NAJERIYA A YAU: Dalilan Farfaɗowar Boko Haram A Jihar Borno
Published: 14th, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar.
Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar.
Ko mene ne dalilin sake farfaɗowar ƙungiyar ta Boko Haram a wannan lokaci?
NAJERIYA A YAU: Yadda Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Zai Shafi Rayuwar ’Yan Najeriya DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’Wannan ne batun shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa https://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16971864-dalilan-farfa-owar-boko-haram-a-jihar-borno.mp3?download=true
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aikin Tsaro Boko Haram jihar Borno
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro
Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata.
Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba.
Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Najeriya ta ɗora alhakin taɓarɓarewar harkokin tsaronta kan AmurkaLamarin ya faru kasa da sa’o’i 24 bayan mummunan harin da aka kai coci a Eruku, Ƙaramar Hukumar Ekiti ta jihar, inda aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da mutum 30.
Majiyoyin al’umma sun ce an fara yin garkuwa da mutane huɗu, ciki har da ɗan sa-kai, a cikin waɗannan hare-haren.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce maharan daga baya sun kashe manoman shinkafa biyu tare da jikkata wani mutum na uku wanda aka ce ɗan sa-kai ne.
A halin yanzu, gwamnati ta ce ta ɗauki matakan tsaro na musamman a makarantu, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinta na tabbatar da kariya ga ɗalibai.
Matakan dai sun shafi makarantu a ƙananan hukumomin Ifelodun, Ekiti, Irepodun, Isin, da Oke Ero.
Gwamnatin ta ce wannan mataki ya nuna ƙudurinta na dakile ayyukan masu garkuwa da mutane waɗanda za su iya amfani da ɗalibai a matsayin garkuwa daga matsin lambar da suke fuskanta.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi da Ci gaban Ɗan Adam na jihar, Dr Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce matakan sun shafi makarantun kwana a Irepodun.
Sanarwar ta ƙara da cewa matakin zai ci gaba da kasancewa a yankunan har sai an samu cikakken tabbacin tsaro kafin a dawo da harkokin yau da kullum.
A ranar Litinin, ’yan bindiga sun kai hari a makarantar GGCSS Maga, Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu ta Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum ɗaya tare da yin garkuwa da ɗalibai 25.