Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba

Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila.

Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza.

Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda ake tsare da su da hakan ke kara masifar azabtarwar da ake gana musu. Haka kuma wanda ake tsare ana yi masa fyade a gaban ’yan uwansa da ake tsare da su, da nufin wulakanta shi da kuma rusa tunaninsa, da hakan ke kara tsoro da firgici a tsakanin sauran wadanda ake tsare da su.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da ake tsare da su

এছাড়াও পড়ুন:

Australia ta gargadi Isra’ila game yunkurin mamaye birnin Gaza

A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai ga barkewar matsaloli na jin kai a yankin.

Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wang a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Australia ta yi kira ga Isra’ila da kada ta bi wannan zabi, wanda zai kara ta’azzara matsaloli a zirin Gaza, tana mai jaddada cewa, tilasta tsugunnar da  Falastinawa a wajen yankunansu ya sabawa dukanin dokoki na kasa da kasa.

Wang ta sake nanata kiranta na “tsagaita bude wuta, da shigar da kayan agaji ba tare da wani cikas ko tarnaki ba, da kuma sakin fursunonin da Hamas ke tsare da su tun watan Oktoban 2023.”

Ta yi nuni da cewa, batun kafa kasashe biyu ita ce hanya daya tilo ta hanyar samun zaman lafiya mai dorewa, ta hanyar kafa kasar Falasdinu tare da kasar Isra’ila, da zaman lafiya da tsaro a cikin iyakokin da kasashen duniya suka amince da su.”

Duk da ci gaba da sukar da take yi wa Isra’ila, har yanzu Australia ba ta bi sahun kawayenta na yammacin duniya kamar Canada da Faransa ba wajen bayyana aniyarsu ta amincewa da kasar Falasdinu mai ci cin gashin aknta ba. Duk da haka, ta jaddada cewa “za ta yanke shawara a lokacin da ya dace.”

Kalaman na Wang sun zo ne a matsayin mayar da martani ga wata hira da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi da gidan talabijin na Fox News, inda ya bayyana aniyar Isra’ila na kakaba takunkumin soji a daukacin zirin Gaza. Ya ce, “Tel Aviv na son mika wa dakarun Larabawa yankin gabar tekun don tafiyar da shi,” ba tare da fayyace tsari ko kuma  kasashen da za su shiga cikin shirin ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliyar Kasar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba August 7, 2025 Manjo Janar Mousawi: Martanin Iran Nan Gaba Zai Kasance Mafi Muni Kan Makiya   August 7, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Tunkarar Duk Wata Barazana August 7, 2025 Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Guterres: Dole Ne Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Gaggauta Janye Shirinta Kan Gaza
  • Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza
  • Xi Jinping Ya Zanta Da Putin Ta Wayar Tarho
  • Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu
  • Australia ta gargadi Isra’ila game yunkurin mamaye birnin Gaza
  • Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin
  • Hizbullah Da Amal Na Kasar Lebanon sun Yi Tir Da gwamnatin Kasar Saboda Bukatar Kwance Damarar Hizbullah
  • Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
  • A gaggauta sakin Sowore — Atiku
  • Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji