Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kona Yara Da Mata A Harin Da Suka Kai Khum Yunis Na Gaza
Published: 17th, April 2025 GMT
Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza
Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu,
Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama.
Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata tare da kona gawarwakinsu sakamakon yin luguden makamai masu linzami kan sansanoninsu musamman wadanda suke rayuwa a cikin tantuna a yankin al-Mawasi da ke yammacin Khan Yunis.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
Aƙalla sojoji 13 aka cafke a ƙasar Benin bayan yunƙurin da juyin mulki da suka yi bai yi nasara ba.
Majiyoyin tsaro da na soja sun bayyana cewa dukkan waɗanda aka kama sojoji ne masu aiki a halin yanzu, sai mutum ɗaya da ya taɓa yin aiki a rundunar amma ya yi ritaya.
Kama su ta biyo bayan sanarwar da aka yi a talabijin na ƙasar da safiyar Lahadi, inda sojojin suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon tare da rushe dukkan cibiyoyin gwamnati.
Jami’an da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa, sun ce sun karɓe mulki, sun rufe iyakokin ƙasar tare da dakatar da jam’iyyun siyasa.
Sai dai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Shugaba Talon yana cikin ƙoshin lafiya, kuma dakarun da suka tsaya kan gaskiya na dawo da doka da oda.
Gwamnati ta bayyana lamarin a matsayin aikin “tsiraru mutane” da ba su da tasiri.
“Wasu ’yan tsiraru ne kawai da ya mamaye talabijin. Rundunar sojan ƙasa na sake karɓar iko. Birnin da ƙasar gaba ɗaya suna cikin tsaro,” in ji sanarwar fadar shugaban ƙasa.