2025-09-17@23:11:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6136
«manyan motocin»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Tarihi ya yi mana gargadi da cewa, makomar dan adam tana hade da juna, kuma kowace kasa, da kowace kabila dole ne su daidaita da juna, su zauna lafiya, su taimaki juna, domin ta haka ne kawai za a iya kiyaye tsaro na gama gari, da kawar da tushen yaki, da tabbatar da tarihi bai maimaita kansa ba! A jawabin nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, al’ummar kasar Sin babbar al’umma ce mai dogaro da kanta, wadda ba ta jin tsoron masu nuna karfin tuwo. A lokutan baya, an sha fama da gwagwarmaya tsakanin adalci da mugunta, tsakanin haske da duhu, tsakanin ci gaba da koma baya, kuma jama’ar kasar Sin sun hada kai sun tashi tsaye wajen yaki da...
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar Habasha, domin gina daya daga cikin manyan masana’antun takin zamani a duniya a garin Gode. An rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin rukunin Dangote da kamfanin zuba jari na Habasha (EIH), wanda zai baiwa rukunin Dangote damar rike hannun jarin kashi 60 cikin dari, yayin da EIH zai rike kashi 40 cikin dari. Ana has ashen cewa idan an kammala aikin, zai kasance cikin manyan masana’antun samar da takin zamani guda biyar na duniya, wanda zai rika samar da takin zamani ton miliyan uku a kowace shekara. A cewar EIH, za a kammala aikin a cikin...
Jami’an Iran sun yaba matuka da irin nasarorin da aka samu a yayin halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian a taron kungiyar Shanghai (SCO) a kasar China. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran ta yi amfani da tsarin diflomasiyya a bangarori daban-daban a yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekara-shekara a kasar Sin. Gharibabadi ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon shafin Twitter a jiya Talata, inda ya yi bayani kan abubuwan da suka shafi taron, wanda shugaba Masoud Pezeshkian, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin ya aiwatar da su. A cewar jami’in diflomasiyyar, halartar babban jami’in gudanarwa na kasar Iran a taron ya...
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar rayukan da za su kai sama da miliyan 100, wadanda daga cikinsu sojoji da fararen hula miliyan 35 ne Sin ta yi asara. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan mummunar akida ta mulkin danniya, yayin da ta shiga cikin sahun sojojin sauran kasashe a yakin duniya na biyu. Kafada da kafada suka yi gumurzu wajen murkushe maharan kasashen Japan, Jamus da...
Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya suka samu a yakin duniya na biyu. Bugu da kari, Guterres ya jaddada ta hanyar nuna batutuwan tarihi cewa, babbar mamayar da Japan ta yi wa Sin ita ce farkon yakin duniya na biyu na gaskiya. Guterres ya yi imanin cewa, tsayin daka da kasar Sin ta yi wajen yin tir da hare-haren Japan, ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru da dama, tare...
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku. ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027. A ’yan kwanakin nan ne aka...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce alakar Sin da Rasha ta zama misali na kyakkyawar dangantaka tsakanin manyan kasashe, wadda ke kunshe da ingantaccen yanayin kawance na makwafta, da cikakken salon tafiya tare bisa manyan tsare-tsare, da hadin gwiwar cimma moriyar juna. Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin zantawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Beijing. A nasa tsokacin kuwa, shugaba Putin ya ce shawarar da shugaba Xi ya gabatar game da tsarin shugabancin duniya ta zo a lokacin da ake matukar bukatarta, kuma wajibi ne a yi aiki da ita, kana za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance gibin dake akwai a tsarin shugabancin duniya. Ya ce a nata bangare, Rasha a...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hakimin Bagaji Odo a Karamar Hukumar Omala ta Jihar Kogi, David Wada. Rahotanni sun ce basaraken ya faɗa tarkon ’yan bindigar ne a ƙauyen Ojuwo Ugweche da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, yayin da yake dawowa daga taron sarakunan gargajiya a Abejukolo, hedikwatar ƙaramar hukumar. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Wani mazaunin yankin, Maji Ahiaba, ya bayyana cewa a ’yan kwanakin nan ƙauyen Ojuwo Ugweche na fuskantar hare-haren masu ta’adar garkuwa da mutane, duk da cewa a baya an taɓa tura jami’an tsaro da ’yan sa-kai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata. Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da kuma jagorancin cike gibin kudi na samar da ci gaba da bunkasa. Sabuwar ajandar mulkin duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta yi magana kai tsaye kan wasu muhimman abubuwa guda uku a tsarin jagorancin duniya, wato rashin daidaiton iko, da rarrabuwar ra’ayoyi, da kuma rashin daukar matakai. Ajandar, wadda ta fitar da wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar wa auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24 Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya karu zuwa shahidai 63,633, tare da jikkatan wasu 160,914. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar alkalumman baya-bayan nan da ma’aikatar ta...
Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya. A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce za a karrama Sarkin tare da wasu fitattun ’yan Najeriya guda shida a babban taron shekara-shekara da cibiyar ke shiryawa. Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025, a Cibiyar Karatun Alƙur’ani...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci Golan zai riƙa amfani da riga mai lamba 99 domin ranar haihuwarsa ta 1999, kamar yadda ƙungiyar ta sanar. A jawabin da ya yi dangane da komawa ƙungiyar, Donnarumma ya ce yana cike da farin ciki da jin daɗi. “Na koma ƙungiya da ke cike da zaratan ’yan wasa, sannan kuma ƙungiya...
Hukumar NDLEA a Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na ɗauke da ƙwayoyi, tare da tabar wiwi guda 48. An cafke wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, bayan an gano kayan a cikin tirela ɗauke da kekuna a kan hanyar Zariya zuwa Kano a Gadar Tamburawa. ’Yansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Katsina, Sun Ƙwato Makamai ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Daba 107 A Kano, Sun Ƙwato Makamai Da Ƙwayoyi NDLEA ta ce tana tsare da wanda ake zargin da kuma kayayyakin, yayin da ake ci gaba da bincike. Hukumar ta buƙaci jama’a su riƙa sanar da ita duk wani abin da suka zarga na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi. Daga kanmu, magana ta...
Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako. A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da suke aiki a gonakinsu. Haka zalika, a yankin Mussa da ke Askira/Uba, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen a ranar asabar da daddare, inda suka kashe matasa uku, kafin su ƙona wasu gidaje da shaguna da ƙauyen. Waɗannan munanan hare-haren sun jefa al’ummomin cikin zaman makoki wanda ya ƙara nuna damuwa kan rashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin. Sai dai kuma Sanata Ndume...
Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Abdulwahid Muhammad Nour na kungiyar ‘The Sudan Libration Movementa’ Wato (SLM) wacce take iko da yankin yana fadar haka. Ya kuma kare da cewa, zaizeyar kasa ta aukune bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin. Ya kuma kammala da cewa mutum guda ne kacal ya tsira da ransa a garin Marra dake kan tsaunin. Kungiyar ta bukaci taimakon MDD da kuma sauran kungiyoyin Agaji a duniya don fidda gawakin mutanen da zaizayar kassar ta bisne a kan tsaurin. Kasar Sudan dai tana cikin yaki fiye da shekaru...
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), ta yi kira ga Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) da ta ƙara mayar da hankali wajen yada labarai kan wasannin gargajiya, irin su langa da kokawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe wanda shi ne shugaban ALGON reshen Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin SWAN na jihar suka kai masa ziyarar ban girma, inda suka nemi goyon bayansa kan babban taron bita da ƙungiyar ke shirin gudanarwa. A cewarsa, ƙara bayar da muhimmanci ga wasannin gargajiya zai taimaka wajen jan hankalin matasa zuwa harkokin ci-gaban rayuwa, tare da rage yawan fadawa cikin laifuka da shan miyagun ƙwayoyi. Ya kuma shawarci SWAN da ta ƙulla alaƙa...
’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai a jami’ar mai suna Jon Reider, ya musanta iƙirarin na Kemi Badenoch, wadda ta yi kaurin suna wajen sukar ƙasarta ta haihuwa. Kemi Badenoch ta yi iƙirari cewa ta samu gurbin ƙaramin tallafin kuɗi daga Jami’ar Stanford, amma rashin kuɗin iyayenta ya hana ta amfani da damar. Sai dai Jon Reider, wanda a lokacin yake kula da ɗalibai daga ƙasashen waje da tallafin karatu a Stanford,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sau da dama ibti’lai kan faru da wasu mutane wanda ya kamata ace sun bi hanyoyi don a biya su diyya. Sai dai masana na bayyana cewa sau da dama mutane basu san honyoyin da ya kamata subi don neman hakkokin su ba. NAJERIYA A YAU: Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da mutane zasu bi don neman diyya idan an zalunce su. Domin sauke shirin, latsa nan
An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta. Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen a jiya, inda aka gabatar da jawabai daban-daban, da ke kara tabbatar da aniyar al’ummar kasar Yemen wajen ci gaba da bin tafarkin wadanda suka yi shahada, domin mara baya ga al’ummar Gaza mara kariya. A nasa bangaren Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan wannan hari na wuce gona da...
shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na nukiliya a gabar tekun Venezuela. Inda Ya kira wannan matakin da cewa shi ne mafi muni da Amurka ta dauka a tsawon shkaru a yankin Caribbean. Maduro ya zargi Washington da aiwatar da manufar matsin lamba ta soja a kan Caracas, wanda ya tilasta wa Venezuela ayyana cikakken shirin tsaron kasa. “Venezuela kasa ce mai zaman lafiya, amma al’ummarta mayaka ne kuma ba za su...
A lokacin wani taro da ya gudana tsakanin shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio gutteres a kasar china ya bayyana cewa iran tana da hakkin ta mallaki fasahar nukiliya na zaman lafiya, kana ya nuna damawarsa game da batun takunkumi da kasashen turai ke son sake kakabawa iran, Wannan bayanin na Gutteres ya kara fito da matsayin iran a mataki na kasa da kasa na hakkin mallakar fasahar nukiliya domin ayyukan zaman lafiya, a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tankiya tsakanin iran da kuma kasashin turai game da shirin ta na nukiliya da kuma yunkurin sanya mata takunkumai, A nasa bangaren shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya bayyana cewa...
Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari. Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa, Kodayake babu asarar rai. Bayan dawowar tsohon ministan a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gida ya yi zargin siyasa ce ta a da aka kai masa harin, yana mai jaddada cewa, harkar siyasarsa babu gudu babu ja da baya. “Shari’a ta tanadi ka kare kai, in aka kawo maka hari amma kai kar ka kai wa kowa hari, maganar siyasa ba gudu ba ja...
Kazalika, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin hada karfi da karfe wajen kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu, da samar da karin alfanu ga daukacin bil’adama ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ba da tabbacin cewa, Majalisar za ta kara sanya ido domin tabbatar da gaskiya da rikon amana ga yadda ake sarrafa kudaden jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a matsayin muhimmin ginshiki na tsarin kasa da kasa, dole ne ta dauki matakai na zahiri, na musamman, da kuma a bayyane kan hanyoyi guda biyu masu kamanceceniya da juna, don samar da duniya mai zaman lafiya, da duniya mai shirin fadada hadin gwiwar tattalin arziki. A yayin taron kolin shugabannin kungiyar hadin gwiwar Shaghai “SCO” karo na 25 a birnin Tianjin na kasar China, shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, a cikin tsarin karfafa hadin...
Shawarar da Iran ta gabatar ga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai zai durkusar da darajar kudin dalar Amurka A jawabin da ya yi a wajen taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a kasar China, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ba da shawarar kafa tsarin hada-hadar kudi ga kungiyar da rage dogaro da kudin dala. A rana ta biyu ta taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 25, wanda aka shirya a birnin Tianjin na kasar China, tare da halartar shugabannin kasashe fiye da 20, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, da inganta hadin gwiwar hada-hadar kudi, domin dakile illar da takunkumin da ake kakaba wa kasashe na bangare guda zai haifar....
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya kamata wajen tsara manyan tsare-tsare. Guterres ya ce, akwai misalai da dama da suke iya tabbatar da haka. Alal misali, shugaba Xi ya taba sanar da burin gina na’urorin samar da wutar lantarki bisa makamashin da ake iya sabuntawa, wadanda karfinsu ya zarce kilowatt biliyan 1.2 zuwa shekarar 2030 a kasar Sin, wanda aka riga aka cimma shi. Kazalika, ya yi alkawarin cimma nasarar kaiwa...
A cewar sa, yankin Arewa-maso-yamma ya samu kaso mafi girma na ayyuka da ya kai naira tiriliyan 5.97, Kudu-maso-kudu ya samu naira tiriliyan 2.41, Arewa-ta-tsakiya naira tiriliyan 1.13, Kudu-maso-gabas naira biliyan 407, Arewa-maso-gabas naira biliyan 400, yayin da Kudu-maso-yamma (ban da Legas) ya samu naira biliyan 604. Idris ya ce dukkan waɗannan yankuna suna amfana da manyan hanyoyi, layukan dogo da kuma hukumomin raya yankuna. Ministan ya ce daga cikin muhimman ayyukan da ake aiwatarwa akwai Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, da Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri, da gyaran layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri, da kuma Hanyar Gadar Neja ta 2. Haka kuma, gwamnati ta samar da fiye da naira biliyan 250 don ayyukan...
Yayin da yake zantawa da ’yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Pakistan Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa, Xi Jinping shugaban kasa ne mai matukar hangen nesa. A cewar firaministan, Xi Jinping, shugaban kasa ne wanda ke mayar da hankali sosai kan kyautata rayuwar jama’a, kuma a karkashin jagorancinsa, kasar Sin ta samu nasarar yaki da matsanancin talauci, al’amarin da ke bukatar matukar hangen nesa da babbar hikima. Kazalika, shugaba Xi yana amincewa da ra’ayin cudanyar sassan kasa da kasa. Firaminista Shehbaz ya kara da cewa, ba sauya yanayin tattalin arzikin kasar Sin kawai shugaba Xi ya yi ba, har ma ya mayar da kasar zuwa matsayi na biyu a karfin tattalin...
Wata kotu a ƙasar Finland ta yanke wa ɗan Najeriya mai rajin ɓallewar ƙasar Biyafara, Simon Ekpa, hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari bisa laifukan da suka shafi ta’addanci, zamba da karya doka. Kotun ta tabbatar da cewa Ekpa ya aikata laifuka da suka haɗa da ƙoƙarin hargitsa jama’a da nufin ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyoyin masu ɗaukar makami. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Gwamnan Neja ya rushe kwamishinoninsa Haka kuma, kotun ta ce an same shi da laifin zamba ta haraji da keta wasu dokokin Finland. A cewar kotun, daga watan Agusta 2021 zuwa Nuwamba 2024, Ekpa ya yi amfani da kafafen sada zumunta wajen yaɗa shirye-shiryen neman ɓallewar Biyafara...
Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa. Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan. Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a jihar tare da yi musu fatan alheri. Sai dai kuma gwamnan ya sake nada sakataren gwamnatin da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da mataimakinsa a da wasu jami’ai a kan muƙamansu
Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace. El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ta ƙara ƙamari, duk da cewa gwamnati ta yi ƙoƙarin rage yadda ake rahoto a kafafen watsa labarai. “Har yanzu ina kan bakata cewa waɗannan ’yan bindiga a halaka su baki ɗaya, ba a rika lallashi ko yin sulhu da masu ta’addanci ba. Wannan bai taba aiki a ko’ina ba,” in ji shi a yayin tattaunawar. Martanin ONSA A martanin da aka fitar da...
’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Neja. A yayin zanga-zangar a ranar Lahadi, wani daga ƙauyen Rinaye ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro gare mu a ɗauki matakin korar mana ’yan bindigar su bar yankinmu. “Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace...
Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala sanarwar a hukumance da misalin ƙarfe 7 na yamma. Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi A farkon tattaunawar, Newcastle ta dage cewa sai Liverpool ta biya fam miliyan 130 kafin ta sayar da ɗan wasan, amma daga bisani...
Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba. Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.” Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa...
Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya. Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa? NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Amsar wannan tambaya shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi yunkurin bicikowa. Domin sauke shirin, latsa nan
Allah Ya yi wa Shugabar Ma’aikata ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, Misis Grace Adayilo, rasuwa a safiyar Litinin ɗin nan. Shaidu sun tabbatar wa wakilinmu cewa ta rasu ne ’yan sa’o’i kaɗan da suka gabata. Kodayake kawo yanzu ba a sanar da rasuwar a hukumance ba. Misis Grace Adayilo ita ce mace ta farko kuma ’yar asalin yankin Babban Birnin Tarayya ta farko da ta riƙe wannan muƙami. ta kasance tsohuwar Sakatariyar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Birnin Abuja (AMAC), kafin Minista Nyesom Wike, ya naɗa ta Shugabar Ma’aikata. Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata a biya ’yan Arewa diyya Gargaɗi kan zagin Sahabban Annabi Muhammad (SAW) Ita ce ta wakilci Wike a babban taron Majalisar Taro ta Ƙungiyar G-7 da...
Ƙungiyar Arewa ta ’Yan Jarida (ABMPF) ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara, tana mai cewa matakin ya jawo asarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce rusau ɗin ya haddasa wa ’yan kasuwar asarar kimanin Naira biliyan 20, tare da ruguza shaguna da wuraren ibada fiye da 40, abin da ya ce “bai dace ba kuma yana iya jawo rikicin ƙabilanci.” Kungiyar ta roƙi gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da sarakuna na gargajiya su shiga wajen tabbatar da kare haƙƙin ’yan Arewa da suke zaune a Legas. Haka kuma ta yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya...
Ya kuma tuna da tsohon abokin ajinsu wanda ya kasance tsohon Sufeton ƴansanda, marigayi Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. El-Rufai ya bayyana shi a matsayin mutum nagari, yana mai cewa tsarin ƴansanda na yanzu ya sha bamban da lokacin da Arase ya jagoranta. Daga ƙarshe, ya ce zai sake rubuta ƙorafi ga IGP da kuma hukumar kula da ƴansanda (PSC), yana mai gargadi cewa idan jami’an tsaro suka zama kariya ga masu tada fitina, to hakan zai kai ƙasa ga rugujewa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya a kan akasar. A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin...
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi na kai hari kan ministoci da ma’aikatan farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba. Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan shahidai, abokan aikinsu, da al’ummar kasar Yemen, ya tabbatar da cewa wuce gona da...
Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki a Gombe Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba. Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a. Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja...

Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO
Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori. Kafin liyafar maraba, Shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun yi maraba da shugabannin kasashen waje da matansu cikin fara’a, inda suka mika musu hannu tare da gaisawa, kuma suka dauki hotuna tare da su.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ruhi mai karfi da aka samu a lokacin yakin turjiyar ya kasance wani muhimmin ginshiki mai karfi, wanda ya jagoranci jama’ar kasar Sin zuwa shawo kan wahalhalu da cikas a yunkurinsu na farfado da kasa, kamar yadda makalar ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kilishiyar Waja, Hajiya Rabee Abubakar Kulani, ta kai ziyara gidan gyaran hali na Gombe, inda ta raba mata fursunoni kayan tsaftar jiki domin su kula da kansu a lokacin al’ada. Ta ce ta kai wannan gudummawa ne domin tallafa wa mata fursunoni wajen kare mutuncinsu, ganin cewa sau da yawa ba su da damar samun irin waɗannan muhimman kayayyaki. Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Zaɓen Ribas: APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 20, PDP ta samu 3 “Ina so su ji kamar sauran mata, su samu tsafta da mutunci duk da yanayin da suke ciki. “Shi ya sa na sayi kayayyakin da kaina domin na tallafa musu,” in ji ta. A yayin ziyarar,...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Muhimmancin Aiwatar Da Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya wallafa wani bangare na jawabinsa cikin harshen chinanci kan muhimmancin dangantakar Iran da China. Kididdigar ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci ya wallafa bayanansa kan kasar Iran da kuma damar da kasar China ke da ita ta taka rawa a fagen duniya da kuma wajibcin aiwatar da yarjejeniyar tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, wanda ya zo daidai da ziyarar...
Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya tabbatar da cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Iran. Duk da tsare-tsare masu yawa da kuma sanar da manufofinsu a baya, makiya sun kasa cimma wata manufa da suka ayyana a cikin yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan Iran, lamarin da ya tilasta musu amincewa da shan kashi ta hanyar amincewa da tsagaita bude wuta cikin hanzari. Fadavi ya kara da...

Gwamnatin Kenya Ta Ci Gaba Da Tono Gawarwakin Da Masu Tsaurin Addinin Kirista Da Suka Kashe Kansu A Kenya
Kenya ta tono gawarwakin mutane 32 a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mace-macen ‘yan darikar addini masu tsattsauran ra’ayi Hukumomin kasar Kenya sun tono gawarwaki 32 a makon da ya gabata a kudu maso gabashin kasar, wani sabon bala’i da ya sake haifar da sukar gwamnatin kasar, wadda a baya ta yi alkawarin murkushe kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi bayan mutuwar daruruwan mabiya kungiyar asiri ta “Apocalypse” shekaru biyu da suka gabata. Gwamnatin Kenya da mazauna yankin sun danganta gawarwakin da aka gano a kauyen Kwa Binzaro da wata kungiyar kiristoci da ake zargi da hannu wajen kashe mutane fiye da 400 a dajin Chakahola da ke kusa a shekarar 2023. Babban likitan gwamnati a...
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa za ta riƙa bai wa kowane masallacin Juma’a a jihar kuɗi daga Naira 300,000 zuwa 500,000 duk wata domin tallafa musu. Haka kuma gwamnatin za ta riƙa biyan limaman masallatan, na’ibansu da ladanai alawus na kowane wata domin sauƙaƙa wa hidimominsu. Zaɓen Ribas: APC ta yi nasara a ƙananan hukumomi 20, PDP ta samu 3 Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno Mai magana da yawun gwamnatin, Abubakar Bawa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce manufar shirin shi ne ƙarfafa karatun Alƙur’ani da koyar da ilimin addini ga yara da matasa a jihar. Gwamna Ahmed Aliyu, ya sanar da wannan mataki ne a ranar Asabar yayin...
Yu ya ce, kasar Sin ta tafka asarar rayukan sojoji da fararen hula sama da miliyan 35 da kuma asarar tattalin arzikin da ya zarce dalar Amurka biliyan 600 a lokacin yakin duniya na biyu. Ya yi nuni da cewa, tsayin dakan da kasar Sin ta yi ya yi mummunar wargaza mulkin danniya, tare da ba da gudummawa mai tarihi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.” (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) tare da Civilian JTF, sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 12 a Jihar Borno. A ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta, sojojin sun kai farmaki ƙauyukan Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da Loskori Kura, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan. Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja A Loskori Kura, sojojin sun yi nasara, inda suka kashe ’yan ta’adda 12, suka kuma kwato8 bindiga ƙirar AK-47 guda shida, harsasai guda takwas da magunguna iri-iri. Majiyoyin tsaro sun ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun ji raunuka, bayan artabun da suka yi da sojojin. Wannan farmaki ya...
135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin...
A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
137- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin gama gari tsakanin sojojin Imam Ali (a) da...
Tsohon Sufeto-Janar na rundunar ’yan sandan Nijeriya, Solomon Arase ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, babban birnin kasar. Rahotanni sun ce tsohon IG din ya rasu ne a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja a safiyar Lahadin nan. An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja Chelsea ta kammala ɗaukar Garnacho daga Manchester United Kawo yanzu dai iyalai ko rundunar ’yan sandan kasar ba su fitar da rahoton rasuwar a hukumance ba, sai dai wani hadiminsa da Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da hakan. Arase wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada a Afrilun 2015 shi ne Sufeto Janar na 18 a tarihin Nijeriya. Kazalika, bayan ritayarsa a shekarar 2016, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari...
Tsohon Sufeto-Janar na rundunar ’yan sandan Nijeriya, Solomon Arase ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, babban birnin kasar. Rahotanni sun ce tsohon IG din ya rasu ne a Asibitin Cedarcrest da ke Abuja a safiyar Lahadin nan. An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja Chelsea ta kammala ɗaukar Garnacho daga Manchester United Kawo yanzu dai iyalai ko rundunar ’yan sandan kasar ba su fitar da rahoton rasuwar a hukumance ba, sai dai wani hadiminsa da Aminiya ta tuntuba ya tabbatar da hakan. Arase wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada a Afrilun 2015 shi ne Sufeto Janar na 18 a tarihin Nijeriya. Kazalika, bayan ritayarsa a shekarar 2016, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari...
Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu. Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin taimakon kasashen da makamai da horo. Amma ganin yadda har yanzu kasashen ke ci gaba da fuskantar hare-hare, shin za a iya cewa alaka da Rasha ta yi musu rana? Sababbin kawayen Moscow Tun a 2021 Rasha ke tura dubban sojoji da makaman da suka kai miliyoyin Dala zuwa Mali da Burkina Faso da Nijar. Tana haka ne domin taimakon kasashen wajen yaki...
Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta dauki danwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu. Bayan da cinikin Eze ya fada, yanzu kuma kungiyar ta Arsenal ta sake mayar da hankalinta wajen sayan dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafa ta Bayer Liberkusen, wato Piero Hincapie. Chelsea Da alama har yanzu mai horarwa Enzo Maresca bai hakura da karin cefane ba kafin rufe kasuwar, yayin da yake neman Alejandro Garnacho na Man United da danwasan RB Leipzig Dabi Simons. Sai dai komai zai dogara ne da yawan ‘yanwasan da ta iya sayarwa kamar Nicolas Jackson da Christopher Nkunku da Tyrikue George, wadanda...
Hakan yana faruwa ne saboda yawan hormones “progesterone” da yake taruwa a jikinta. A wannan gaban ana kiran yanayin da “luteal phase”. Shin wasu lokuta ne za ki tsammaci ganin farin ruwa a gabanki; Idan kin gani ba damuwa bane Yawanci mata suna iya samun bushewar gaba kamar na kwana 3 zuwa 4 kowane bayan yankewar al’adarsu. bayan wannan kwanakin, farin ruwa mai danko ya kan sake bullowa wanda zai yi kamar kwana 4 zuwa 5 kafin lokacin fitar kwayar alitta, alama ce ta kwayar alitta sun fara girma, ana kiransa da “follicular phase” that means a lokacin ne “eggs” (for obulation) suke kokarin girma. Idan kuma lokacin fitar ya yi, ruwan sai ya canza daga mai danko zuwa fari...
Lauyoyin kare hakkin bil’adama a Argentina sun shigar da kara a gaban kotunan tarayya suna neman a kama firayim ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu idan ya saka kafarsa a kasar, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna yiwuwar cewa zai kai ziyara a kasar a wata mai zuwa. Karar da lauyoyin kasar Argentina masu rajin kare hakkin bil adama suka shigar, na zargin Netanyahu da alhakin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama da ke da alaka da hare-haren sojin Isra’ila a Gaza. Har ila yau, a cikin karar an bukaci a gudanar da bincike kan shugabannin siyasa da na soji na Isra’ila kan wani lamari da ya faru a ranar 23 ga Maris, inda aka kashe mutane 15, ciki har da...
Shugaban mayakan RSF a Sudan Mohammed Hamdan Dagalo ya yi rantsuwar shugabatar gwamnati mai kishintar gwamnatin kasar. Sanarwar ta ce Dagalo, wanda aka fi sani da Hemedti, wanda kuma ba kasafai ake ganinsa a kasar Sudan ba tun bayan barkewar rikici na tsawon watanni 28 tsakaninsa da sojojin kasar, an rantsar da shi ne a yayin wani biki a birnin Nyala na kasar Sudan, ko da yake kamfanin dillancin labaran Reuters ya kasa tabbatar da inda yake. Nyala, daya daga cikin manyan biranen kasar Sudan dake yankin Darfur, wanda kuma shi ne babbar tungar mayakan kungiyar RSF, kungiyar da ta nada nata firaminista da majalisar shugabancin karkashin jagorancin Dagalo. A ranar 16 ga watan Afrilu, Dagalo, kwamandan rundunar RSF ya...
A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, a birnin tashar ruwa na Tianjin dake arewacin kasar Sin. Yayin zantawarsu, shugaba Xi ya ce alakar Sin da Masar na cikin wani yanayi mafi kyau a tarihi, ya kuma yi kira da a yi amfani da damar bikin cika shekaru 70 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekara mai zuwa, wajen cimma nasarar gina al’ummar Sin da Masar mai makomar bai daya a sabon zamani, da kara bayar da gudummawa don wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya, da bunkasa ci gaba da walwalar sassan kasa da kasa. A dai yau din, shugaba Xi ya gana da firaministan Cambodia Hun...
Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaduwa kamar wake dan arba’in. An taba yin wani shugaban kasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin bata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk kasar da ya ratsa a Arewacin kasar domin yakin neman zabe, da harshen Hausa yake magana. Abin da nake nufi...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta raba wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Ƙaramar Hukumar Potiskum ta Jihar Yobe, kayan tallafi. Darakta Janar na hukumar, Zubaida Umar, ta amince da fara wannan tallafi a Potiskum, inda ta samu wakilcin Abdullahi Garba, ko’odinetan ofishin NEMA na Maiduguri. An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara A cewarta, wannan mataki ya biyo bayan ambaliyar ruwa da ta auku a ranar 15 ga qatan Agusta, 2025. Ambaliyar ta shafi dubban jama’a kuma ta lalata gidaje da dama. Binciken da NEMA tare da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa gidaje 2,557 ne abin ya...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce har kullum kasar Sin za ta kasance amintacciyar abokiyar huldar MDD, kuma a shirye take ta zurfafa hadin gwiwa da majalisar, da tallafa mata, ta yadda MDDr za ta taka muhimmiyar rawar jagoranci a harkokin kasa da kasa, da hada karfi da karfe wajen sauke nauyin dake wuyanta na kare yanayin zaman lafiyar duniya, da ingiza ci gaba da walwalar dukkanin sassa. Shugaba Xi, ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin da yake ganawa da babban magatakardar MDD Antonio Guterres, a birnin tashar ruwa na Tianjin. Ya ce tarihi ya nuna yadda cudanyar mabambantan sassa, da goyon baya da hadin gwiwa, suka kasance amsa ga tarin kalubalen dake addabar duniya. Mista...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin ganawarsa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin tsaron kasar Armeniya a yau Asabar, ya jaddada cewa: Dole ne su tabbatar da cewa babu wani karfin kasashen waje da zai iya wargaza dangantakar abokantaka tsakanin Iran da Armeniya. Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa, damuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin Caucasus na baya-bayan nan, musamman kasancewar dakarun kasashen waje a wannan yanki mai matukar muhimmanci, an kawar da su sosai bisa la’akari da fayyace da kuma tabbacin da jami’an kasar Armeniya suka bayar. Ya ce, “Dole ne su...
Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya. Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, ya gana tare da tattaunawa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Armeniya a safiyar yau. A cikin wannan taro, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana gamsuwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi kan matakin tattalin arziki, siyasa, tsaro da kasar Armeniya, tare da jaddada hadin gwiwa da...
Watan Mayu 1956,aka gabatar da kudurin niyyar yin doka a majalisar Kudu maso gabashin Nijeriya, suka gabatar da kudurin zai bada dama ta a amince da Sarakunan gargajiya, wanda ta haka ne aka samu damar kafa majalisar Sarakunan Kudu maso gabashin Nijeriya, duk kuwa a lokacin da akwai turjiyar da aka samu daga masu fafutukar tafiyar da lamurra yadda suka dace, saboda sun ki goyon bayan a sa su masu Sarautun gargajiya a harkokin yadda ake tafiyar da gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Kungiyar Hamas ta yi maraba da Allah wadai da kasashen Turai 6 suka yi da matakin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka kan Gaza Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi marhabin da matakin da wasu kasashen Turai shida suka dauka na yin Allah wadai da wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka yi a kan birnin Gaza, tare da la’akari da shi a matsayin wani muhimmin mataki da ke kara habaka matsayar kasashen duniya na neman kawo karshen wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu. Kasashen da ake magana a kai su ne: Iceland, Ireland, Luxembourg, Norway, Slovenia, da Spain. Ministocin harkokin wajensu sun bayyana rashin amincewarsu da hare-haren wuce gona da iri kan...
Zanga-zangar adawa da kakaba yunwa da gudanar da kisan kare dangi da sojojiin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza a biranen kasar Morocco Dubban al’ummar Moroko ne suka gudanar da zanga-zanga a garuruwa da dama na masarautar kasar a cikin jerin gwanon dare, domin neman kawo karshen yunwa da kisan kiyashin ga Falasdinawa a zirin Gaza. Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka tsananta kai hare-hare ta sama, da kasa da kuma ta ruwa a wasu unguwanni a cikin birnin Gaza, inda Falasdinawa kusan miliyan daya suke, tun da sanyin safiyar Juma’a. Wannan dai na daga cikin shirinta na mamaye birnin da kuma kammala kisan gillar da ta shafe watanni 23 tana yi wa Falasdinawa....
Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse. Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar. Jigon jam’iyyar PDP a Gombe, Haruna Jonga, ya koma APC Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike Harin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Birnin Magaji, inda ’yan bindiga suka kai wa ƙauyuka biyu hari. Mutane da dama ne suka tsere zuwa bakin kogi, inda suka riski jirgin ruwa guda ɗaya kacal. Hakan ya sa aka jirgin da mutane sosai, lamarin da ya sa ya nutse a cikin ruwa. “Babban yayana...
Ɗan wasan ɗan shekaru 22 ya zura ƙwallaye 10 ne kawai a wasanni 52 da ya buga a United bara, kuma zuwan Sesko ya ka5ra rage masa damar zama a cikin ƙungiyar. Sha’awar Napoli kan Højlund ta ƙaru ne bayan Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa wanda zai sa ya daɗe a jinya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shi yasa ta ce duk kowa daga ciki al’umma yana da irin gudunmawar da zai bada wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar da zai tafi makaranta, ta kuma kara jaddada tsarin nastressing TaRL yana bada dama ga Jihohi su samu kira da sa duk masu ruwa da tsaki. A tasu gabatarwar ta hadin gwiwa, Dakta Goni Shetima,wanda shi horarwa ne ta bangaren tsarin TaRL,da Malam Abdulrahman Ibrahim Ado, kwararre jami’in ilimi na UNICEF, sun bayyana cewa tsarin an fara gudanar da shi a karamar hukumar Alkaleri. Kamar yadda suka ce, an fara tsarin ne da makarantu 190, ‘yan makaranta 10,865, sai kuma Malaman makarantar gwamnati 290. Shi ma darektan shiyya na hukumar (UBEC), wanda Abdulsalam Abubakar ya...
Tsohon babban jami’in hukumar tsaro ta Marshall a Jihar Gombe, Alhaji Haruna Jonga, ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya koma APC. An yi bikin karɓarsa a ofishin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gombe. Dokar ta-ɓaci: Fubara zai dawo ofis ranar 18 ga Satumba — Wike A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn Shugaban ALGON na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya ce wannan sauya sheƙa na Jonga alama ce cewa jama’a suna yaba wa ayyukan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya. Shugaban APC na ƙaramar hukumar Gombe, Alhaji Abubakar Danladi, ya ce Jonga babban mutum ne da zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi, musamman kafin zaɓen 2027. Da yake jawabi, Jonga, ya bayyana cewa ayyukan raya ƙasa na...
‘Kun kuduri aniyar kiyaye manyan ka’idojin bin doka domin tabbatar da cewa kowa, har da masu mulki, suna karkashin doka kuma ana iya daukar mataki a kansu. Idan muka yi haka, to mun magance tushen matsalar mulki a wannan kasa,’ in ji shi. Sarkin Musulmi ya jaddada cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiyar al’umma, kuma dole doka kullum ta kasance mai nufin cimma adalci a matsayin babbar manufarta. Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da wannan taro wajen tattauna muhimman batutuwan da suke tsara makomar Nijeriya.” “Ya ce, ‘Ina fatan wannan taro zai ba ku damar tattauna batutuwan da suka shafi makomar al’ummarmu. Abubuwa uku ne manya: Ci gaba da kokari wajen gyaran dokoki domin a hankali...
Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati. Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar. Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi. Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar...
Yayin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da tura manyan ayyukan ci gaba zuwa Legas, tambaya a nan shi ne: shin za a ji daɗin “Renewed Hope” daidai da yadda ake ji a bakin tekun Legas a ƙauyukan Arewa maso Gabas? Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jihar Legas, mahaifar Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ta samu ayyukan gwamnati da darajarsu ta kai Naira Turkiya 3.9 a cikin shekaru biyu na gwamnatinsa. Ayyukan da gwamnatin ta ba wa Jihar Legas ya zarce jimillar abin da aka ware wa jihohin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Kudu maso Gabas baki ɗaya, waɗanda suka haɗa da jihohi 18. Rahoton binciken da wakilanmu suka gudanar ya bayyana cewa cikin shekaru biyu da suka gabata, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 3.9 a jihar Legas. A cewar rahoton, cikin lokaci guda, FEC, wadda Shugaban Ƙasar ke jagoranta, ta amince da ayyuka da darajarsu ta kai naira tiriliyan 5.97 ga Kudu maso Yamma,...
Gwamnan Jihar Taraba, Dokta Agbu Kefas, ya shirya wa Gwamnonin yankin Arewa maso Gabas inda ya shirya musu ƙasaitaccen biki da liyafar dare a Jalingo, a gabanin taron gwamnonin da za a gudanar yau Asabar. An gudanar da liyafar ne a daren Juma’a a babban ɗakin fadar gwamnati, inda aka nuna raye raye na al’adu daga kungiyoyin gargajiya na Taraba da sauran jihohin yankin. A jawabinsa, Gwamna Kefas ya bayyana cewa haɗin kan Arewa maso Gabas na da matuƙar muhimmanci wajen shawo kan matsalolin tsaro, talauci da rashin ingantattun ababen more rayuwa. Ya kafa da cewa taron gwamnonin na bayar da dama ta musamman don tsara manufofi da inganta zaman lafiya da ci gaban yankin. Editan BBC Hausa ya magantu...
Majalisar dokokin kasar Turkiyya ta yi tir da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza sannan ta amince da hana jiragen fisinja na HKI wucewa ta sararin samaniyar kasar. Banda haka ta bukaci a kore daga Majalisar dinkin duniya. Majalisar ta bukaci a kula da hakkin Falasdinawa a fagen kasashen a kuma kawo karshen yakin da ke faruwa a gaza, a ranar jumma’a ce majalisar dojojin kasar ta Turkiyya ta amince da wadannan matakan, wadanda suka dakatar da harkokin kasuwanci kwata-kwata da HKI da hana sararin samaniyar kasar ga jiragen HKI. Ya bukaci dukkan shugabannin bangariri na majalisar su sanyawa dokar hannu don ya samu matsayin gwamnatin da mutanen turkiyya gaba daya. Kudurin ya bukaci a kafa kasar Falasdinu...
Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, ya ce zargin cin zarafi a wurin aiki da ake yi masa ba su da tushe. Lamarin ya samo asali ne bayan wata tsohuwar ma’aikaciyar BBC Hausa, Halima Umar Saleh, a yayin wata tattaunawa da tashar Arewa24 ta bayyana cewa ta fuskanci musgunawa a lokacin aikin ta, kodayake ba ta ambaci sunan editan da ya yi mata hakan ba. A cikin bidiyon, Halima ta ce ta sha wahala a lokacin da take aiki a sashen, tana mai cewa wani babban jami’i ya nuna mata ƙiyayya ba tare da wani dalili ba, abin da ya sa ta shiga damuwa ta kan yi kuka akai-akai. Ta bayyana cewa ta sha barazanar korar aiki duk...
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci. Wasu sun rasa matsugunansu saboda rashin tsaro. Wasu kuma suna asibiti ba tare da kulawa ta gari ba—ko kuma ba za su iya zuwa ba saboda babu kuɗi a hannunsu. “Mutanen wannan kasa sun yanke shawara kan abin da za su yi a 2027. Shi ya sa muke farin ciki da kanmu—saboda muna tare da jama’a. Kuma jama’a sun san muna tare da su. Ba...
Bisa wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, hakan ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da Asusun Anita na Nijeriya ya samu karuwa tun daga watan Disambar shekarar 2021. Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, a watan Agusta Asusun ya ci gaba da karuwa wanda daga watan aka samu kimanin dala biliyan 1.46 zuwa yau daga dala biliyan 39.54 a ranar daya 19 ga watan Agustar shekarar 2025, suka karu zuwa i dala biliyan 41.00. Wannan ya nuna yadda karuwar Asusun ta kai zuwa kaso 3.69 a kasa da makwanni uku, da suka gabata. Bugu da karu, Asusun ya samu wannan karuwar ce, saboda yawan shigowar kudaden musaya na waje cikin kasar da...
“Wannan mummunan aikin yana nuna gazawar harkokin tsoro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a karkashin wannan gwamnati ta APC. Kazalika, yana zama manuniya kan tabarbarewar rashin tsaro a kasarmu, wanda ya sa har babban jami’in tsaro na kasa ya yi kira ga ‘yan kasa su koyi kare kansu,” in ji Abdullahi. Jam’iyyar ta kuma caccaki Shugaba Tinubu kan burus da abubuwan da suka fi muhimmanci, ta zarge shi da mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi kasa da kasa mai makon magance rikicin da al’ummar kasar nan ke fuskanta. “Abin takaici ne cewa maimakon fuskantar wadannan mummunan lamuran da wahalar da suka jawo, shugaban kasa Tinubu na ci gaba da tafiya kasashen waje, yana holewa a kasashen ketare,...
Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu. Shugaban ya kuma koka kan yadda aka shafe wadannan shekarun masu yawan gaske, ba tare da an yi masu wani gyara ba. Ya buga misali da kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na kasasehe kamar na Togo, Côte d’Iboire da Ghana, wanda suka kasance, Tashoshin Jiragen Ruwa da manyan Jiragen Ruwa ke sauka. A cewar Shugaban irin lalacewar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka yi, abu ne, da ya...
Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja. Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar. Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro. Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi Ya ruwaito...
“Zan iya tabbatar muku da cewa an kammala dukkan sharye-sherye na sauya shekan wani gwamna na PDP zuwa cikin APC. Ana ganin wannan gwamna a matsayin gwamna mai aiki tukuru da kwazo wanda yake da farin jini sosai a fagen siyasa a jiharsa. Abin da zan iya cewa a yanzu shi ne, ya kasance yana bangaren jihohin kuduncin Nijeriya ne. Mun gama dukan wasu shirye-shirye, muna jiran dawowar shugaban kasa daga kasashen waje don bayyana ficewarsa a hukumance,” in ji wata majiya. Duk da cewa majiyar bai ambaci sunan gwamnan da abin ya shafa ba, idan zama a iya tunawa dai PDP tana da matukar karfi a bangaren siyasar kudancin Nijeriya. A kudu maso gabas, Gwamnan Jihar Inugu, Peter...
Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa. Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba. Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima, rashin saka rigar iyo, amfani da jiragen ruwa marasa inganci, da kuma rashin bin ƙa’idojin tsaro. Duk da wannan, gwamnati ba ta ɗauki matakan tsaro ba. A halin yanzu, magidanta a Shagari da ƙauyuka maƙwabta na cikin tashin hankali suna jiran labari game da ‘yan uwansu da suka ɓace, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...