2025-10-13@20:22:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1984

«kungiyar ta NUJ»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas (PENGASSAN), ta dakatar da yajin aikin kwanaki uku da ta fara biyo bayan rikici tsakaninta da matatar Dangote. Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a ranar Laraba. Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 26 a Kogi Jihar Gombe ta fara aiwatar da dokar hana kiwo da daddare Ƙungiyar ta kuma gargaɗi matatar Dangote da kada ta kaeya yarjejeniyar da aka cimma a ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro. Shugaban PENGASSAN, Festus Osifo, wanda ya sanar da janye yajin aikin, ya ce idan matatar ta karya yarjejeniyar, ƙungiyar ba za ta yi shiru ba. Rikicin ya samo asali ne bayan...
    An kuma amince da cewa ma’aikatan da aka kora za a mayar da su kan ayyukan su cikin wasu kamfanoni na rukunin Dangote ba tare da sun yi asarar albashi ba, kuma babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa saboda rawar da ya taka a wannan taƙaddamar.     An cimma matsayar ne a gaban manyan jami’an gwamnati da suka hada da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ministan kudi kuma mai kula da tattalin arziki, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, karamin ministan albarkatun man fetur (Gas) da shugabannin NMDPRA da NUPRC, da wakilan kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).   Haka kuma shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) sun halarci tattaunawar tare da shugabannin kungiyar ta...
    Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a wata tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan ƙwadago na Nijeriya, Mohammed Dingyadi a ranar Litinin.   Wannan yajin aiki na PENGASSAN ya shafi rufe ɓangarori da dama na harkar mai a Nijeriya, ciki kuwa har da babban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, tare da dakatar da ba matatar Ɗangote ɗanyen mai.   Kungiyar ta PENGASSAN ta ja daga, inda ta bayyana cewa, “Muna kan bakar mu har yanzu, saboda mutanen mu da aka kora daga aiki, muna so dole a mayar da su.”   Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotun Abuja ta bayar da umarnin hana yajin aikin ƙungiyar ta PENGASSAN da ɗaukar matakin hana kai wa matatar Ɗangote ɗanyen...
    Wata kotu a Jihar Florida da ke ƙasar Amurka ta aike da wani mutum Craig Vogt mai shekaru 61 gidan waƙafi, bayan samunsa da laifin yanka tsuntsayen Dawisu guda biyu, sannan ya yi dabge da naman su. Hukumomin Hudson, wani yanki da ke Florida, sun cafke mutumin ne bayan an samu rahoton abin da ya aikata, wanda ya ta da hankalin maƙwabta da ya shaida musu cewa ya yanka tsuntsayen kuma ya soya har ya ɗebi dabgen. An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin ya amince da laifinsa, yana mai cewa ya aikata hakan ne saboda ɓacin ran...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinjina wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira “juriya, haƙuri da ƙarfin halin da suke nunawa duk da matsin tattalin arziki da matsalolin tsaro” da ƙasar ke fuskanta.  A cikin saƙonsa na taya ’yan Nijeriya murnar zagayowar ranar samun ’yancin kai da ƙasar ta yi shekaru 65 da suka gabata, madugun adawar ya yi zargin cewa, gwamnatin jam’iyyar APC mai mulki ta yi watsi da halin ƙaƙanikayi da ’yan ƙasar suka tsinci kansu a halin yanzu. A gaggauta binciko makasan ’yar jaridar Arise TV —Tinubu ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe Wazirin Adamawan ya bayyana damuwa kan yadda ’yan Najeriya ke rayuwa cikin ƙangin talauci, da yunwa, da rashin...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa  Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV. A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida. ’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata. Tinubu...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali, da kuma cike da zaman lafiya, da abota, da zaman tare, da tattaunawa, kuma za ta iya sanya tausayi ya mamaye harshen bai daya ta hanyar yin amfani da arzikin al’adu. A cikin sakon da ya gabatar a wurin taron karrama mawakan Iran Shams Tabrizi da Mawlana Jalaluddin Mohammad Balkhi, shugaba Pezeshkian ya ce a ranar Talata: An ambaci ranakun 29 da 30 ga watan...
    Ambaliyar ruwa a Sudan na barazana ga rayuwar dubban mutane tare da kara munana matsalolin jin kai Kogin Nilu ya mamaye yankuna da dama a Sudan, lamarin da ke barazana ga rayuwar dubban mutane. Ambaliyar ruwa ta lalata gonaki da kadarori a jihar Al-Jazirah da kewaye, lamarin da ya shafi dubban iyalai tare da barin su cikin bukatar tallafin gaggawa da matsuguni da abinci da magunguna. Haka zalika ruwan sama kamar da bakin kwarya ya dakatar da zirga-zirgar wasu jama’a a wasu yankuna, yayin hukumomin cikin gida suke kokarin rage barnar da ake amma lamarin ya foi karfinsu sakamakon karancin kayan aiki. Ambaliyar ruwan ta kara ta’azzara matsalar jin kai a birnin El Fasher da sauran garuruwa, inda mazauna garin...
    Tsohon Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Neja (SUBEB), Alhaji Alhassan Bawa Niworo, ya shiga hannun ’yan bindiga. An yi garkuwa da shi tare da wasu fasinjoji da dama a yammacin Litinin, 29 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 4 na yamma, tsakanin ƙauyukan Felegi da Ibi a kan hanyar Mokwa zuwa New Bussa a Ƙaramar Hukumar Borgu. Wata majiya ta ce Niworo tare da wasu ciki har da wani lauya, Barista Ahmad, na kan hanyarsu zuwa Minna ne lokacin da ’yan bindigar suka tare hanyar, suka kuma yi awon gaba da su cikin daji. Wasu daga cikin waɗanda aka sace ’yan kasuwa ne da suka fito daga kasuwar mako ta New Bussa. Abin da ya faru a zaman...
    Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar da matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi. Kwamitin ya bayyana cewa ƙasar ta karya doka ne ta hanyar amfani da ɗan wasa da bai cancanci buga wasan ba, a fafatawar da suka yi da Lesotho, inda Teboho Mokoena ya taka leda a ranar 21 ga Maris, 2025. FIFA ta ce amfani da ɗanwasan ya saɓa da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saɓa da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta ƙwace...
    Sudan ta fitar da gargaɗin gaggawar samun ambaliyar ruwa a jihohi biyar bayan matakin ruwa a Kogin Nilu ya ƙaru kamar yadda rahoton gidan jaridar gwamnati Suna ya ruwaito. Rahotanni sun danganta ƙaruwar matakin ruwa da babban dam ɗin Ethiopia da aka buɗe a wannan watan. Ma’aikatar nomar rani ta Sudan ta sanar da gargadin ne a ranar 28 ga watan Agusta, inda ta ce ya shafi jihohin Khartoum da River Nile da White Nile da Sennar da kuma Blue Nile. Ma’aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwa na iya mamaye gidaje da gonaki, tare da kira ga ɗaukar matakan gaggawa. Farfesa Abbas Sharaky na jami’ar Cairo, masani a fannin ƙasa da albarkatun ruwa, ya bayyana cewa ƙaruwar matakin ruwa a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ɗangote, PENGASSAN Ba Su Yi Ba Don Magance Rikicinsu DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
    Shugabannin ƙungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da wakilan Matatar Dangote na halartar wani taron gaggawa tare da wakilan Gwamnatin Tarayya. Shugaban ƙungiyar PENGASSAN, Festus Osifo, tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (TUC), Nuhu Toro, ne ke jagorantar ɓangaren ƙungiyoyin ƙwadago, yayin da Ministan Ƙwadago da Ayyuka, Maigari Dingyadi da wasu jami’ai ke wakiltar Gwamnatin Tarayya. Ya zama tilas ɗalibai su gabatar da ‘Project’ kafin rajistar NYSC — Tinubu Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutu ranar Laraba Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamnatin Tarayya ta gayyaci shugabannin PENGASSAN da na ɓangaren Matatar Dangote zuwa wannan taro sakamakon rikicin da ke tsakanin ɓangarorin biyu. Sai dai, duk da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wata hira da gidan talabijin din Aljazeera yayi da sakataren cibiyar kula da yan gudun hijira a kasar Nowy ya fadi cewa babban abin da yake damunsu shi ne inda duniya ta yi shiru kan abubuwan da ke faruwa a Gaza inda israa’ila ke kisan kiyashi. Dubban daruruwan alummar Gaza ne suka tarwatse  da suke fuskantar tsananin bala’I kamar jan Egeland yadda ya bayyana, yace dole ne a a dakatar da kisan kiyashin da isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza, Haka zalika ya nuna damuwar sosai game da gum da baki da majalisar dinkin duniya ta yi akan batun gaza, babban abin da muwar shi ne yadda duniya take nuna halin ko in kula da abin da...
    Masana’antar raya al’adu ta kasar Sin, ta samu ci gaba bisa daidaito yayin shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, wanda aka gudanar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. A cewar mataimakin ministan ma’aikatar raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sin Lu Yingchuan, a shekarar 2024, darajar jimillar kadarorin sashen ta kai yuan tiriliyan 34.4, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.84. Lu wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai, ya ce tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, Sin ta kuma cimma manyan nasarori a fannin bunkasa tasirin al’adunta. Ya ce a shekarar ta 2024, jimillar adadin cinikayya a fannin al’adu na Sin ya kai yuan tiriliyan 1.4, inda karin abubuwan sayayya a fannin da...
      Idan dai ba a manta ba, gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin babban sakataren ma’aikatar, Abel Enitan, domin duba buƙatar ƙungiyar ASUU, a wani yunƙuri na tabbatar da ci gaban jami’o’in.   Sai dai har yanzu kwamitin bai fitar da wata sanarwa ko sakamakonsa ga jama’a ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi. “Mun ɗauki...
    Yanzu haka dai akwai jami’o’i da kwalejoji da cibiyoyi da dama da ake koyar da harshen mandarin a kasashen Afirka. Yayin da dalibai masu koyon harshen Mandarin suke ta karuwa a kullum. Misali a kasar Uganda akwai cibiyar koyar da harshen Mandarin wadda ta fara da dalibai 30 a shekara goma da ta gabata, amma a yau tana da sama da dalibai 400. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya, wato PENGASSAN, ta fara yajin aiki a faɗin Nijeriya daga daren Litinin, 29 ga Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan umarnin da shugabancin ƙungiyar ya bayar tun ranar Lahadi, inda aka umurci mambobi da su tsaida aiki a dukkan kamfanoni da cibiyoyi da hukumomin da suke aiki a su. A sakamakon haka, an kulle ƙofar shiga shalƙwatar hukumar NUPRC da ke Abuja, inda ɗaruruwan ma’aikata suka taru a waje ba tare da an bari sun shiga ba. Wannan mataki ya haddasa tsaiko a gudanar da ayyuka, musamman a sashen kula da harkokin mai da iskar gas na ƙasar. Rikicin Dangote Da PENGASSAN Ba Zai Kawo Wahalar Fetur Ba Majalisa Ta...
    Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na hanya. Mako guda bayan nan kuma wani ɓangaren ya rushe a Sabon Gari. Shekara guda da wata ɗaya bayan faruwar lamarin, wanda ya mayar wuraren da suka rushe sun koma tarkon mutuwa da ke haddasa haɗurra da suka kashe mutane da raunata wasu da dama. Wakilinmu da ya kai ziyara ya samu wani kamfanin gine-gine ya dawo Malori da kayan aikinsa. Mazauna sun tabbatar da...
    Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce adadin zirga-zirgar fasinjoji yayin hutun bikin tsakiyar kaka na Sin dake tafe nan da ‘yan kwanaki, zai kai kimanin biliyan 2.36. Da yake karin haske kan hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lahadin nan, mataimakin ministan ma’aikatar Li Yang, ya ce yayin kwanaki takwas na hutun da za a fara tun daga ranar Laraba, za a samu karuwar tafiye-tafiye na yawon bude ido ko na ziyartar ‘yan uwa. Li, ya kara da cewa, an yi kiyasin ganin tafiye-tafiye kimanin miliyan 295 a duk rana cikin kwanakin hutun masu zuwa, karuwar da ta kai kaso 3.2 bisa dari kan na shekarar 2024 da ta shude. An kuma yi hasashen kaso...
    Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti na 14 da fara wasan ne Kun Khalifa suka fara zura ƙwallo a ragar Barau FC. Sai dai minti biyu kacal bayan haka, Yahaya Ibrahim ya farke wa Barau FC kwallo, wanda ya buɗe musu ƙofar dawowa cikin wasan. Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Ba za a yarda da ƙoƙarin maido da kudurori da suka ƙare ba kan Iran Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta tabbatar da cewa: Yunkurin da kungiyar Tarayyar Turai Troika da Amurka ke yi na maido da kudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran, ba abu ne da za a amince da su ba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da sanarwar mayar da martani ga ikirarin da kasashen Turai uku da Amurka suka yi na maido da kudurorin kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da suka kare kan Iran. Ma’aikatar ta yi la’akari da yin amfani da hanyar warware takaddama da aka tanada a cikin yarjejeniyar hadin gwiwa game da...
    Ƙungiyar Ma’aikata Masu Aikin Mai da Gas ta Najeriya (PENGASSAN), ta fara yajin aiki saboda korar wasu ma’aikata a Matatar Mai ta Dangote da ke Jihar Legas. Sakataren ƙungiyar, Lumumba Okugbawa, ya ce sun fara yajin aikin ne daga ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa ‘Yan fashi sun sace mutum 17 a mahadar tekun Akwa Ibom da Kuros Riba Da misalin ƙarfe 6 na safe, mambobin ƙungiyar da ke aiki a ɗakunan kula da na’urori suka daina aiki. Umarnin ya shafi mambobin da ke ofisoshi, kamfanoni, da hukumomin gwamnati a faɗin Najeriya, waɗanda za su daina aiki da misalin ƙarfe 12:01 na daren ranar Litinin, 29 ga watan Satumba. Okugbawa,...
    An kori Lage daga Benfica duk da wasa daya ya yi rashin nasara a dukkan karawa a kakar nan, kuma Mourinho ya gaji kungiyar da take ta shida a teburin Primeira Liga da tazarar maki biyar tsakani da Porto mai jan ragama. Ya fara da wasa ranar Asabar, inda suka ziyarci ABS, wadda take ta 17 a kasan teburin a babbar gasar kasar Portugal. Mourinho, dan kasar Portugal wanda ya bai wa kansa sunan ”the special one’ a 2004 zai ziyarci tsohuwar kungiyarsa wadda ya koyar sau biyu a tarihi wato Chelsea a Champions League da Benfica za ta buga ranar 30 ga watan Satumba. Jerin kungiyoyin da Mourinho ya koyar Porto (2002-04) Primeira Liga biyu, Champions League, Uefa Cup...
    Yayin da yake bayani kan muhimmancin wannan shiri, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaki, ya ce: “Wannan Cibiyar wata gagarumar alama ce ta kudurin Gwamnatin Jihar Kaduna na bunkasa koyon sana’o’i, karfafa matasa, da haɓaka tattalin arziki.   Yace An zaɓi fannonin sana’o’i 14 ne cikin hikima domin su magance manyan bukatun ƙwararrun ma’aikata a bangarorin gine-gine, makamashi, fasahar zamani (ICT), kula da baƙi, da harkokin ƙirƙira. Muna da yakinin cewa waɗanda suka kammala karatu a wannan Cibiyar ba kawai za su samu ayyukan yi ba ne, har ma za su zama masu dogaro da kai kuma su samar da dama ga wasu.”   Shima Shugaban Cibiyar, Malam Husaini Haruna Muhammad, ya jaddada muhimmancin da horon ke...
    Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...
    Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta Najeriya, reshen Jihar Zamfara, ta ce sun shiga yajin aiki na kwanaki shida a matsayin gargaɗi. Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tunatar da gwamnati batun sabon tsarin albashi na ma’aikatan lafiya. AGILE ta raba kayan karatu da sana’o’i a cibiyoyi 54 a Gombe HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Ya ce duk da cewa gwamnati ta amince da tsarin CONHESS na ma’aikatan lafiya, amma har yanzu ta kasa aiwatar da tsarin CONMESS na likitoci. A baya, ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai a ranar 11 ga watan Satumba, amma ta dakatar bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Rafael Grossi babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA a wata hira da yayi da gidan talbijin din Russia 24 ya bayyana cewa shirin nukiliya iran na zaman lafiya ne baki daya. Wannan maganar ta yi karo da kalaman prime minister isra’ila Benjamin Natanyaho  inda ya nuna cewa shirin nukiliyar Iran babban barazana ne,  don haka kalaman na shugaban IAEA sun tabbatar da ikirarin da iran ta dade tana yi na cewa shirin na zaman lafiya ne. Grossi ya fadi cewa ya amince hare-haren soji sa israila ta kai sun auna cibiyoyin nukiliyarta ta Fordo Natanza da kuma Isfahan inda ake ci gaba da inganta sinadarin yunariyum. Ya tabbatar da cewa iran ta tace yuraniyom kashi 60% ...
    Tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka bisa jagorancin Adam Smith ta kammala ziyara a kasar Sin a jiya Alhamis 25 ga wannan wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan batun. Kafin ziyarar tawagar, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho, da yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan da suke sa lura tare, kana sun tsara taswira kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kama a mataki na gaba. Bisa wannan yanayi, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka ta shaida muhimmiyar rawar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da ci gaba da karfafa mu’amalar dake tsakanin...
    Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra. An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka Extension a garin Akure, ya ruwaito cewa ’yarsa Jesinta, ta ɓace ne a lokacin da take tare da mahaifiyarta Sunday Happiness. Gwamnatin Kebbi ta sake jaddada goyon bayanta ga hukumomin tsaro Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka sanarwa manema labarai a Akure ranar...
    Kasashen Iran da Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dala biliyan 25 don gina tashoshin makamashin nukiliya guda hudu a wani bangare na yarjejeniyar hadin gwiwa ta dogon lokaci da nufin karfafa alaka tsakanin Tehran da Moscow a fannoni daban-daban. An rattaba hannu kan yarjejeniyar zartarwa a birnin Moscow yau Juma’a tsakanin Kamfanin Hormoz na Iran da kamfanin Rosatom Project na kasar Rasha don ginawa da kuma kafa cibiyoyin samar da makamashin nukiliya na zamani hudu a garin Sirik da ke gabar teku a lardin Hormozgan na kudancin kasar. Babban aikin da za a gudanar a gundumar Kuhestak na yankin Sirik na lardin Hormozgan, zai iya samar da megawatts 5,020 daga makamashin nukiliya. An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne...
    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci birnin Ibadan, a yau Juma’a domin halartar bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan, Oba Rashid Adewolu Ladoja na 44 da ake kan gudanarwa yanzu haka. Shugaba Tinubu da tawagarsa sun sauka a filin jiragen sama na Ladoke Akintola da ke Ibadan ne da misalin ƙarfe 1:30 PM na rana inda Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi masa maraba. Yadda ’yan haya za su samu ragin N500,000 a shekara  Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso Aminiya ta ruwaito cewa, tun kafin isowar Shugaba Tinubu aka fara gudanar da bukukuwan al’adun gargajiya da suka danganci miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan Oba Rashid Adewolu Ladoja. Juma’a a...
    Sojojin Yemen sun kaddamar da mummunan farmaki kan yankin Jaffa da makami mai linzami Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Alhamis cewa; Sun kai hari da makami mai linzami kan yankin Jaffa da aka mamaye. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Yemen ta fitar ta tabbatar da cewa: Rundunar sojinta ta kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2 mai dauke da kawuna da dama, inda harin ya yi mummunan barna a yankin Jaffa da aka mamaye. Sanarwar ta kara da cewa, wannan farmakin ya samu nasarar cimma manufofinsa, kuma ya sa miliyoyin garken yahudawan sahayoniyya sun tsere zuwa matsugunin karkashin kasa tare da dakatar da zirga-zirga a filin jirgin...
    Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya yi wani kakkausan gargadi game da halin da ake ciki na jin kai a Gaza, a daidai lokacin da Isra’ila ke yakin kisan kare dangi a can. A ranar Alhamis din nan, Lazzarini ya shaida wa manema labarai a wani taron manema labarai a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York cewa, har yanzu yanayi a Gaza ba zai iya jurewa ba, yana mai bayyana halin da ake ciki a matsayin jahannama ta dukkan bangarorinta. “Ina ganin yana da mahimmanci ko da yaushe, kowace rana, mu tunatar da kanmu game da abin da ke faruwa a can, don kawai mu tabbatar da cewa ba mu fara...
    Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama, amma daga bisani aka sake shi bayan wasu dattawan unguwar sun sa baki. Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Budurwar da abin ya faru da ita da ke koyon sana’a a wajen mutumin da ake zargi, ta ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8 na daren ranar Lahadi yayin da ake ruwan sama. A cewarta:...
    Daga nan sai ya jaddada aniyar Sin, ta ci gaba da goyon bayan matsayi da ikon MDD, tare da mara baya ga sassan kasa da kasa wajen cimma nasarar amfani da dandalin MDDr a matsayin fagen karfafa shawarwari da hadin gwiwa, da tsare-tsare da aiwatar da matakai yadda ya kamata.   Haka kuma, a yayin zantawarsa da shugabar taron MDD karo 80 Annalena Baerbock, a gefen babban taron muhawarar majalissar dake gudana a halin yanzu, firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce Sin na goyon bayan gina MDD mai karin inganci da hangen nesa, ta hanyar gudanar da sauye-sauyen kyautata karko da nagartar ayyukanta. Ya kuma bayyana kakkarfan goyon bayan Sin ga ikon MDD, da rawar da take takawa a...
    Bugu da kari, mahalarta bikin sun bayyana cewa, bikin ya nuna maimaituwar tarihin MDD na shekaru 80 da suka gabata, tare da yin kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, domin karfafa aniyar al’ummomin kasashen duniya ta kare zaman lafiya, da inganta fahimtar juna.   Haka kuma, Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG, ya shirya wani bikin kade-kaden fina-finai masu alaka da zaman lafiya, mai taken “Hadin kai a duniya, Muryar zaman lafiya”, a cibiyar fasaha ta Lincoln da ke birnin New York na kasar Amurka a daren ranar Talata.   Mataimakin sakantaren MDD mai kula da harkokin watsa labarai, Melissa Fleming, ta taya murnar bude bikin ta kafar bidiyo. Haka kuma, shugaban...
    An gurfanar da wasu malamai biyu na wata makaranta ta Zariya Children School da ke yankin GRA Zariya, a gaban kotun majistare da ke Tudun Wada bisa zargin lalata wata ɗalibar makarantar mai shekaru 11. Jami’in da ke gabatar da ƙara a gaban kotun, ASC Mustapha Abdulkadir, ya ce malamai biyu tare da wasu uku da suka tsere, na fuskantar tuhuma kan laifin aikata lalata, wanda ya saba wa sashi na 259 na kundin laifukan Jihar Kaduna na shekarar 2017. An ceto mutum 5 bayan gini ya rufta da su a Legas Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata da malaman makaranta na bogi 3,488 Ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Satumba wani mai suna Yahaya Aliyu, mazaunin Tudun Jukun...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Leken Asiri ta Iran ta fitar da wasu bayanai na sirri da suke da alaka da ayyukan cibiyar makaman Nukiliyar HKI. Bayanan da ma’aikatar leken asirin ta Iran ta fitar wadanda aka watsa a kafafen watsa labarun kasar, sun kuma kunshi ayyukan da wasu masana a fagen Nukiliya na turai suke gudanarwa.  Majiyar tsaron ta Iran ta kuma ce bayanan da ta samu suna kunshe a cikin miliyoyin shafukan takardu, sun kuma same su ne ta hanyar wasu cibiyoyi na ‘yan sahayoniya da kuma cibiyarta ta Nukiliya.”  Ministan hukumar leken asirin ta Iran ya ce, an shigo da miliyoyin takardun masu kunshe da wadannan bayanan zuwa cikin Iran, suna kuma kunshe da bayanai masu kima. Share 0 0 votes...
    Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sanya la’adar Dala 10,000, kwatankwacin Naira miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran. Ana dai neman Olumide ne a Amurka ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan zamba da dama. ’Yan bindiga sun harbi wani saboda rashin isassun kuɗi a asusunsa Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki A cewar sanarwa da aka wallafa a shafin FBI a ranar Laraba, ana tuhumar shi da laifukan zamba a banki, zamba da takardun shaida, laifukan da ake zargin ya aikata a jihar Illinois tun shekarar 2001. Adediran, mai shekaru 56, yana amfani da sunaye...
    Rahotanni sn bayyana cewa shugaban kasar Iran Masud pezeshkyan  ya gana da shugaban  kungiyAr tarayyar turai Antonio costa a gefen taron majalisar dinkin duniya a birnin newyork,Kuma ya fadi cewa wadanda suka fice a tattaunawar JCPOA su suka haddasa aka fada a halin da ake ciki yanzu. Har ila yau ya kara da cewa Iran  bata da niyyar mallakar makamin nukiliya kuma ba za ta taba nemansa  ba, don haka Tehran a shirye take ta yi hadaka domin fayyace gaskiya da kuma karyata zarge-zarge marasa tushe balle madafa da ake yi mata kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya. Yace nauyi ya rataya ne a wuyan wanda suka fice daga yarjejeniyar JCPOA , wato shugaban Amurka ke nan da ya...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake fitar da Naira biliyan 5 domin biyan bashin ’yan fansho da haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritaya, lamarin da ya kawo adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta biya zuwa yanzu ya kai Naira biliyan 27 tun bayan hawansa mulki. A wannan karon, kimanin tsofaffin ma’aikata 1,026 ne suka samu haƙƙoƙinsu waɗanda aka tsayar da biya tun a shekarar 2017. Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar rashin adalci — Atiku Darajar Naira ta ƙaru bayan CBN ya rage kuɗin ruwa Aminiya ta ruwaito cewa, wannan wani yunƙuri na gwamnatin domin rage bashin Naira biliyan 48 na tsofaffin ma’aikata a matsayin haƙƙoƙin fansho da giratuti. Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da...
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran, amma shigarsu ta dogara ne da manufofin siyasar Iran. Ya ce: “Damar da suke da shi tana da kunci sosai, don haka tawagar hukumar IAEA tana da ‘yan sa’o’i kadan ko ‘yan kwanaki don sanin ko yarjejeniya da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai za...
      Gavi dai ba zai dawo ba sai a farkon shekarar 2026, shekarar da ake ganin kasar Sifaniya za ta kasance cikin kasashen da suka fi damar lashe gasar cin kofin duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da kuma Canada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
      Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar.   Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana samu a jere.   Tuni, dama masana suka yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025.   Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Hassan Jibril wanda ke zaune a yankin Pata da ke fama da ambaliyar ruwa a duk shekara, ya ce a yanzu haka suna cikin fargaba, duk da cewa a ko wace shekara sun saba yin gudun hijira tun bayan afkuwar ambaliyar ruwa ta 2012 da ta mamaye wasu al’ummomi a wasu kananan hukumomin jihar.   Ƙananan hukumomin dake cikin fargaba sun haɗa da Kogi, Ajaokuta, Ofu, Ibaji, Adavi, Bassa da Omala. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) ta tabbatar da cewa ta samu takardun kotu da ke hana mambobinta sayar da tikiti ko duk wani yunƙuri da zai kawo tsaikon al’amura a Matatar Ɗangote. Shugaban NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja ranar Talata, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Gas (PENGASSAN). An ƙone al’aurar ’yar shekara 5 saboda fitsarin kwance a Bauchi CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Akporeha ya ce kungiyar tana mutunta doka, kuma za ta bari shari’a ta yi aikinta har sai an kammala duk wani sha’ani a kotu. “Kamar yadda kowa ya sani, Ɗangote ya kai mu kotu, kuma...
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
    Ana zargin wata matar aure, Rabi Nuhu da ke garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi, da cin zarafin wata yarinya ’yar shekara biyar ta hanyar ƙone mata al’aura, saboda zargin tana yawan yin fitsarin kwance. Wakilinmu ya gano cewa yarinyar marainiya ce wadda mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, inda take zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama a garin, Kabiru Abdulkadir, ya bayyana cewa sai bayan kwana biyar da ƙonewar ta faru ne al’amarin ya bayyana. “Don guje wa matsala, mahaifin yarinyar ya sayi wata...
    A yau Talata ne dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, ta bude wani zama na musamman a birnin Brussels domin tattauna zargin da ta yi wa kasar Rasha da keta hurumin sararin samaniyar kasar Istonia. Taron na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, yana a karkashin aiki da doka ta 4 ne na tsarin aikin kungiyar wacce ta yi kira da a rika yin tarukan gaggawa domin yin shawara a duk lokacin da wata memba ta fuskanci barazana. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Estonia ce dai ta bayyana cewa jiragen yakin Rasha, samfurin Meg-31 guda 3 su ka keta hurumin sararin samaniyarta a ranar juma’ar da ta gabata, sun kuma dauki tsawon mintuna 12 suna karakaina a samaniya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar...
      Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai.   Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu ƙwarewa kan harkar ciyar da ɗalibai.   Taron ya mayar da hankali ne wajen duba nasarorin da aka samu cikin watanni goma tun lokacin da aka fara shirin a Ladduga, Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, da kuma Maigatari a Jihar Jigawa.   Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana cewa shirin ya shafi makarantun makiyaya kawai a jihohin Jigawa da Kaduna.   Ya...
    A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko. Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita. Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a...
    A jiya Lahadi ne dai jirgin ruwan agaji da aka bai wa sunan; ” Umar Mukhtar” ya bar ruwan kasar Libya  domin nufar Gaza da zummar karya killace yankin da aka yi na tsawon shekaru 18. Masu kula da jirgin ruwan na “Umar Mukhtar” sun bayyana cewa; Sun yi tanadin kayan aikin liktanci da aka bai wa sunan; Likitan Falasdinawa Husam Abu Saafiyyah. Har ila yau, hukumar agajin kasar Libya ta tanadi jirgin sama mai saukar angulu domin kai daukin gaggawa idan bukatar hakan ta taso. Da akwai mutane 20 a cikin wannan jirgin ruwan da su ka likitoci, masu fafutuka da kuma lauyoyi daga Libya da wasu kasashen turai. Jirgin ruwan na Agaji yana da cikakken goyon bayan al’ummar...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da nufin wargaza hadin kan Larabawa da na Musulmi Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila suna neman tada fitina da sanya kiyayya a tsakanin al’ummomin Larabawa da na Musulmi. Ya yi nuni da cewa wadannan ‘yan kore ba su da wani aiki na gaske da zai yi hidima ga kasashensu na asali, sai dai mayar da hankali kan kokarinsu wajen wargaza zamantakewar al’umma, karkashin kulawar Amurka da tallafin Larabawa da kuma jagorancin yahudawan sahayoniyya. A cikin jawabin da ya gabatar a jiya Lahadi, a daidai lokacin da ake gudanar...
    Ƙaramar Hukumar Sabuwa da ta Ɗandume a Jihar Katsina sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen da suka daɗe suna addabar yankin. An gudanar da taron sulhun ne a ranar Asabar a ƙauyen Kabalawa Dungun Mua’zu, da ke iyaka da ƙananan hukumomin biyu, amma yana ƙarƙashin Sabuwa. Da wannan ci-gaban, adadin ƙananan hukumomi da suka ƙulla yarjejeniyar sulhu da ’yan bindiga a jihar ya kai tara. Sauran sun haɗa da Batsari da Kankara, Kurfi da Musawa da Ɗanmusa da Jibia da kuma Faskari. Yadda aka kashe jami’an tsaro 53 cikin mako biyu NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu Shugaban Ƙaramar...
    Wannan yana faruwa sosai gaskiya, kuma ƙarshe ba a wayewa da lafiya gaskiya. Masu yi gaskiya tun wuri su daina wallahi, dan aure ya sha mutuwa ta sanadin haka ƙarshe azo ana nadama mara amfani. Sosai ana samun gagarumar matsala tsakanin ma’aurata zargi ya shiga tsakani, daga nan ma dai wani aure ka ji ya mutu. Su yi wa kansu faɗa, su daina gaskiya.   Sunana Haj. Maryama Ahmad, daga Jihar Kaduna: Wannan matsaloli suna faruwa sosai, kuma rashin tunani ne yake janyo hakan. Dalili kuwa ko da namiji ba shi da wannan tunanin na soyayya da wata to, kin ƙirƙirar masa ke da kanka, kin riga da kin nemo masa hanyar da zai riƙa samun damar bibiyar wasu. Haka...
    A daren ranar 19 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho, inda shugaba Xi ya jaddada cewa, alakar Sin da Amurka na da matukar muhimmanci, Sin da Amurka na iya cimma nasarar bai daya da wadata tare, ta yadda za su amfani kawunansu, da ma sauran sassan duniya baki daya. A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi, alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa, aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a. ’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Gwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba. “Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa...
    A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa. Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna. Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan. Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka...
    Rahotanni daga Islamabad sun nuna cewa gwamnatin kasar tana kwatanta yarjejeniyar tsaro da ta kulla da kasar Saudiya ,da irin wadda ke tsakanin dakarun tsaron kasashen turai da kuma kungiyar tsaro ta nato. Kasashen saudiya da Pakistan sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro tsakaninsu a wata ganawa da aka yi tsakanin prime minisata shehabaz sharif na Pakistan da takwaransa na kasar Saudiya Mohammad bn Salman a birnin Riyadh a ranar laraba da ta gabata inda suka kirata da yarjejeniya kan dabarun kasa, Musadik ya fadi cewa yarjejeniyar bata barazana ga kowa, kuma bata gayyaci wani ya kai wa kowa hari ba, amma kamar idan wata kasa dake cikin kungiyar kwance ta nato akai kai mata hari to kamar an kai...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan tsaron kasar Pakitsan Khaje Asif ya fada a jiya Juma’a cewa, makaman Nukiliyar da kasarsa take da su, wani sashe ne na yarjejeniyar tsaro da su ka kulla da kasar Saudiyya. Haka nan kuma ya kara da cewa; Yarjejeniyar ta tsaro ce tsagwaronsa, kuma manufarta ita ce aiki tare a tsakanin kasashen biyu a wannan fagen. Asif wanda tashar talabijin din “Geo News” ta yi hira da shi ya kuma ce; Idan daya daga cikin kasashen ta fuskanci hari,to za mu mayar da martani na hadin gwiwa.” Ministan tsaron na kasar Pakistan ya kuma ce; Ba tare da ambaton suna ba,amma duk wanda ya kai harin wuce gona da iri, to zai fuskanci mayar da martani na hadin gwiwa....
    Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar. “Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa. “Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani,...
    Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne,  bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta  su yi aikin koyarwa.” Tsarin na ma’aikatar ilimin ya ƙara jan kunne na da akwai buƙatar tabbatar da cewaana amfani da shi tsarin dokar kamar yadda aka bayyna “a kuma samu dama ta wayar da kan duk masu ruwa da tsaki kan lamarin” a duk illahirin faɗin tarayyar Nijeriya”saboda kar abin ya kawo cikas na jarabawar da ta shafi ƴ aƴ an al’umma.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Shugaban kungiyar goyon bayan Sanata Marafa, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya ce ficewar Sanata Kabir Garba Marafa daga jam’iyyar APC ya kara karfafa masa siyasa tare da jaddada goyon bayansa ga magoya bayansa.   A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa da kan sa, Alhaji Maikatako ya bayyana cewa Sanata Marafa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ba wani yunkuri ne na kashin kai ba, sai dai an dauki matakin ne na gama-gari bayan tattaunawa da magoya bayan sa.   Ya ce tun bayan wannan sanarwar kungiyar ta fara samun sakonni da ziyarce-ziyarcen hadin kai daga fadin jihar Zamfara da Arewa maso Yamma da kuma wajenta, inda da yawa ke bayyana shirin tafiya da sabuwar alkiblar siyasa....
    Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna, da tabarmi, da gidajen sauro, da magungunan zazzabin cizon sauro. A cewar ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai, kimanin mutane 273,000 ne ambaliyar ta shafa a gundumomi 12 na jihohin Jonglei da Unity da Upper Nile da Central Equatoria, inda jihohin Jonglei da Unity suka dauki sama da kaso 91 na jimilar mutanen da ambaliyar ta shafa. Martha Remijo Rial, daraktan kula da...
    1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani da ita, zai iya kamuwa da cutar, ko kuma wani abu maikama da haka. 3- Ɓangaren saduwa a tsakanin ma’aurata- A wajen saduwa tsakanin mata da miji, ta hanyar haɗuwa maniyyi ko maziyyi da sauran makamantansu, wannan cuta za ta samu hanyar shigewa nan take da ɗaya daga cikinsu na ɗauke da ita. Don haka, waɗannan hanyoyi da aka ambata dukkanninsu na iya faruwa a...
    Wata matar aure ta shiga hannu kan zargin ƙone fuskar ’yar mijinta, Fatima Talba mai shekara 17 da tafasasshen man girki, a unguwar Jiddari Polo da ke Jihar Borno. Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, bayan wata taƙaddama da kaure tsakanin Fatima da matar ubanta. Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe “Matar ce ta kwara wa Fatima man girki mai zafi a fuska, wanda ya janyo mata mummunan ƙuna,” in ji majiyar. An bayyana cewa Fatima na tare da mahaifinta a lokacin da suke shirye-shiryen aurenta da ake sa ran yi a nan...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce abin da ya faru shi ne wani jami’in tsaro da ke gadin wajen ne ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu. A cewarsa, raunin ba shi da alaƙa da harbin bindiga, kamar yadda wasu shafukan Internet suka wallafa. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na daren ranar...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari. Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi. Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, inda ya sake yi musu ta’aziyya. Ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari cewa zai ci gaba da kula da ayyukan alheri Buhari ya bari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona farjin ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
    Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda. Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya...
    Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da sanyin safiyar Juma’a. Rahotanni sun ce yayin harin, maharan sun harbi wani jami’in ɗan sanda da ke gadin sakatariyar suka ji masa rauni ƙafa. An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda maharan suka buɗe wuta. Shugaban ƙungiyar NUJ reshen jihar, Rajab Ismail Mohammed, ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali da kuma babbar barazana ga lafiyar ’yan jarida...
    Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce akalla mutane 1,666 mazauna jihar Legas sun rasa ransu ta hanyoyin da ba su dace ba, ciki har da kashe kansu, tsakanin farkon 2020 zuwa karshen 2024. Wannan bayani ya fito ne daga bakin likitan binciken gawarwaki na rundunar, ACP Samuel Keshinro, yayin gabatar da rahoton bincike kan kisan mata a wani taron da aka gudanar a jihar ranar Alhamis. Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza A cewar Keshinro, rahoton ya mayar da hankali ne kan abubuwan da suka shafi kisan kai, kashe kai, hatsarurruka da sauran hanyoyin mutuwa da ba su da alaka da cuta, domin wayar da kan...
    Bayan tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi da babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar tarayyar turai kaja kallas ta maimaita bukatar kungiyar na sa ido kan tashohin nukiliyar iran, kana tayi gargadin cewa kofar diplomasiya tana gab da rufewa, matsayin da iran taki amincewa da shi kuma ta bayyana shi a matsayin mara inganci, Iran a matsayinta na member a NPT ta yi aiki da nauyin da ya rataya akanta, karkashin yarjejeniyar JCPOA yayin da Iran ke jiran kungiyar tarayyar turai ta yi aiki da abin da ya hau kanta kuma ta cire takunkumi, amma hakan bai samu ba, kasashen turai da hadin bakin Amurka suna barazanar sake dawo da takunkumai don matsin lamba ga...
    Rahotanni sun bayyana cewa tankunan yakin HKI na ci gaba da kutsa kai a tsakiyar gaza a yau juma’a, lamarin da ya jawo tsananta kai hare-hare ta kasa da tilastawa dubban mutane barin muhallinsu sakamakon yankewar hanyoyin sadarwa, A gefe daya kuma Amurka a karo na 6 ta hau kujerar naki kan kudurin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na bukatar dakatar da bude wuta da kuma sakin fursunoni da aka kama. Yankin gaza yana dauke da mutane miliyan daya kafin yaki, sai dai rahutanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu sama da 350,000 ne suka bace. Hare hare Isra’ila tun daga 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 ta kashe falasdinawa 65141 kuma ta jikkkata 165925 kamar yadda majiyar...
    Najeriya ta tabbatar da shirinta na karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila na 2030, inda za ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta kafa wannan tarihi tun 1930. Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Shugaban Ma’aikatansa Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnati ta ba da cikakken goyon baya, ta kuma shirya samar da dukkan abubuwan more rayuwa, tsaro da masauki kafin lokaci. A jawabansu daban daban, Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa Shehu Dikko da Shugaban Kungiyar Wasannin Renon Ingila Habu Gumel, sun bayyana cewa Najeriya ce damar Afirka mafi cancanta, yayin da kwamitin neman karɓar gasar ya gabatar da shirin gudanar da wasanni 15, ciki har da kwallon ƙafa. Najeriya da Indiya ne ke neman karɓar gasar, inda za a...
    Benfica ta sanar da naɗa José Mourinho a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Bruno Lage, wanda ƙungiyar ta karo bayan da Qarabag ta doke ta a gasar Zakarun Turai ranar Talata. Benfica ta kori Lage duk da cewa wasa ɗaya kawai ya yi rashin nasara a dukkanin gasa a bana. Wata sanarwa da Benfica ta fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa, Mourinho mai shekaru 62 zai jagoranci ƙungiyar har zuwa kakar wasanni ta 2026/2027, tare da zaɓin raba gari a ƙarshen kakar nan. An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar Tsohon kociyan Chelsea, Real Madrid da Manchester United, ya dawo Benfica ne bayan ya rasa aiki a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya. An yanke wa Musa hukuncin kisa ne a ranar Alhamis bayan da aka same shi da laifuka biyu kan kisan gilla da aka yi wa wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare na Jihar Bauchi. Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu Daily Trust ta ruwaito cewa, an fara shari’ar Musa ne a farkon watan Agustan 2025 bayan kama shi biyo bayan binciken haɗin gwiwa da...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci jihar Kaduna  ranar Juma’a 19 ga watan Satumban 2025. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa shugaba Tinubu zai halarci daurin auren  Nasirudeen Yari, ɗa ga Sanata Abdul’aziz Yari, da ke wakiltar Zamfara ta Yamma,  da Amaryarsa Shehu Idris. A yayin wannan ziyara, shugaba Tinubu zai kuma ziyarci Hajia Aisha, matar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidansu da ke Kaduna. Ana sa ran shugaban zai koma Abuja a ranar, nan take bayan kammala ziyarar.   Daga Bello Wakili
    A yau Alhamis ne ne aka kai wasu hare-hare biyu na suka da wuka akan mashigar ‘al-karamah’ dake kan iyakar Falasdinu da Jordan. Majiyar ‘yan sahayoniya wacce ta ambaci labarin ta kuma ce; A matakin farko an kai hari ne ta hanyar bude wuta da bindiga akan sojoji, sannan aka kai wani harin ta hanyar sara da wuka. Harin ya yi sanadiyyar kashe sojoji biyu da kuma jikkata wasu da dama. Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai,sojojin HKI su ka killace yankin baki daya domin yin bincike. A cikin watan Satumba an kai wani harin irin wannan wanda ya yi sanadiyyar halakar ‘yan sahayoniya 3 da kuma jikkata wasu da dama. Wannan harin na ‘yan gwagwarmaya ya zo...
      Zhakom ya ƙara da cewa, wanda aka cafken da kuma kayayyakin da aka ƙwato suna hannun rundunar domin ci gaba da bincike, kuma rundunar za ta ci gaba da farmakar wadanda suka tsere daga haramtacciyar masana’antar kera makaman. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da Cin Zarafin Mata a Jihar Neja”. Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara Taron dai wata kungiya mai zaman kanta mai suna Tunani Initiative ce ta shira shi, tare da hadin gwiwar gidauniyar Dorothy Njemanze Foundation da kuma gidauniyar Foundation, domin ƙarfafa gwiwar mata wajen magance cin zarafin jinsi...
    Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa, SEMA, tare da hadin gwiwar Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, sun shirya gwajin yadda za a gidanar ayyukan ceton ambaliyar ruwa a karamar hukumar Auyo.   Gwajin wanda ya tattaro masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban, an yi shi ne da nufin baiwa mahalarta taron kwarewa da ilimin da suka dace don ceto da kuma mayar da martani ga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa.   Aikin ya ƙunshi mahimman wurare kamar dabarun bincike da ceto, taimakon farko, da hanyoyin ƙaura.   Wannan yunƙurin ya nuna himmar SEMA, NEMA, da UNICEF don haɓaka ƙarfin masu ruwa da tsaki na...
    Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis. Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar. Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m Sai dai a ranar Laraba, Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci tare da umartar gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar da su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba. A halin yanzu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya miƙa mulki...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido Wada ya jagoranta a Dutse babban birnin jihar.   Ya bayyana cewa, Rundunar za ta hada gwiwa da wadanda abin ya shafa domin fuskanatar kalubalen zirga-zirga don daukar matakin da ya dace.   A cewarsa, rundunar ta ci gaba da  shirye-shiryen ‘yan sanda da al’umma ke tafiyar da su ta hanyar samar da hadin gwiwa mai karfi da masu ruwa da tsaki da suka himmatu...
    Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na  jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...
    A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...