Hamas Ta Fadawa Iyalan Yahudawan Da Take Tsare Dasu A Gaza Kan Cewa ‘Ya’yansu Zasu Koma A Cikin Akwatunan Gawaki
Published: 16th, April 2025 GMT
Reshen soja na kungiyar Hamas wato rundunar Izzuddin Qassam, ya gargadi iyalan fursinonin yahudawan Sahyoniyya wadanda take tsare da su a Gaza kan cewa yayansu zasu koma hannunsu gawaki, saboda irin yadda HKI take kara yawaita Jefa boma-boman a kan Falasdinawa a Gaza.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani mai magana da yawan dakarun yana fadar haka a wani fai-fai bidiyo da rundunar ta watsa a yanar gizo a jiya talata.
Dakarun suna kira ga iyalan yahudawan da su yi shirin karban gawakin yayansu a cikin akwatunan gawaki, wannan kuma saboda yadda jiragen yakin HKI suke kai hare-hare babu kakkautawa kan gaza ba tare da bambanta tsakanin yara da mata da sauransu ba.
Sakon Bidiyon yana cewa (Ya ku iyalan fursinonin ku yi shirin karban gawakin yan uwanku cikin akwatunan gawaki, tare da ganin yadda naman jikinsu a tarwatse, saboda gwamnatinku ta yanke shawarar kashe su a Gaza, don haka ku jira ku gani’.
Wannan sanarwan tana zuwa ne bayan da kungiyar ta bada sanarwan cewa ta kasa samun labarin bangaren dakarun kungiyar wadanda suke kula fursinoni don sanin halin da suke ciki, don mai yuwa an halaksu.
Daga cikin fursinonin da dakarun suka rasa inda yake dai, shi ne Edan Alexander bayahude kuma ba’amerike.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar Turkiyya Ta Dakatar Da ‘Yan Wasa 1024 Saboda Laifin Caca
Kamar ‘yan wasa da masu horarwa, an hana jami’an wasa shiga ayyukan yin caca bisa ga ka’idojin TFF, da kuma na FIFA da hukumar gudanarwa ta Turai (Uefa), masu gabatar da kara na Turkiyya sun bayar da umarnin tsare mutane 21 ciki har da alkalai 17 da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa biyu a wani bangare na babban bincike kan yin caca da kuma shirya yadda sakamakon wasa zai iya fitowa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA