2025-10-15@02:15:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6920
«a yanke mata»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
’Yan bindiga sun sace wata matar aure da ’ya’yanta biyu a yankin Bareke-Egbe a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma da ke Jihar Kogi. ’Yan bindigar sun kai farmaki gidan wani manomi mai suna Tokpe Gody da misalin karfe 2 na dare ranar Juma’a, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su sace matarsa da ’ya’yansa biyu. Rahotanni sun ce Gody ya sha da ƙyar amma ya samu raunukan harbin bindiga a jiki da ƙafafuwansa, kuma yana karɓar magani a asibitin Egbe, inda likitoci ke cewa yana cikin mummunan yanayi. Wani mazaunin yankin mai suna Samuel Adeyemi ya ce: “Tokpe Gody manomi ne mai fama da yadda zai ciyar da iyalinsa. Ya tsira da ƙyar daga ’yan bindigar, amma matarsa da ’ya’yansa...
“Rushewar wannan gada na haifar mana da matsala sosai. Gwamnati ta taimaka ta gyara,” in ji Wayu Bamga, mazaunin yankin. Nanlong Nyas ya ƙara da cewa, “Gyaran da aka yi bai daɗe ba kafin ruwa ya sake lalata gadar.” Wasu direbobi kamar Umar Sa’adu da Abubakar Haruna sun ce duk lokacin da suka isa wurin gadar, sai sun biya ma’aikata su tura motarsu kafin su iya tsallaka rafi kana su ci gaba da tafiya. Rushewar Gadar Namne Ta Taraba Ta Tsayar Da Zirga-Zirga A Jihar Taraba kuwa, Gadar Namne dake kan hanyar Jalingo–Wukari ta rushe a watan Agustan 2024 bayan ruwan sama mai yawa, kuma har yanzu shekara guda bayan haka, babu wani gyara da gwamnatin tarayya ko ta jiha...
’Yan bindigar da ke addabar yankunan karkara sun kaƙaba sun ƙaƙaba musu haraji da ke kaiwa Naira miliyan 10 a Ƙaramar Hukumar Mashegu Jihar Neja. Rahotanni sun nuna cewa an umarci al’ummomin yankunan Babban Rami da Kaboji su su biya Naira miliyan biyu-biyu. Yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami an umarce su da su Naira dubu 500, yayin da aka umarci ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji su tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya. Haka nan, ana ƙaƙaba wa al’ummar Khizi an kaƙaba musu harajin Naira miliyan shida, da wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025. Wata mata ta banka wa kanta wuta a Bauchi Sharri Jonathan ke wa Buhari don lashe zaɓen 2027 —Garba Shehu Wani mazaunin yankin...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a Kasuwar Dutse Ultra-Modern Market, inda ya cika alkawarin gwamnatinsa na samar da tsaftataccen makamashi ga ‘yan kasuwa a jihar Jigawa. Aikin wanda Hukumar Samar da Tattalin Arzikin Kasa da Samar da ayyukan yi ta Jihar Jigawa ta gudanar, ya hada shaguna 300 da wutar lantarki daga na’urorin hasken rana da aka sanya a cikin kasuwar, inda kowane shago kuma an saka masa fanka amfani da hasken rana kyauta. Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da kasuwar a hukumance, Malam Umar Namadi ya ce shirin zai saukaka harkokin kasuwanci, da rage kashe kudi, da kuma bunkasa ribar ‘yan kasuwa. ...
Nijeriya za ta zama kasa mai girma duk da kalubale — Afenifere Kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere, ta nuna kwarin gwiwa cewa kasar za ta kasance mai girma. Sakon wannan kwarin gwiwa ya fito ne daga kakakin kungiyar Afenifere, Kwamared Jare Ajayi, a ranar Asabar yayin da LEADERSHIP Sunday ta tuntube shi a Akure, babban birnin Jihar Ondo. Kungiyar siyasa da al’umma mafi girma ta Yoruba ta ce ta dogara da wannan kwarin gwiwa “A kan alherin Allah, albarkatun da kasar ke da su, jajircewar da gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu ke nunawa wajen tabbatar da ci gaban Nijeriya, juriya da karfin hali na mutanen kasar, da kuma jimillar kwarewar da muka samu, kuma har yanzu muna samun sa.”...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta amince da daftarorin zaman lafiya da shugaba Donald Trump ya gabatar, wanda ganin zai kai ga kawo karshen yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin. A wata sanarwa da ta fitar kungiyar “ta bukaci janyewar dukkan sojojin Isra’ila, sannan ta saki dukkan Isra’ilawan da suke tsare a hannunta, masu rai da matattu.” Kungiyar, ta kuma ce sakin zai faru “idan har an tabbatar da yanayin tsarin musayar.” Don haka, kungiyar ta ce a shirye take ta shiga tattaunawa da masu shiga tsakani domin cimma manufar. Haka zalika, Hamas ta ce ta amince da mika ragamar mulkin zirin ga wata hukumar Falasdinu mai cin gashin kanta. Duk da haka, kungiyar ta bayyana...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadin cewa amincewa da takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Iran ba bisa ka’ida ba ya sabawa dokokin kasa da kasa, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su bijirewa haramtattun takunkuman. Jakadan Iran a Colombo Alireza Delkhosh ya bayyana cewa, gargadin na ministan harkokin wajen kasar na kunshe ne a cikin wasikun da ya aike wa takwarorinsa na Sri Lanka da Maldives. Araghchi ya yi kira ga takwarorinsa na kasashen da su dau mataki mai tsanani kan takunkumin da Amurka da kasashen yammacin Turai suka kakaba iran, bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar a ranar 28 ga watan Satumba sake dawo da takunkuman da aka kakaba wa Iran,...
Kasashen duniya sun fara yabawa kungiyar Hamas kan amincewa da shirin zaman lafiya na Trump. Qatar mai shiga tsakanin Isra’ila da Hamas a yakin Gaza ta yaba da matakin da kungiyar ta dauka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Maged al-Ansari, wanda kuma ya goyi bayan kiran da Donald Trump ya yi na tsagaita bude wuta ya ce ” Qatar na maraba da sanarwar da Hamas ta yi cewa ta amince da shirin na Shugaba Trump.” A nata bangare Masar tana kallon wannan a matsayin “ci gaba mai kyau.” Kuma tana fatan a sakamakon haka, bangarorin biyu “za su himmatu wajen aiwatar da shirin Shugaba Trump da kuma kawo karshen yakin,” in ji ma’aikatar harkokin wajen kasar a shafin Facebook. Ita...
Shugaban Madagaska Andry Rajoelina ya bayyana cewa gagarumar zanga-zangar da akeyi a kasar, na da nufin “yi masa juyin mulki,” ne. A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mista Rajaolina, ya yi ikirarin cewa matasan da suka yi gangami a kan tituna, da tun farko suke yin Allah-wadai da katsewar wutar lantarki da ruwan sha, wasu ’yan siyasa ne ke amfani da su. A jawabi na tsawon mintuna ashirin da aka watsa kai tsaye a shafinsa na Facebook, wanda shi ne na farko tun soma fara zanga-zangar, Shugaban kasar ta Madagaska ya tabbatar da cewa matasan da ake wa lakabi da ‘’G Z’’, ‘yan adawa” ne ke amfani da su wajen neman kawar da shi daga mulki....
Mista Fall ya jagoranci tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta kunshi wakilai daga UNICEF, UNESCO, UNDP, UNFPA, da mata na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron. Ya jaddada cewa canjin al’umma ya ta’allaka ne akan jarin dan’Adam musamman ta hanyar ilmantar da ‘ya’ya mata da karfafa wa mata. Ya kara da cewa, “tare da gwamnati da abokan huldarmu, mun himmatu wajen kawar da duk wani cikas da ke hana yara, musamman ma masu rauni damar samun ilimi”. Fall ya gano muhimman abubuwan da ke kawo cikas ga ilimi a Nijeriya, da suka hada da rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, sauyin yanayi, da kuma ka’idojin zamantakewa da al’adu. Ya yi kira da a kara himma wajen inganta daidaiton jinsi...
Fim na Nezha 2 na kasar Sin ya kara samun lambar yabo. A gun bikin nune-nunen littattafan zanen hotuna na kasa da kasa na kasar Sin karo na 18 da aka kaddamar a jiya 2 ga wannan wata, fina-finai guda 10 ciki har da fim na Nezha 2, da The Legend of Hei 2, da Curious Tales of a Temple sun samu lambobin yabo na Golden Dragon na kasar Sin karo na 22. Ya zuwa yanzu, fim na Nezha 2 ya samu kudin tikitin kallo Yuan biliyan 15.44 a duniya gaba daya, yawan kudin tikitin fim din da aka samu a kasashen waje ya kai Yuan miliyan 400. Fim din ya hau matsayi na farko na fim na kagaggun hotuna...

Sabbin Gonakin Da Za A Magance Zaizayewar Kasa A Sin A Karshen Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Na 14 Sun Kai Muraba’in Kilomita 340,000
Bisa labarin da ma’aikatar harkokin albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, ana sa ran cewa, fadin sabbin gonakin da za a shawo kan matsalar zaizayewar kasa a Sin a karshen shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14 ya kai muraba’in kilomita dubu 340, fadin gonakin da aka tabbatar da yanayin ruwa da kasar da ke cikinsu ya kai kashi 73 cikin dari. Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, a yayin gudanar da shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, an kiyaye kyautata yanayin zaizayewar kasa a kasar Sin, kuma an cimma burin rage fadin gonakin da suka gamu da matsalar, da kuma rage illar da ruwa da iska suka haddasa wa gonaki....

Jami’in MDD: Kayataccen Hutun “Golden Week Plus” Na Kasar Sin Ya Nuna Tasirin Yawon Bude Ido A Duniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai, lamarin da ya sa yaƙin ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaron ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya rubuta. 2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe Jonathan, ya ce rikicin Boko Haram ya bambanta da sauran matsalolin da Najeriya ta fuskanta kamar na ’yan tawayen yankin Neja Delta da rikicin addini ko ƙabilanci. Ya bayyana cewa Boko Haram sun samu goyon baya daga ƙasashen waje, suna...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce Boko Haram sun fi sojojin Najeriya makamai, lamarin da ya sa yaƙin ya zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin tsaron ƙasar nan. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin ƙaddamar da littafin Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum da tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya), ya rubuta. 2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe Jonathan, ya ce rikicin Boko Haram ya bambanta da sauran matsalolin da Najeriya ta fuskanta kamar na ’yan tawayen yankin Neja Delta da rikicin addini ko ƙabilanci. Ya bayyana cewa Boko Haram sun samu goyon baya daga ƙasashen waje, suna...
A wani sabon hari rahotanni sun ce an kashe wani manomi ɗaya yayin da wasu ’yan bindiga suka sace wasu biyar a Tungan-Gari da ke Ƙaramar hukumar Kontagora a gundumar Neja ta Arewa a jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, ’yan bindiga sun kai wa al’ummar garin hari ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Alhamis inda suka yi ta harbe-harbe na tsawon sa’o’i ba tare da an ƙalubalantarsu ba. Remi Tinubu ta ƙaddamar da Asibitin Koyarwa na Tarayya a Gombe NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su akwai mata huɗu da namiji ɗaya. “Ba mu da wani zaɓi a yanzu da ya wuce mu...
Bayanan sun bayyana cewa; “Jimillar makarantu 228 suka ci gajiyar shirin, inda kimanin dalibai 829,423 suka nema. Ya zuwa yanzu kuma, dalibai 510,378 ne suka samu wannan tallafi na bayar da rance. “Zuwa 10 ga watan Satumba, an biya kimanin Naira 53,801,717,293.00 a matsayin kudaden makaranta na daliban, yayin kuma da aka biya Naira 45,751,360,000.00 a matsayin alawus-alawus na daliban. Idan aka tattara kudaden baki-daya, jimillarsu ta kama Naira 99,553,077,293.00,” a cewar rahoton. Duk da nasarar da aka samu a fadin kasar, shirin ya fuskanci kalubale wajen ganin an yi adalci a rabon a dukkanin shiyoyin fadin kasar guda shida da ake da su. Alkaluman da LEADERSHIP ta tattara a watan Mayun 2025, sun nuna dimbin gibin da ke tsakanin...
Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar da sabon Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da aka gina a garin Kumo, Ƙaramar hukumar Akko ta Jihar Gombe An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne tare da halartar Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da kuma Ministan Kula da Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate. NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe A jawabinta, uwargidan shugaban Ƙasar ta ce wannan asibiti na nuna sakamakon jagoranci irin na hangen nesa ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Ta ce, asibitin zai ƙara inganta damar samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Gombe da ma maƙwabtan jihohi, tare da...
Wannan sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, ya sanya wasu na ganin kamar tana fargabar fitowar takarar Jonathan din ne. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan al’amari ya nuna yadda ake samun ƙarin rashin jituwa tsakanin shugabancin kamfanin da ƙungiyoyin ƙwadago, duk da cewa matatar ana ganin ta zama muhimmin ginshiƙi wajen cikar burin Nijeriya na cin gashin kai a fannin makamashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Farfesa Adeyeye ta jaddada ƙudirin NAFDAC na kare lafiyar ƴan Nijeriya, tare da shawartar al’umma da su rika amfani da kayayyaki da aka tabbatar da rajistarsu a hukumar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) a ranar Alhamis ta lalata magunguna da kayayyakin jabu, da wa’adin aikinsu ya ƙare da marasa inganci, da jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan 15 a garin Ibadan na Jihar Oyo. Darakta-Janar ta Hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta sanar da hakan a lokacin da aka lalata magungunan a Ibadan, babban birnin jihar. 2027: Dalilin da ya sa Atiku bai ayyana takararsa ba — Hadimi An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko Adeyeye wanda Daraktan bincike da tabbatar da doka na NAFDAC, Martins Iluyomade ya wakilta, ya ce hukumar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa abinci, magunguna, kayan kwalliya, na’urorin likitanci, sinadarai...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai ayyana cewa ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba. Yayin da wasu ’yan siyasa kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi suka nuna sha’awar tsayawa takara, Atiku ya ce “lokaci bai yi ba” domin yanke hukunci. Isra’ila ta kame dukkan jiragen ruwan da ke koƙarin kai kayan agaji Gaza An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko Kwanan nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya faɗa wa BBC Hausa cewa zai bai wa matashi damar tsayawa takara. Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta. Amma hadiminsa, Paul Ibe, ya ce ba a yi wa maganganun Atiku kallo na tsanaki ba, an fahimce su ba daidai ba. Ibe, ya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari. Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro...
Yayin da yake kira ga ‘yan kasa kan cewa, kada su karaya ko fitar da rai daga rabo, Atiku ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa; shekarar 2027, wata dama ce da za a iya amfani da ita wajen kawar da wannan mulki na zalunci, domin tabbatar da ganin gobenmu ta yi kyau. “Babban kyawun demokuradiyya shi ne, ‘yancin samun damar kada kuri’a, duk wadanda ake zalunta; musamman mutanenmu a halin da ake ciki yanzu, za su samu damar kawar da wannan azzalumar gwamnati a zabe mai zuwa. Babu shakka, wannan shi ne ikon da babu wani dan takara da zai iya kwacewa daga al’umma,” in ji shi. Atiku ya kara da cewa, a shekara 65; Nijeriya ta kasance kasa wadda...
Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku. Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne. “Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu. Sai dai ya bayyana cewa babu...
Ita dai wannan yarjeniyar wadda wanda mamallakin karamin Jirgin Sama, zai bayar da hayar Jirginsa na Sama, ba tare da ma’aikata da kula da Jirgin da kuma yin inshore ba. Akasarin wannan yarjeniyar ana yinta da takardar shedar mamallakan Jiragen Samn wato AOC. “Hakan ya nuna cewa, mun fara shiga cikin matakin fafada harkar kasuwanci mai zaman kansa ne kuma za mu yi hakan a bangaren Kamafnin Jirgin Sama na Air Peace ba ne, sai dai kawai, a bangaren sauran Jiragen Sama,” A cewar Manajin Darakantan. A shekarar 2024 ne dai, aka cire Nijeriya daga cikin jeren kasasshen da suka yi kaurin suna wajen saba yarjeniyar, ta bayar da hayar Jirgin Sama. Kazalika, hakan ya biyo bayan kiyaye daukacin ka’idojin...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Filato, ta sha alwashin ba da misali da masu yanke hukunci da kansu ba tare da barin doka ta yi aikin ta ba. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, CP Emmanuel Adesina ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Jos yayin da suka kama wasu manyan mutane tara (9) da ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane da wasu laifuka daban-daban. Ku tuna cewa a wasu lokutan a cikin watan Agustan wannan shekara ta 2025, an kashe jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a karamar hukumar Bassa sakamakon aikata irin wannan danyen aiki. An bayyana cewa dan sandan ya tafi...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya ziyarci Oke Ode da ke karamar hukumar Ifelodun domin jajanta wa al’umma da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon hare-haren da masu garkuwa da mutane suka kai kwanan nan. A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu. Ya kuma yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, sannan kuma ya baiwa al’umma tabbacin dawo da zaman lafiya cikin kankanin lokaci. Sanarwar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da jaje ga daukacin al’ummomin da aka samu cikin wannan rikici — daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi. A cewarsa ana tanadin komai don rage illar hare-haren da kuma tabbatar da kawo...
Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce ta ware naira biliyan biyu domin biyan kudaden tallafin karatu da alawus alawus na guraben karatu a jihar. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kaddamar da biyan alawus-alawus na shekarar 2023/2024 da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta karamar hukumar Akwanga ta jihar. Gwamnan a lokacin da yake kaddamar da shirin raba kudaden ya jaddada cewa baya ga biyan kudaden NECO, gwamnatin jihar tana biyan dalibai sama da 155 tallafin karatu na kasashen waje da sama da dalibai 30,000 a fadin kasar nan. Shima da yake nasa jawabin, kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Dokta Danladi Jatau wanda shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ilimi Mista Abel Yakubu Bala...

Shugaban Gidauniyar Malala, ya jaddada kudirin gidauniyar na bunkasa ilimin yara mata a fadin Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya. Da yake jawabi, shugaban gidauniyar Malala, Mista Ziouddin Yousafzai ya yaba da kyakkyawar tarba da aka yi masa tare da tawagarsa, inda ya bayyana Masarautar Zazzau a matsayin babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da manufofin Gidauniyar gaba. Ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da cibiyoyin gargajiya domin bunkasa samun ilimi da karfafawa ‘ya’ya mata samun damar da suke da ita. A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yabawa gidauniyar Malala bisa ci gaba da tallafawa wajen inganta ilimin yara mata, musamman a Arewacin Najeriya. Sarkin ya yi...
Hukumar Kwastam ta Kano/Jigawa ta kama jimillar kafso guda 261,750 na Polyglycine (miligiram 300) da allunan Tramadol hydrochloride 228,700 (miligiram 225) da aka boye a cikin buhunan jumbo guda biyar. Shugaban hukumar kwastam na yankin Kano, Dalhatu Abubakar, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce an boye magungunan ne a cikin fakiti 35 na Polyglycine da kuma allunan Tramadol 28. Yayin da yake mika haramtattun magungunan ga wakilin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, Konturola Dalhatu Abubakar, ya ce abubuwan na da illa ga lafiya da suka hada da lalata gabobi, jaraba, da rashin natsuwa, musamman a tsakanin matasa. Abubakar yayi gargadi game da illolin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya isa birnin bandar Abbas a jiya alhamis gari na 10 ke nan a ci gaba da ziyarar aiki yi a fadin jihohin kasar, da yake kaddamar da ayyukan ci gaba da aka kammala. Ziyarar ta shugaban kasa a jihohi tana taimakawa wajen samar da cundanya tsakanin gwamnati da jama’a, kuma tana bawa shugaban kasa dama gane ma idonsa irin kalubalen da ake fuskanta da kuma bada umarnin kawar da duk wani abu da ka iya kawo cikas wajen ayyukan raya kasa. Gwamnatin iran ta mayar da hankali wajen karfafa damammaki a bangaren ilimi da ci gaban tattalin Arziki a jihohi daban daban, ziyarar lardin Hormuzgan wani bangare ne na babban...
Fira ministan kasar malesiya Anwar Ibrahim da na Pakistan shehbaz sharif suna tir da matakin da HKI ta dauka kan jiragen tawagar Sumud Flotilla ajiya Alhamisi a shafukansu na X , bayan da jagororin tawagar suka sanar da cewa sojojin HKI sun kama jiragen ruwa guda 14 dake dauke da yan kasashen waje da kayayyakin agaji zuwa yankin Gaza. Haka zalika shugaban kasar Bolivia da takwaransa na kasar Cuba suna yi Allah wadai da Isra’ila , haka su ma ministocin harkokin wajen spaniya jose manueal dana kasar irish simon harris sun bayyana damuwarsu matuka game da halin da tawagar ta flotilla ke ciki a hannun Israi’la na kokarin hana su isa yankin gaza. Ita dai tawagar Sumud Flotilla tana dauke...
Wani abu da ya ja hanklan mutane shi ne, irin muggan makaman da ‘yan bindigar suka hallara da su a wajen kulla yarjejeniyar, wadanda kuma babu wani mahaluki da ke da ikon kwace makaman daga hannunsu, a yayin kulla yarjejeniyar, ta jeka nayi ka. Kazalika, a cikin daya daga cikin faifan Bidiyon, an ga yadda daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar ya yi bazaranar shedawa gwamnati da sauran jami’an gwamnatin da suka halarci wajen kulla sulhun cewa, idan har gwamnati ta kuskura ta kashe ‘yan bindiga dubu goma, suma za su hallaka adadin mutane kamar hakan. Wasu ‘yan Nijeriya dai, sun yi ittifakin cewa, kasar nan, ta koma tamkar, a hanun tafin ‘yan bindigar. Kulla wannan yarjeniyra dai, ta nuna...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI), harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen daukar hoto. A da, mutane kan je shagon daukar hoto domin samun hoto mai kyau na fasfo ko na bikin aure ko bikin suna, ko kuma kowane irin taron biki. Amma yanzu, manhajojin AI suna ba wa mutane damar kirkirar irin wadannan hotuna daga wayoyin su ko kwamfuta cikin mintuna kadan ba tare da zuwa shagon daukar hoto ba. Wannan yanayi na iya jefa...
Ministar kula da shari’a da harkokin majalisar dokoki da hakkin mata ta kasar Sao Tome and Principe Vera Cravid ta yi kira a maida dangantakar dake tsakanin kasarta da kasar Sin a matsayin misalin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, domin dangantakarsu tana da tarihi mai zurfi da kuma samun ci gaba a zamanin yau. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”. Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya. Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar. “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
Gomman matasa a Jihar Kano sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a ranar Alhamis domin bayyana goyon baya ga Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP AI Bakori. Matasan da suka gudanar da zanga-zangar sun daga kwalaye da alluna dauke da sakonnin “A bar mana CP”, “Mutanen Kano suna bayan CP,” da “Gwamna Abba Kabir Yusuf ka kyale mana CP.” Mun kama wani mahaifi kan yunƙurin safarar ‘yarsa zuwa Iraƙi — NAPTIP Babu wanda na cewa zan janyewa takara a 2027 — Atiku Zanga-zangar na zuwa ne dai bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya caccaki Kwamishinan ’Yan Sandan kan ƙaurace wa farerin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Larabar da ta gabata. Yayin da yake jawabi a bikin da...
A nasa jawabin, gwamnan ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya tsige CP Bakori, yana mai nuni da rashin halartar rundunar ‘yansanda daga faretin bikin a matsayin rashin mutuntawa da tsoma baki cikin siyasa. Sai dai ga dukkan alamu, kalaman gwamnan sun janyo rashin amincewar jama’a musamman a tsakanin matasan Kano. Zanga-zangar ta ranar Alhamis ta kasance cikin kwanciyar hankali da bin doka da oda, inda masu zanga-zangar ke jaddada muradin su na CP Bakori ya ci gaba da rike mukaminsa da kuma ci gaba da aikinsa ba tare da cikas na siyasa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan. Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun jaddada aniyarsu ta watsi da duk wata barazanar makiya tare da alwashin mayar da martani mai tsanani fiye da harin alkawarin gaskiya da ya gabata A cikin wani sako mai kakkausar murya, Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun yi gargadi ga haramtacciyar kasar Isra’ila game da aikata sabbin kura-kurai tare da jaddada cewa duk wani hari da za a kai wa Iran zai fuskanci martani mai tsauri fiye da martanin Alkawarin Gaskiya na baya. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki matakin soji da na siyasa bai daya dangane da tunkarar barazanar da take fuskanta da kuma matakin da ya biyo bayan sake maido da takunkumin da kare kan kasarta, a daidai...
Masar ta jaddada goyon bayanta ga zaman lafiyar Sudan tare da yin watsi da matakan bangare guda kan kogin Nilu Kasar Masar ta jaddada cikakken goyon bayanta ga zaman lafiyar kasar Sudan da kuma yankinta a jiya Laraba, tare da tabbatar da hadin kan matsayar kasashen biyu da kuma kin amincewa da matakan bangare daya kan kogin Nilu. Wannan dai ya zo ne a wata ganawa da ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty da shugaban majalisar gudanar da mulkin Sudan Abdel Fattah al-Burhan suka yi a birnin Port Sudan, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar. Abdel Aty ya ce ziyararsa ta uku zuwa Port Sudan cikin shekara guda sako ne na nuna goyon baya...
Rundunar ta kuma bayyana cewa, a ranar 30 ga watan Satumba da misalin karfe 11:15 na safe, wata tawagar rundunar ta kama wasu mutane biyu a filin tirela na Dangauro. Sanarwar ta kara da cewa, “An samu wadanda ake zargin dauke da buhu bakwai da ake zargin kayan maye ne wanda aka fi sani da ‘Akuskura.’ Ko wanne buhu na dauke da kwalabe 350, adadinsu ya kai kwalabe 2,450, wanda kudinsu ya kai ₦2,450,000. SP Kiyawa ya kara da cewa, bisa hadin gwiwar hukumomin tsaro, “Rundunar ta mika wadanda aka cafken da kayayyakin su da darajarsu ta kai N120,000,000 ga hukumar NDLEA, ta jihar Kano, domin ci gaba da bincike.” Hakazalika, jami’an rundunar sun kama wasu fitattun...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta yi wata babbar nasarar kama masu baiwa ’yan bindiga makamai da kama wani fitaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi da kuma dillalan makamai ba bisa ƙa’ida ba a wurare daban-daban a faɗin jihar. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, jami’an ’yan sanda da ke aiki da sashen bayanan sirri sun kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Franklin Ozo a Zariya. Gwamna Fubara ya kori duk Kwamishinonin jihar Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa An kama shi da ƙunshin ƙwayoyin Exol guda 500, na miliyoyin Naira. “Bincike na farko ya nuna cewa,...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori dukkan Kwamishinoni da sauran masu riƙe da muƙamai a gwamnatinsa. A cewar wata sanarwa da aka fitar a Fatakwal babban birnin jihar a yammacin Laraba ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi matakin korar ya fara aiki nan take, kuma ya biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli da ta yanke na baya-bayan nan. Matan Sojojin da aka tsare sun nemi a yi wa mazajensu afuwa 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Gwamnan, a yayin wani zama da ya yi da hadimansa domin murnar cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai a gidan gwamnati da ke Fatakwal, ya gode wa jami’an...
Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana matuƙar alhininta kan mummunan hatsarin kwale-kwale da ya faru a kan Kogin Neja, inda aƙalla mutum 26 suka rasa rayukansu. Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Femi Fanwo ya fitar a ranar Laraba ta ce wannan mummunan lamari ya rutsa da ‘yan kasuwa da suka taso daga ƙaramar hukumar Ibaji ta jihar Kogi zuwa kasuwar Ilushi a jihar Edo. Gwamna Ahmed Usman Ododo ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa ciki har da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha da su haɗa kai da ƙananan hukumomin yankin, wajen bayar da tallafi da kuma agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa. Gwamna Ododo ya ƙara da ba da tabbacin cewa gwamnatin...
Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
Matan Sojoji da aka tsare bisa laifuka daban-daban a yaƙin da ake yi da ’yan Boko Haram ko Ƙungiyar ISWAP a garin Maiduguri jihar Borno, a bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin soja da su tausaya musu ta hanyar yi wa mazajensu afuwa. Matan da yawansu ya haura 30 tare da wasu yara ’yan ƙasa da shekara biyu da suka haɗa da ‘yan uwa da abokan arziki sun ziyarci cibiyar ’yan jarida ta Nijeriya (NUJ) da ke Maiduguri a ranar Laraba don miƙa wannan koke na su. HOTUNA: Yadda Boko Haram ta lalata Kwalejin Kagara da ke Neja 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a...
Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata. Mazauna yankin sun bayyana cewa halin da hanyar take ciki ya jefa su cikin matsanancin rayuwa, musamman mata masu juna biyu da ke tilasta musu hawa babura domin neman kulawa a wajen unguwar, kasancewar babu asibiti a yankin. Ɗaya daga cikin mazauna, Rashida Shehu, wadda ke da juna biyu, ta ce ta ji rauni a lokacin da take kokarin bin hanyar zuwa gari domin kula...
Makarantar Kwalejin Kagara da ke Jihar Neja, wadda ta yi fice wajen yayi ɗalibai masu hazaƙa, yanzu ta zama kufai. A shekarar 2021, Boko Haram ta kai hari makarantar ta sace aƙalla dalibai da malamai 27. 2027: Zan iya haƙura da takara in mara wa matashi mai jini a jika baya – Atiku Jiya na yi barci mai daɗi bayan na soke faretin samun ’yancin kai Bayan haka kuma an sake kai hare-hare a yankin, lamarin da ya tsoratar da ɗalibai, tare da hana su komawa makaranta. Yanzu makarantar ta daina aiki, inda aka mayar da ita sansanin soja. Wakilin Aminiya, Abubakar Akote, ya ziyarci makarantar, inda ya ɗauki hotunan da ke nuna halin da makarantar ke ciki a yanzu....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashen duniya na ci gaba da yin Allah wadai da farmakin da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan jiragen ruwan ‘yan fafatuka dake dauke da kayan agaji ga al’ummar Gaza. Kungiyoyin Falasdinawa, kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin Turai sun bi sahu inda sukayi tir da harin baya bayan nan da aka kai wa jirgin ruwan Global Sumud Flotilla a cikin ruwan kasa da kasa. Hamas ma ta yi Allah wadai da farmakin kan Global Sumud Flotilla a iyaka da Gaza wanda ta danganta a matsayin “laifi na fashin teku da ta’addanci kan fararen hula”, tana mai kira ga “dukkan masu kare ‘yanci a duniya” da su yi Allah wadai da harin. Kungiyar Jihadin Islamic ta Falasdinu...
Kotun koli ta Soji a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa bisa samunsa da laifin cin amanar kasa da laifukan yaki ciki har da jagorantar kungiyar ‘yan tawayen M23. An samu Kabila da laifuffuka da dama da suka hada da shiga wani yunkuri na tayar da kayar baya, cin amanar kasa, azabtarwa, da kuma laifukan yaki, a cewar hukuncin da kotu ta yanke a Kinshasa, babban birnin kasar. An fara shari’ar tasa ne a watan Yuli, bayan da majalisar dattawa ta tsige masa rigar kariya a watan Mayu, bisa zarginsa da hannu a ta’asar da ‘yan tawayen M23 suka aikata a lardunan gabashin Congo. Kotun ta ce Mista Kabila “ya gudanar da tarurrukan...
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan bukatar hakan ta taso, zai iya janye burinsa na takarar shugaban kasa a 2027 don mara wa matashi baya. Atiku, wanda jigo ne a haɗakar jam’iyyun adawa ta ADC, ya bayyana hakan ne a wata hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba. NAPTIP ta kama mahaifin da ke ƙoƙarin safarar ’yarsa zuwa Iraƙi ci-rani Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027, sai ya ce lokacin tattauna hakan bai yi ba. Ya ce, “Lokacin hakan bai yi ba tukuna. Idan lokaci ya yi, zan yanke shawara. Abin da muke yi yana da amfani ga kasa....
Ya ce bambancin Nijeriya na ƙabilu, addinai da al’adu bai kamata a ɗauka a matsayin matsala ba, illa ma ya zama ƙarfin ƙasar. “Idan aka tafiyar da bambancin nan da kyakkyawan shugabanci, Nijeriya za ta samu girmamawa a duniya,” in ji shi. Obasanjo ya jaddada cewa ilimi shi ne tushen ci gaba, ba tare da la’akari da ƙabilanci, addini ko al’ada ba. Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato Ahmed Aliyu, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, da kuma Bishop Matthew Kukah saboda jajircewa wajen haɗa kan jama’a da zuba jari a ilimi. Bishop Kukah ya bayyana cewa cibiyar da mai bayar da tallafi Afe Babalola ya gina za ta bayar da horo kyauta ga kowa a fannin amfani da kwamfuta, ƙirƙirar manhajoji,...
Iran ta yi kira da a gaggauta kakaba wa gwamnatin Isra’ila takunkumi mai tsauri kan kisan kiyashin da take ci gaba da yi a zirin Gaza, sakamakon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a baya-bayan nan. Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya karo na 60 a birnin Geneva, wakilin kasar Iran Ali Bahreini ya yi ishara da rahoton da kwamitin bincike mai zaman kansa na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar kan yankin Falasdinu da ta mamaye a watan Satumba, wanda ya kammala da cewa Isra’ila ta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a zirin Gaza. Hukumar, wacce ke binciken abubuwan da suka faru tun ranar 7 ga Oktoba 2023, ta gano...
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce soke faretin zagayowar ranar ’yancin kai karo na 65 da sojoji ke yi ya ba shi damar yin lafiyayyen barci da kuma yin kyakkyawan kari a ranar Laraba. Aminiya ta rawaito cewa Gwamnatin Tarayya ta soke bikin da aka shirya domin murnar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, daya ga watan Oktoba. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin. “Gwamnatin Tarayya na sanar da soke bikin zagayowar ranar ‘yancin kai da aka shirya domin murnar cikar ƙasar shekara 65 a ranar...
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yaba da hadin kai, tsayin daka, da ci gaban Gombe da Najeriya a daidai lokacin da jihar ke cika shekaru 29 da samun ‘yancin kai tare da bikin cikar kasar shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin sakon fatan alheri mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin jihar Gombe, Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa na mai da jihar Gombe ta zama cibiyar zuba jari da ci gaba mai dorewa, wanda aka dora a kan shirin ci gaban jihar na shekaru 10 (DEVAGOM). Alh Inuwa Yahaya ya bayyana irin nasarorin da aka samu a karkashin jagorancin sa, da suka hada da inganta harkokin...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar. A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata. “A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Ismail Falgore, ya mika sakon taya murna ga ‘yan Najeriya a daidai lokacin da kasar ke cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar, shugaban majalisar ya bayyana tafiyar Najeriya bayan samun ‘yancin kai a matsayin wanda ke cike da kalubale da dama, yana mai cewa idan aka yi hangen nesa da tsare-tsare, makoma mai haske tana nan kusa. Ya lura cewa duk da matsaloli, Najeriya a yau tana tsaye a matsayin kasa mai mutane sama da miliyan 230, galibi matasa da kuzarin da ke da karfi na musamman da kasashe da yawa ba su da su. ...

‘Yan siyasa a Nijar sun nemi da su yi aiki tare domin tabbatar da ba a samu cikas a zaben kananan hukumomi ba
An shawarci ‘yan siyasa a jihar Neja da su kiyaye mutuncin da aka san jihar da su domin tabbatar da nasarar zaben kananan hukumomin jihar da ke tafe. Zaben da aka shirya gudanarwa a ranar farko ga watan Nuwamba na wannan shekara, ya yi alkawarin za a yi shi cikin gaskiya ba tare da wata tangarda ba, tare da shirye-shiryen da tuni aka yi nisa. Mai ba Gwamnan Jihar Neja shawara ta musamman kan harkokin siyasa Alh Mohammed Nma Kolo ne ya bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna. Alh Nma Kolo ya kuma tunatar da su cewa a kowace gasa dole ne a samu wanda ya yi nasara...
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya taya al’ummar Jihar Nasarawa murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai da kuma Jihar Nasarawa da ta cika shekara 29 da samun ‘yancin kai. Wata sanarwa da ta sanyawa hannu kuma ta raba wa manema labarai, mashawarci na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai Malam Ibrahim Adra ta ce al’ummar kasar nan sun samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori na rayuwar dan Adam, haka nan kuma jihar nasarawa ta samu ribar dimokuradiyya tun bayan kafa jihar da marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya kafa. Sanarwar a yayin bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai a yau, ta yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da...

Kwara ta bukaci a sanya ido sosai, yayin da jami’an tsaro ke kara kai hare-hare a maboyar masu garkuwa da mutane
Gwamnatin jihar Kwara ta shawarci al’ummar da ke kewayen kananan hukumomin Ekiti, Ifelodun, Isin, Oke Ero, da Irepodun, da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita harkokin a wuraren da sojoji ke aikin musamman. A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Bolanle Olukoju ya fitar t cea shawarar ta biyo bayan tsaurara matakan tsaro da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi a garuruwan Kogi da Kwara, inda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da su. “Muna kira ga jama’a da su yi taka-tsan-tsan tare da takaita zirga-zirgar ababen da suka dace kawai, wato don gudun kada a kama su ba tare da saninsu ba, yayin da masu garkuwa da mutane ke tserewa maboyarsu, ba...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana damuwarta kan yadda likitoci ke kin zuwa aiki musamman a lokutan da suke kai ziyara wuraren kiwon lafiya da ba a shirya ba. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar, Suleiman Isah ya fitar, ya ce kwamishinan lafiya Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta yi gargadi ga likitoci a babban asibitin garin Gusau, bayan da suka gano rashin zuwan su a wata ziyarar ba-zata. Dakta Maradun, wadda ta kai ziyarar bazata asibitin, ta ce ta firgita da ganin cewa babu wani likita da ke bakin aiki, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abu da ke faruwa a baya. Ta yi Allah wadai da lamarin a matsayin...
Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Julius Ishaya Lepes, ya rasu. Ishaya, ya riƙe mukamin Kwamishina a farkon gwamnatin Inuwa Yahaya na tsawon shekaru huɗu, amma ya yi murabus domin yin takara. Tinubu ya buƙaci ’yan Najeriya su daina yi wa ƙasar mummunan fata Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Ya rasu bayan a ranar Laraba, bayan fama da ciwon ƙoda. Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana baƙin cikinsa kan rasuwar marigayin. A cikin saƙon ta’aziyyarsa, gwamnan ya ce Julius Ishaya, mutum ne nagari mai basira da jajircewa. Hakazalika, ya ce ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jam’iyyar APC a jihar, musamman kafin kafa gwamnatinsa. Ya ce a lokacin da Ishaya yake Kwamishinan...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi ’yan Najeriya da su daina yin maganganu ɓatancin ga ƙasar. Ya ce Najeriya ƙasa ce mai girma, mai cike da damar ci gaba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ’Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace 9 a Neja Shugaban ya yi wannan jawabi ne a daren ranar Talata a Jihar Legas, lokacin da aka sake buɗe Cibiyar Al’adu ta Ƙasa (National Theatre) da aka gyara. Ya ce dole ne ’yan ƙasa su yi imani da Najeriya kuma su haɗa kai domin gina ta. “Ku daina yin magana mara kyau game da Najeriya. Mu mutane ne masu alfahari, jarumai, da jajirtattu. Mu...
Manyan garuruwan da suka shiga cikin wannan jerin sun haɗa da Mubi, Gusau da Azare. Ma’aikatar ta roƙi jami’an gwamnati a jihohi da sauran masu ruwa da tsaki da su sa ido sosai kan halin da ake ciki kuma su bayar da rahoto a kan lokaci. Haka kuma, ta shawarci jama’a da ke zaune kusa da koguna ko rafuka su ɗauki matakan kariya ko su bar waɗannan wurare domin guje wa ambaliyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemah Mohajerani ta fayyace cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta maraba da yaki, amma tana ci gaba da shirye-shiryen tsaro mafi girma don kare kanta. Ta kara da cewa Tehran ta bayar da shawarar tattaunawa da Amurka kai tsaye a wata ganawa tare da ministocin Turai, amma wakilin Amurka Steve Witkoff ya ki isa a lokacin da aka tsara. Mai magana da yawun gwamnatin ta Iran ta kuma bayyana cewa, kasarta na ci gaba da musayar sakwanni kai tsaye da kuma a fakaice, kuma tana ci gaba da kokarinta, sai dai kuma gwamnatocin yammacin duniya su ne ke warware alkawuran da suke dauka. A nasa bangaren, sakataren majalisar kula da harkokin tsaron kasar,...
Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma. Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya. Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki? Wannan shine batun...
Aƙalla mutum huɗu suka rasu yayin da aka sace wasu tara a wani hari da ’yan bindiga suka kai a ƙauyuka da dama na Ƙaramar Hukumar Magama; ciki har da garin Ibeto a Jihar Neja. Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa mutum huɗu aka kashe, an jikkata wasu 11, sannan an yi garkuwa da mutum tara. Rashin Tsaro: An rufe makarantu sama da 180 a Arewacin Najeriya Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Daga cikin waɗanda aka sace har da wanda ya wallafa rubutu a Facebook kan hare-haren ’yan bindiga a yankin, Barista Isyaku Muhammad Danjuma. Rahotanni sun nuna cewa wasu masu bai wa ’yan bindiga bayanai ne suka sanar da...
Collins mutum ne mai jajircewa da azama. Bayan gaza cin nasara da ya yi a ƙoƙarinsa na kafa tarihi a shekarar 2024, ya ɗauki tsawon shekara guda yana ɗaukar horo da shiri sosai domin wannan rana. Ya ce, “Na koyi darussa da dama daga ƙoƙarina na farko. Yanzu na shirya sosai. Tare da goyon bayan Indomie, domin mu kafa tarihi.” A wajen Collins, fentin fuska ba nishaɗi ba ne kaɗai ba, fasaha ce da ke bayyana fikira da ƙirƙira. Ƙoƙarinsa ya haskaka wa duniya irin baiwar da matasa ’yan Nijeriya suke da ita a idon duniya. Kamfanin Indomie, ya jima yana bayar da gudummawa da goyon baya a fannin ƙirƙira da ilimi a tsakanin matasa, kamfanin ya bayyana farincikinsa da...
Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun bayan da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka koma yakin kisan kare dangi a ranar 18 ga watan Maris ya kai 13,280, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 56,675. A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mutane 51 ne suka yi shahada wasu 180 kuma suka jikkata a zirin Gaza. A halin da ake ciki dai, wani adadi mai yaw ana wadanda abin ya shafa...
Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
Ɗalibi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin karya tarihin Kundin Tarihi na Duniya, na zane a fuska mafi yawa cikin mintuna uku. Ɗalibin ya samu tallafi daga kamfanin da ke yin taliyar yara Indomie, inda ya yi zane a fuskar mutum 17 cikin mintuna uku, wanda hakan ya ba shi damar zarce kambun Emilia Zakonnova, wanda ta kafa a watan Yulin 2025 na zane fuskar mutum 12. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Collins ya gwada sa’arsa a mataki uku: Na farko: ya zane fuskar mutum 17 cikin mintuna 2 da sakan 40 Na biyu: ya zane...
Fitaccen ɗan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmann ya kafa tarihin zama na farko a ƙungiyar da ya ci mata ƙwallaye 200. Griezmann ɗan asalin Faransa ya kafa wannan tarihin ne a ranar Talata yayin Gasar Zakarun Turai, inda Atletico ta lallasa Eintracht Frankfurt ta Jamus da ci 5-1. Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Babban malamin Qur’ani da ƙira’a na Masallacin Madinah ya rasu Kocin Atletico, Diego Simeone ya bayyana farin cikinsa kan ƙwazon ɗan wasan, inda yake cewa “ba ruwan hazaƙa da shekaru.” Griezmann mai shekaru 34, ya kwashe kusan shekaru 10 a Atletico kafin ya cim ma wannan mataki. A cewar Simeone, “ina godiya ga Antoine da lokacin da ya kwashe a Atletico Madrid. Ya...
Majiyoyin tsaro sun ce waɗannan hare-haren wani ɓangare ne na yunƙurin karya ƙarfin ’yan ta’adda da kuma katse hanyoyin samun kuɗaɗensu ta hanyar safarar miyagun ƙwayoyi, haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma sata man fetur. Sun kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomin tsaro domin kawo ƙarshen ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a faɗin ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A rana ta farko ta watan Oktoba, gwamnatin tarayya ta kasar Amurka ta sake tsayar da ayyukanta. Bisa binciken da CGTN ta gudanar na jin ra’ayoyi a duniya a kwanan baya tsakanin mutane 7,671 daga kasashe 38, an ce, masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna damuwa game da matsalar da aka samu a tsarin kasar Amurka sakamakon matsalar harkokin siyasa da sarrafa harkokin kasar, inda suka bayyana cewa, salon tsarin demokuradiyyar Amurka yana sabawa da ainihin tsarin demokuradiyya, kuma Amurka ba ta zama kasa mafi kyawun ba da jagoranci a wannan fanni ba. An sake tsayar da ayyukan gwamnatin kasar Amurka bayan shekaru 7, an samu irin hakan a baya yayin wa’adin shugaba Donald Trump karo na farko. Bisa binciken...
Fitaccen masanin karatu da ƙira’ar Al-Qur’ani kuma babban malamin nan da ke karantarwa a Masallacin Annabi da ke Madina, Sheikh Bashir bin Ahmed Siddiq, ya riga mu gidan gaskiya a yau Laraba. Shafin Al-Haramain ya ruwaito cewa Sheikh Bashir ya rasu ne bayan shafe kusan shekaru sittin yana koyar da Al-Qur’ani a Al-Masjid An-Nabawi da ke birnin Madinah. Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake tallafawa Ilimin mata Sheikh Bashir da aka haifa a shekarar 1358 Hijiriyya, wanda shi ne mafi shahara a cikin sahun bajiman malaman ƙira’a, ya rasu bayan shafe kusan shekaru 90 a doron ƙasa. Fitattu daga cikin malamansa akwai Qari Fath Muhammad Panipati, da Sheikh...

A yau sharhin namu zai yi muku Magana ne game amincewa da falasdinu a matsayin kasa da wasu kasashen turai suka yi a baya bayan nan ciki har da birtaniya da kasar Faransa, sai dai amincewa da kasar falasdinu ci gaba ne babba mai cike da tarihi amma haka
A yan kwanaki kin nan kasashen duniya sun fuskanci wani lamari mai jan hankali sosai, wanda ya jaddada hakkin falasdinu na kafa kasarsa mai cin gashin kai, hakika wannan lamari ya kai kololuwasa inda ya kai ga ranar litinin da ta gabata aka kira wani taro a gegen taron majalisar dinkin duniya karo na 80 domin bayyana nuna amincewa da warware rikicin falasdinu na kafa kasashen biyu masu cin gashin kansu, Akwai abubuwa guda buyi masu gayar muhimmancin da suka sanya aka gudanar da taron kafa daula biyu, na farko hakika yazo a yan kwanaki kadan sanar da shimfida taswirar hanya na kafa kasar falasdinu mai cin gashin kai bisa iyakoyin da aka cimma a wata yuni shekara ta 67...
Kyawawan sakamakon da aka samu a tsarin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar wanda a bana ake kammala karo na 14, sun nuna muhimmancin da ake bai wa rayuwar al’umma. A halin yanzu kasar Sin tana alfahari da tsarin kula da samar da ruwa mafi girma a duniya, inda ta mallaki manyan tafkunan adana ruwa fiye da 95,000, da manyan ayyuka 200 na janyo ruwa zuwa yankunan da ba su da shi domin aikin gona da inganta rayuwa a birane. Zuba jarin kasar a bangaren bincike da samarwa (R&D) ya karu da kashi 50%, wanda hakan ya haifar da samun nasarorin kimiyya masu yawa a cikin kasa har ma da duniya. Bangaren samar da ci gaba mara gurbata muhalli...
Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya ya jaddada ƙudirinsa na yin aiki tare da Gidauniyar Malala a ƙoƙarinta na ci gaba da bunƙasa ilimi da magance ƙalubalen da ke hana miliyoyin yara, musamman ’yan mata rashin zuwa makaranta. Da yake yi wa Malala Yousafzai maraba a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya, Babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai a ofishin Mohammed Malick Fall, ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya zata yi aiki tare da gidauniyar Malala, wacce ta samu kyautar lambar yabo ta Nobel. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi mat An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja “Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada goyon bayanta ga asusun Malala wajen ganin ‘ya’ya mata da yawa suna samun...
Yau Najeriya ke cika shekaru 65 da samun ƴancin kai daga Turawan mulkin mallaka, inda aka saba gudanar da bukukuwa da kuma nazari dangane da ci gaban da ƙasar ta samu a ƙarƙashin mulkin ƴan ƙasa da kuma ƙalubalen da take fuskanta. Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar ƙasar ke rayuwa a cikin mawuyacin hali, sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki da tsadar rayuwa waɗanda suka biyo bayan sauye-sauyen da gwamnatocin da suka gabata da kuma mai ci suka ƙaddamar da zummar sake fasalin tafiyar da ƙasar. A irin wannan rana a shekarar 1960, aka rantsar da Dr. Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban ƙasa, tare da Sir Abubakar Tafawa Balewa a matsayin Firaminista, shugabannin da suka yanke...
A cewar Wike, ana sa ran kamfanin CCECC zai kammala aikin gabanin kaddamar da fara amfani da titin nan da watan Yunin shekarar 2026. Tsarin aikin ya kunshi komai da komai, ba kawai shimfida titin ba har ma da gada mai ginshikai guda hudu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Kwamitin Shura na Jihar Kano, ya ta dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga y’in wa’azi har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zarginsa da yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). Sakataren kwamitin, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a yau Laraba. PENGASSAN ta dakatar da yajin aiki, ta gargaɗi matatar Dangote Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare “Yau mun sake yin zama domin karɓa da kuma nazarin zarge-zargen da ake yi wa Sheikh Lawal Shuaib Abubakar, wanda aka fi sani da Triumph. Mun saurari sauti da kuma kallon bidiyon da aka turo. “A cikin tattaunawarmu, mun yi bincike mai zurfi. Mun yanke cewa...
Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas (PENGASSAN), ta dakatar da yajin aikin kwanaki uku da ta fara biyo bayan rikici tsakaninta da matatar Dangote. Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba. Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 26 a Kogi Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Ƙungiyar ta kuma gargaɗi matatar Dangote da kada ta kaeya yarjejeniyar da aka cimma a ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro. Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, wanda ya sanar da janye yajin aikin, ya ce idan matatar ta karya yarjejeniyar, ƙungiyar ba za ta yi shiru ba. Rikicin ya samo asali ne bayan...
“Ina kira ga kowane ɗan Nijeriya da ya rungumi zaman lafiya, kwanciyar hankali, da haɗin kai a gidajenmu, al’ummominmu, da fadin ƙasarmu. Tare, cikin haɗin kai da ƙauna, za mu iya gina Nijeriya ta mafarkinmu. Barka da ranar ‘Yancin Kai!” in ni Shettima. Akan hakan, Shettima ya jinjinawa ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wanda ya samar da abubuwan ci gaban ƙasa, inda ya ƙara da cewa, idan aka ƙara haƙuri abubuwa za su yi kyau a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa ba za su bar irin waɗannan matakai su ɗauke hankalinsu daga manufar tabbatar da zaman lafiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana alhininta game da rasuwar aƙalla mutum 26 waɗanda hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su. Mutanen sun fito ne daga Ƙaramar Hukumar Ibaji, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Ilushi a Jihar Edo. Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Kingsley Fanwo ne, ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba. Ya ce wannan lamari babban rashi ne, kuma gwamnatin jihar na miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Ibaji gaba ɗaya. Gwamna Ahmed Usman Ododo, ya aike ta’aziyyarsa, inda ya ce gwamnatin jihar na tare da al’ummar Ibaji a wannan lokaci...
Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare da kuma takaita zirga-zirgar makiyaya tsakanin kananan hukumomi daga ranar Laraba, daya ga watan Oktoban 2025. Shugaban kwamitin sasanta rikicin manoma da makiyaya na jihar, wanda kuma shi ne kwamishinan Ma’aikatar Noma da Kiwo ta jihar, Dakta Barnabas Malle, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar. Gwamna Abba ya bukaci Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sandan Kano Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sanarwar ta ce matakin na cikin tsare-tsaren tabbatar da zaman lafiya a lokacin kakar bana, wanda manoma ke girbe amfanin gonarsu. Daga cikin ƙa’idojin da aka kafa akwai hana kiwo daga ƙarfe 6 na yamma zuwa ƙarfe...
‘Yan ƙasashen ƙetare da suka karya dokar shige da fice ta Nijeriya za su fuskanci hukunci, wanda zai iya haɗawa da tara, kora, ko kuma yiwuwar hana sake shigowa Nijeriya nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa aiwatar da yarjeniya ta musamman da kasar china a halin da ake ciki a yankin da kuma yadda duniya take sauyawa da sauri ya zama wajibi ga kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin da yake gabatar da sakon murna ga gwamnatin kasar China kan cika shekaru 76 da kafuwar kasar. Wanda kuma itace ranar kasa a kasar ta China. Pezeshkiyan ya kara da cewa wannan ranar ta samuwar kasar China, rana ce da hadin kai da ci gaba da kuma godewa ga irin ci gaban da kasar ta samu daga lokacin zuwa yanzu a cikin gida da kuma fagen kasa da...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya cire Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, saboda yadda ya siyasantar da aikinsa. Kiran na zuwa ne bayan kwamishinan tare da ilahirin dakarun rundunar a jihar sun kaurace wa halartar bikin tunawa da ranar samun ’yancin kai da aka gudanar a jihar. A bisa al’ada dai Gwamna kan jagoranci hukumomin tsaro wajen gudanar da faretin bikin ranar a duk ranar daya ga watan Oktoba. To sai dai a bana, ba a ga Kwamishinan ’Yan Sandan na Kano ba, sannan babu ko dan sanda daya a wajen bikin. Bayan wuya sai daɗi: Sakon Tinubu ga ’yan Najeriya Sojoji sun kama ’yan sandan bogi da motoci...
A shekarar da ta gabata, Nijeriya ta ƙuduri aniyar samar da gangar ɗanyen mai 445,000 a kowace rana ga matatar a cikin kuɗin gida (Naira). Jami’an gwamnati sun yi nuni da cewa, shirin, idan ya yi nasara, za a iya fadada shi zuwa sauran matatun mai na masu zaman kansu da ke cikin kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp