Hizbullah Ta Yi Allawadai Da Keta Hurumin Masallacin Kudus Da ‘Yan Sahayoniya Su Ka Yi
Published: 16th, April 2025 GMT
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta fitar da bayani da ya kunshi yin Allawadai da keta hurumin masallacin kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a cikin kwanaki uku a jere.
“Yan sahayoniyar dai sun rika shiga cikin harabar masallacin na Kudus, suna yin ibadunsu na yahudanci, tare da kariyar ‘yan sandan HKI.
Kungiyar ta Hizbullah ta kuma ce; Abinda ‘yan sahayoniyar suke yi nuna kiyayya ne, da keta hurumin masallacin kudus.
Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa; Abinda ;yan sahayoniyar suke yi, ya isa bakantawa musulmi al’ummunsu da gwmanatocinsu, ya kuma sa su yunkurawa domin hana ci gaba da abinda yake faruwa.
Hizbullah ta kuma ce; Al’ummarmu ta larabawa da musulmi tana da cikakkiyar masaniya akan bukatar a daga murya da karfi da kuma yin dukkanin abinda ya kamata domin fuskantar wannan keta hurumin, saboda yin shiru yana kara karfafa abokan gaba akan abinda suke yi a cikin Kudus, yammacin kogin Jordan, Syria da kuma Yemen.
Bayanin na kungiyar Hizbullah ya kuma yi kira ga kungiyoyin kasashen musulmi da na larabawa da kuma cibiyoyin addini da malamai ma ‘yantattu a duk duniya da su yunkura da sauri, su kuma dauki nauyin da ya rataya a wuyansu na tarihi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Wani Matashi A Jihar Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
An samu mummunan rikici tsakanin mambobin ƙungiyoyin asiri wanda ya shafi tsofaffin daliban kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara da ke Ilorin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa dalibin mai suna Oyelade Olawale wanda ya karanci aikin Injiniya a fannin Gine-gine, ya rasu ne a yayin wannan rikici na kungiyoyin asiri.
An samu labarin cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a tarzomar da ta faru a Kwalejin.
A cikin wata sanarwa, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Kwalejin, Halima Garba, ta tabbatar da mutuwar matashin da kuma kama wasu mutane da ake zargi da hannu a rikicin.
Sanarwar ta yi kira ga dalibai da al’umma su rika kai rahoton duk wani abin da suke zargin zai iya haddasa fitina ga hukumomin da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a makarantar.