar Hukumar Warji, Jihar Bauchi, ya riga mu gidan gaskiya bayan rikici mai tsanani da ya barke a bikin radin suna a ranar 2 ga watan Disamba, 2025,” in ji Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin arewa maso gabas.
Ya kara da cewa rashin jituwa tsakanin wasu matasa a wajen bikin ta rikide zuwa fada, lamarin da ya bar wanda abin ya shafa ya suma nan take.
An ce an garzaya da Haruna zuwa Asibitin Gwamnati na Warji, amma ya rasu a yayin da ake masa jinya.
Da aka tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda na jihar, Ahmed Wakili, ya ce yana cikin taro kuma ya yi alƙawarin dawowa da bayani, sai dai bai yi hakan ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.