An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato
Published: 12th, April 2025 GMT
Rahotanni sun ce an kashe wani uba da ‘ya’yansa biyu a ƙauyen Zogu da ke Gundumar Miango a Ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Kakakin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA), Sam Jugo, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Jos, ya bayyana sunayen waɗanda harin ya rutsa da su kamar haka, Weyi Gebeh a mai shekara 56, da Zhu Weyi mai shekara 25 da Henry Weyi mai shekara 16.
A cewar Jugo, an kashe mutanen ne cikin dare a lokacin da suke barci, inda ya bayyana lamarin a matsayin dabbanci.
Ya ce, “An sanar da shugabannin Ƙungiyar ci gaban Irigwe (IDA) game da wani harin da aka kai ƙauyen Zogu, Miango wanda ya yi sanadin mutuwar wani uba da ‘ya’yansa biyu waɗanda suka haɗa da: Weyi Gebeh da Zhu Weyi da Henry Weyi.
“Wannan harin na baya-bayan nan ya kai ga mutuwar mutane tara a cikin makon nan kaɗai, Ƙungiyar IDA ta nuna rashin jin daɗinta game da taɓarɓarewar al’amura a yankin Irigwe tare da yin kira ga jami’an tsaro da su yi duk abin da ya kamata don daƙile wannan ɓarna a yankinmu tare da kama waɗanda suka aikata laifin don fuskantar shari’a.
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom da rundunar ’yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, har yanzu ba su mayar da martani ga saƙon da wakilinmu ya aika masu ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Operation Safe Haven
এছাড়াও পড়ুন:
Mutun 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano
Aƙalla mutum 21 ne suka rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Zariya zuwa Kano, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar.
Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:23 na safe a unguwar Kasuwar Dogo da ke yankin Dakatsalle.
Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Gwamna ya gargaɗi sarakuna kan mamaye filayen kiwo a GombeHatsarin ya rutsa da wata babbar mota ƙirar DAF mai lambar GWL 422 ZE da kuma motar ɗaukar fasinjoji ƙirar Toyota Hummer mai lambar KMC 171 YM.
FRSC, ta ce bincike ya nuna cewa direban motar fasinjojin ne ya karya doka ta hanyar bin hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya sa suka yi karo da babbar motar.
Bayan aukuwar hatsarin, motocin biyu sun kama da wuta, inda mutane da dama suka ƙone ƙurmus.
Kwamandan FRSC na Kano, MB Bature, ya ce jami’ansu sun isa wajen cikin gaggawa bayan samun rahoto.
Sun kuma kira ma’aikatan kashe gobara na jihar da na tarayya domin kashe gobarar da kuma ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce: “Mutum 24 ne hatsarin ya rutsa da su. Abin takaici, 21 sun rasu, yayin da uku suka jikkata.”
Gawarwakin da suka ƙone an kai su ɗakin ajiye gawa na Asibitin Nassarawa da ke Kano, yayin da waɗanda suka jikkata ke samun kulawa a Asibitin Gwamnati da ke Garun Malam.
Bayan haka, jami’an FRSC tare da taimakon ’yan sanda sun ɗauke motocin da suka tare hanya domin sauƙaƙa zirga-zirgar ababen hawa a titin.
Kwamanda Bature, ya bayyana alhininsa kan wannan mummunan lamari, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu.
Ya kuma yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi.
Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin direbobi su guji karya doka; kamar bin hanya ba daidai ba da tuƙin ganganci, wanda hakan ke haddasa haɗura.
“Wannan lamari abin takaici ne wanda ke nuna muhimmancin bin ƙa’idojin hanya. Mafi yawan haɗura za a iya kauce musu idan direbobi za su kiyaye doka,” in ji Bature.
Ya kuma buƙaci direbobi, musamman na motocin haya, da su guji gudu fiye da ƙima da ganganci a hanya, wanda a cewarsa shi ne babban dalilin da ke haddasa haɗura da asarar rayuka.
Ga hotunan yadda hatsarin ya auku: