2025-06-19@02:49:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 138

«da iyayensu»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa. Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa. A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yanki na kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik, da girmama bukatunsu da al’adun kabilunsu da kuma hadin gwiwarsu wajen samun ci gaba da kansu. A kwanakin baya, yayin da firaministan kasar tsibiran Cook Mark Brown yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye girmama kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik a fannoni 4. Firaminista Brown ya yi nuni da cewa, kasarsa ta tsibiran Cook ta dora muhimmanci ga girmamawar da Sin ta nuna mata, kasar Sin ta kiyaye yin hakan tun da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu....
    Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 22 a hannun ’yan bindiga. An sace shi ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke garin Tsiga a Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari. Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250 Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta Maharan sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 250 kafin su sako shi. Sai dai bayan tattaunawa, an biya kuɗin fansa, wanda ya kai ga sakinsa. A halin yanzu, likitoci na kula da shi a wani asibiti da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau ranar 27 ga wannan wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da maida batun samun bunkasuwa a matsayin batu mafi muhimmanci a cikin ajendar kasa da kasa, da bin tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, da zama babbar kasa mai ba da muhimmiyar gudummawa a duniya, don tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin ta kiyaye sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya. A matsayin kasa ta biyu mafi ci gaban tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 cikin dari ga bunkasuwar duniya, kana ita ce muhimmiyar abokiya ta...
    Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Wata majiya ta ce uwar jaririn mai shekaru 18 ta jefo shi ne ta tagar ɗakin wani otel daga hawa na biyu a Kudancin Faransa. An bai wa jaririn kulawar gaggawa amma a ƙarshe ya ce ga garinku nan kamar yadda majiyar ta tabbatar. ’Yan sanda sun ce jaririn ya mutu da misalin ƙarfe 7:45 na safiya...
    A yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi a birnin Johannesburg, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afirka ta Kudu Ronald Lamola sun yi wata ganawa ta musamman, inda suka tattauna dangantakar kasashensu da manufofinsu. Sun amince da manufa guda don habaka tasirin Duniya, da nufin tabbatar da ingantacciyar murya guda ta kasashe masu tasowa. Wang ya bayyana a yayin taronsu cewa, kasar Sin a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwar cin moriyar juna tsakaninta da kasar Afirka ta kudu, da kara gaggauta bunkasuwar kasashen biyu, da kuma kara yin hadin gwiwa don kara daukaka murya da wakilci na kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka a cikin ajandar kasa da kasa. Wannan...
    Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram. Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno  Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram. Sanarwar ta bayyana cewa...
    A jiya Juma’a ce aka fitar da jadawalin zagayen ’yan 16 na Gasar Zakarun Turai ta bana a birnin Nyon. Hukumar Ƙwallon Ƙafar Turai, UEFA, ta tsara yadda zagayen na ‘yan 16 da zagayen dab da na kusa da na ƙarshe da zagayen dab da ƙarshe da kuma zagayen ƙarshe za su kasance. Haɗarin mota ya laƙume rayuka 12 a Neja Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi Za a kece raini ne a karawar farko ta zagayen ’yan 16 a ranakun 4 da 5 na watan Maris, inda za a yi karon-batta a karawa ta biyu bayan mako guda. Mai riƙe da kambun gasar Real Madrid za ta kara da abokiyar hamayyarta na birni Atletico Madrid a maimaicin...
      Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari.   Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
    Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu. An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a Gombe Gini ya faɗa kansu ne ba zato ba tsammani, lamarin ya haddasa mummunan tashin hankali tare da jefa ɗalibai da dama cikin baraguzan gini. Bayan aukuwar lamarin, an yi gaggawar ceto ɗaliban, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Ƙwararru na Potiskum domin ba su kulawa. Duk da an samu nasarar ceto da dama daga cikinsu, wata ɗaliba ta rasa ranta...
    Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya. Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
    Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare. Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa Balewa House da ke Abuja. Ya bayyana cewa waɗanda ke tsare a gidan yari a Amurka ne za su kasance cikin rukuni na farko na waɗanda za a dawo da su. Ya Kamata Amurka Ta San Ana Barin Halal Don Kunya Amurka Da Isra’ila Sun Sake Barazanar ‘Lugudan Wuta’ A Gaza A nata ɓangaren, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da...
    Ƙungiyar Boko Haram ta kashe kwamandoji da mayaƙan takwararta na ISWAP da dama yayin wani ƙazamin rikici da suka tafka ranar Juma’a a Ƙaramar Hukumar Kukawa da ke Jihar Borno. Bayanai sun ce an kashe kwamandoji da mayaƙan ISWAP 31 yayin harin da mayaƙan Boko Haram suka kai ƙarƙashin jagorancin wani ta’adda mai suna Bakoura. Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal Ɗan Nijeriya ya lashe kyautar Kundin Bajinta na Duniya a fagen ɗaukar hoto Wata majiya ta shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya, Zagazola Makama, cewa yaƙin da aka fara tun da sanyin safiyar ranar 14 ga watan Fabrairu ya haɗa da sansanonin ISWAP da ke Toumbun Gini...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta mutu, saboda barazanar da yayi na karawa dukkan mambobin kungiyar kudin fito ko haraji na 100% na kayakin kasashensu dake shiga kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, maganar shugaban zai kara sabani a cikin kasashen kungiyar, ta BRICS wanda suke ganin Amurka ta mamaye al-amuran tattalin arziki a duniya. An kafa kungiyar BRICS ne a shekara 2009 kuma kasashen da suka fara kafata sune, Brazil, Russia, India, da kuma China, amma daga baya kungiyar ta kara fadada, inda kasashen Afirka ta kudu, Iran, Habasha, da kuma Hadaddiyar daular Larabawa. Bayan da kasar Rasha ta karbi shugabancin kungiyar na...
    Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine. Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana a wannan Talata a yayin wani taron manema labarai cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan ma’abuta girman kai, da kuma shahidan bil’adama a kan mulkin mallaka”. Ya kara da cewa jana’izar za ta ci gaba da zaburar da mutane masu ‘yanci a duniya shekaru da dama masu zuwa.” Daher ya yi nuni da cewa bikin zai dauki...
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
    Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu. A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya  ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan. Tunda farko...
    LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu.   Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen.   Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.   A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
    A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa.   Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun maslaha.
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa da ta wakilai. A cikin wasikar da aka karanta yayin zaman majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce an sami  karin kudin ne sakamakon karin kudaden shigar da hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta samu na Naira tiriliyan 1.4, yayin da hukumar hana fasakwabri  ta kasa ta tara Naira tiriliyan 1.2, da kuma Naira tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka tara. A don...
    Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) a Jihar Kano ta gargaɗi al’umma kan wata alawar yara mai da sanya maye, da ke yawo a gari. Hukumar ta gargaɗi, musamman iyaye da su yi hattara da alawar da sauran kayan tanɗe-tanɗe da ke ɗauke da sinadarai masu sanya maye. Kakakin Hukumar a jihar, ASN Sadiq Muhammad Maigatari, ya kuma yi kira ga iyaye da suka riƙa lura da irin kayan tanɗe-tanɗe da ’ya’yansu ke saya. Ya bayyana cewa alawar tana kama da cakulet, amma a cikinta an sanya abin da ke bugarwa, kuma yawanci an fi sayarwa a makarantu. NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, tare da Sojoji sun samu nasarar ceto mutum 23 da ’yan bindiga suka sace a wani artabu da aka yi a ƙauyen Doka, da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru. A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Mansur Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa babban jami’in ’Yan Sandan yankin Kajuru ne ya jagoranci samamen. Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5 Osimhen ya maka ɗan jarida a kotu Ya ce bayan samun bayanan sirri game da maharan, jami’an tsaro sun kai farmaki inda suka ceto dukkanin mutanen 23, waɗanda mazauna Kauru ne. A yayin artabun, wasu daga cikin maharan sun mutu, yayin da wasu suka tsere cikin daji da raunukan harbin...
    Kasar Sin Na Ci Gaba Da Inganta Kiyaye Dausayi
    Wakilin CMG ya yi hira da tsohon shugaban majalisar nahiyar Turai, kuma tsohon firaministan kasar Belgium, Herman Van Rompuy, a kwanan baya, inda tsohon shugaban ya nanata bukatar karfafa cudanya tsakanin al’adun bangarorin yammaci da gabashin duniya. Herman Rompuy ya ce, ta hanyar cudanya, kowa zai iya koyon sabbin dabarun da yake bukata, kana za a iya tabbatar da fahimtar juna. A daura da haka, idan an yi watsi da damar cudanya da tattaunawa, to, tabbas za a samu abkuwar rikici da arangama, har ma zai kai ga barkewar yake-yake. Aston Villa Na Neman Ɗaukar Marcus Rashford A Matsayin Aro  AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Fafata Da Tunisiya A Wasannin Rukuni Dangane da shawarar raya “Ziri Daya da Hanya Daya”...
    Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan hanyarsu daga Barikin Myoung da ke yankin Marocco a Shomolu. Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa a Adamawa Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Waɗanda suka samu raunuka suna jinya a asibitin sojojin Nijeriya da ke Yaba, yayin da aka ajiye gawarwakin sojojin da suka rasu a ɗakin ajiye gawa a asibitin. Hedikwatar Runduna ta 81 ta Sojojin Nijeriya,...
    Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a cikin sansanin Sojojin. Wani Soja da ya tsira daga harin ya bayyana cewa, “Jini ne ko’ina. Na tsira ne kawai saboda ina baya.” Mun Kashe Ƴan Ta’adda Sama Da 70, Kafin Mu Yi Rashin 22 – Sojoji Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara Sojan (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya ce a...
    Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta kama wani saurayi da budurwarsa bisa zargin yin aure a wajen wani taro ba tare da amincewar iyayensu ba. A cewar Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, matasan sun yi auren ne a wajen shaƙatawa bayan wani da ba su da alaƙa da shi ya biya sadakin amaryar. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin waya Ya bayyana cewa yin hakan ya saɓa wa ƙa’idar Musulunci kuma ba za a yarda da irin wannan lamarin ya ci gaba da faruwa a Kano ba. “Muna sanar da cewa mun kama ma’auratan, kuma za mu ci gaba da bincike don kama abokansu da duk wanda...
    Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024. Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan a Damaturu yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekara guda da ta gabata. Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Ya ce magungunan da aka kama sun haɗa da kilo 396.526 na tabar wiwi da kilo 141.2 na sauran kayayyakin maye. Ogunboye ya ce hukumar ta miƙa mutane 21...
    “Ƙungiyar Al-Hilal ta gode wa Neymar bisa gudunmuwar da ya bayar, kuma tana masa fatan alheri a nan gaba,” in ji ƙungiyar. Wannan matakin ya zo ne yayin da ya rage wata bakwai kafin ƙarshen kwantaragin Neymar, wanda ya kai shekara biyu da ƙungiyar. A Al-Hilal, ana biyan Neymar Yuro miliyan 150 a shekara. Lokacin da ya koma ƙungiyar, Neymar ya bayyana burinsa na kafa tarihi, amma raunin da ya samu yayin wasan Brazil da Uruguay a shekarar 2023 ya hana shi buga wasanni da dama.
    Wata nakiya ta fashe a Sabon-Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata da kuma jikkata wasu mutum shida. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe. An gurfanar da masoyan da suka kai wa malami hari a Kano Kotu ta ɗaure matashi shekara 2 kan satar wayoyi a Kano Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wasu nakiyoyi da wani mutum ya ɓoye a wajen domin aikin haƙar ma’adinai. Lamarin ya yi sanadin lalacewar gidaje kusan 12 a yankin, inda ya jefa al’umma cikin tashin hankali. Fatima Sadauki ta rasa ranta...
    An tabbatar da mutuwar aƙalla mutum 18 sakamakon hatsarin wata tankar mai da ta yi bindiga a Jihar Enugu. Alƙaluman da mahukunta suka fitar ya nuna cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31 ciki har da mutum 10 da suka samu raunuka daban-daban yayin da aka ceto wasu uku da suka tsallake rijiya da baya sai kuma mutum 18 ɗin da suka ƙone ƙurmus. An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila Hakan na ƙunshe cikin sanarwa da mai magana da yawun rundunar hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa reshen Jihar Enugu, Olusegun Ogungbemide ya fitar da yammacin ranar Asabar. Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin wanda ya...