Kungiyar Malaman Musulunci Ta Duniya Ta Yi Fatawar Wajabcin Taimakawa Falasdinawa
Published: 5th, April 2025 GMT
A wata sanarwa da kungiyar ta malaman addinin musulunci ta duniya ta ce wajibi ne akan kowane musulmi wanda yake da iko a fadin duniyar musulunci da ya taimakawa mutanen Gaza da makamai da kayan yaki domin dakile ta’addancin Isra’ila da yake cigaba.
A jiya Juma’a ne kungiyar malaman addinin musuluncin ta duniya ta fitar da wannan fatawa wacce ta kunshi yin kira ga daidaikun musulmi da kuma gwamnatocinsu da su bai wa kungiyoyin gwgawarmaya makamai da kayan yaki da kuma bayanai na sirri akan abokan gaba.
An gina fatawar ne akan cewa matakin farko na wajabcin jihadin akan al’ummar Falasdinu, sannan kasashen dake makwabtaka da Falasdinu da su ka hada Masar, Jordan da kuma Lebanon, sannan kuma dukkanin kasashen larabawa da musulmi.
Har ila yau Fatawar ta yi kira ga musulmin da su yunkura cikin hanzari ba tare da ba ta lokaci ba ta fuskokin soja, tattalin arziki da kuma siyasa.
Sanarwar ta kuma ce, bayan kashe mutane fiye da 50,000 babu makawa a dakatar da wannan kisan kiyashi da kuma barna mai girma da take faruwa.
Kungiyar malaman musulmin duniya ta kuma kira yi kasashen musulmi da suke da alaka da Isra’ila da su yanke ta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya
Birtaniya ta sanar da cewa muddin Isra’ila ba ta biyayya wa wasu sharuɗa ba, to kuwa a watan Satumba mai zuwa za ta amince da Falasɗinu a matsayin halastacciyar ƙasa a yayin taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).
Firaiministan Birtaniya Keir Starmer ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya gudanar a yau Talata.
Starmer ya ce za su amince da ‘yancin Falasɗinu idan har Isra’ila ba ta ɗauki hanyar kawo ƙarshen halin da ake ciki a Gaza ba, ciki har da tsagaita wuta da kuma tsarin samar da zaman lafiya na din-din-din.
Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗayaA cewarsa, hakan zai tabbata “har sai idan Isra’ila ta ɗauki matakai na kawo karshen abin da ke faruwa a Gaza, ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ta kuma tabbatar da cewa ba za a ƙwace Gaɓar Yamma ba, har ma da cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta tsawon lokaci da za ta haifar da mafitar ƙasashe biyu.”
Firaministan ya ƙara nanata cewa babu wani bambanci tsakanin Isra’ila da Hamas kuma buƙatar da Birtaniya take da su kan Hamas suna nan — cewa dole su saki dukkan waɗanda suke garkuwa da su, su saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, su kuma amince cewa ba za su saka baki a gwamnatin Gaza ba sannan su ajiye makamai.
Starmer ya ce za su ci gaba da duba lamarin da ke faruwa a Gaza gabanin taron babban zauren MDD da za a yi don ganin yadda ɓangarorin biyu suka ɗauki matakai na samar da zaman lafiya kafin ta ɗauki mataki na karshe.
Matakin da Birtaniyar ke shirin dauka na zuwa ne biyo bayan matsin lamba da Starmer ke sha a cikin ƙasar, inda ‘yan majalisu sama da 200 a makon da ya wuce, suka buƙaci ya aminta da ‘yancin Falasɗinu.
Baya ga haka kuma, ɗaruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a titunan birnin Landan, suna mai kira ga Starmer ya amince da buƙatarsu na a samar da ƙasar Falasɗinu.
Ƙasashe da dama, kusan 139 sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa a hukumance, kuma a makon da ya wuce Faransa ta ce za ta yi shelar hakan yayin taron na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana yanzu haka.
Rikicin Gabas ta Tsakiya na ƙara ƙamari, inda al’ummar Gaza ke mutuwa a kullum , yayin da suke fuskantar matsananciyar yunwa, abinda wasu ke ganin samar da ƙasar Falasɗinu ne na mafita domin kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya.
A halin yanzu ƙasashen duniya sama da 100 ne ke tattauna makomar Falasdinu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa matsalar yunwa mafi muni a duniya na shirin faruwa a Gaza, saboda yadda mutane ke mutuwa wasu ke galabaita a dalilin rashin abinci.