Abbas Arakci: Tattaunawa Da Amurka Ta Hanyar Shiga Tsakanin Oman Ta Shiga Sabon Zango
Published: 19th, April 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Irna” cewa; An sami cimma matsaya a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka akan cewa a ranar Laraba mai zuwa za a dora daga inda akan tsaya a tattaunawar Nukiliya,”
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kara da cewa; Tattaunawar ta gaba za a yi ta ne a tsakanin kwararru, da zai kai ga shimfida ka’idojin da za a dora yarjejeniyar a kansu.
A yau Asabar ne dai aka yi tattaunawa karo na biyu a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka a cikin ofishin jakadancin kasar Oman dake birnin Rome na kasar Italiya.
Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labari a bakin ofishin jakadancin kasar ta Oman a birnin Rome ya amsa tambayoyi mabanbanta da ‘yan jaridu su ka yi masa, da a ciki ya bayyana cewa; An dauki sa’oi 4 ana tattaunawar, kuma a wannan karon ma, tattaunawar ta yi armashi.
Dangane da tattaunawa ta gaba, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa za ayi ta ne a kasar Oman, kuma a ranar asabar mai zuwa za su sake haduwa domin ganin inda nazarin kwararrun ya isa. Ministan harkokin wajen na Iran ya kora kore cewa Amurka ta bijiro da wata Magana idan ba ta makamashin Nukiliya ba. Ya kuma kara da cewa; Batun makamashin Nukiliya ne aka bijiro da shi, kuma akan shi muke Magana.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Ministan harkokin wajen na
এছাড়াও পড়ুন:
Nazarin CGTN: Ana Kara Bayyana Rashin Gamsuwa Da Sabuwar Gwamnatin Amurka Daga Ciki Da Wajen Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp