Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya

Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Siriya suna ci gaba da samun karuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar ISIS tun daga farkon wannan wata. Hare-hare 13 sun kai sune kan Dakarun Syrian Democratic Foeces ta (SDF) ta Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka da kuma fararen hulan yankunan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka.

A cewar kungiyar kare hakkin bil- adama ta Syria, hare-haren sun bambanta wajen aiwatar da su, daga harin kwanton bauna zuwa na kai hari kai tsaye, wanda ke nuni da yadda kungiyar ta canza yanayin kai hare-hare a yankunan saboda matakan tsaron a garuruwan. Wadannan al’amura sun kuma nuna cewa kungiyar ta’addancin na ci gaba da yin barazana a arewaci da gabashin Siriya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kungiyar ta

এছাড়াও পড়ুন:

Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya  Suke Bukata

Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab.

Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan.

A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar.

A cikin watan maris da ya gabata ne shugaba Al-Sharaa na kasar Syriya ya rattaba hannu a kan wata yarjeniya da shugaban dakarun kurdawan kasar Siriya SDF Mazlum Abdi dangane da hade dakarunsa da sojojin kasar Siriya, sannan yace tsarin tarayya ya sabawa wannan yarjeniyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
  • Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi
  • Sabbin Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci: Nan Ba Da Jimawa Ba, ‘Yan Ta’adda Za Su Ɗanɗana Kuɗarsu – COAS
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kutsa Cikin Quneitra Na Kasar Siriya Tare Da Kafa Shingen Bincike
  • Kungiyar Amnesty International Ta Kafa Hujja Kan Ta’asar’Yan Sahayoniyya A Gaza
  • Gwamnati Ta Kafa Kwamitin Binciken Yawaitar Haɗurran Tankokin Man Fetur A Nijeriya 
  • Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu
  • Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
  • Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya  Suke Bukata
  • Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci Ta Yaba Wa Gwamna Lawal Kan Matakan Yaƙi Da ‘Yan Bindiga A Zamfara