An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato
Published: 11th, April 2025 GMT
Dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Filato, sun nemo gawar wani makiyayi mai shekaru 16 da ya ɓace tare da ƙwato shanu sama da 50 da aka sace.
Daily Trust ta rawaito cewa, sojojin sun gano gawar makiyayin da ya ɓace tare da wasu Fulani makiyaya a ranar Juma’ar nan.
Makiyayin Abdullahi Muhammad mai shekara 16 da ya ɓace, kuma an samu rahoton an yi awon gaba da shanu sama da 70 a yankin Ariri, ƙaramar hukumar Bassa, a lokacin da suke kiwo a yankin.
Sai dai a baya, Danjuma Auta, babban sakataren ƙungiyar raya Irigwe (IDA), ya musanta batun satar shanu a yankin, yana mai zargin cewa an kashe mambobinsu da dama a cikin makonni uku da suka gabata, kuma suna fuskantar ƙalubale na hare-hare.
A cewar Ya’u Idris, shugaban Ƙungiyar MACBAN a garin Bassa, wanda ya tabbatar da samun nasarar gano gawar makiyayin da ya ɓace, sojojin OPSH tare da wasu makiyaya ne suka tsinto gawar a wani kabari mara zurfi, tare da wasu makiyaya a gaɓar kogi da ke kusa da babban yankin Ariri.
Ya ce, an fille kan makiyayin, aka datse hannunsa na hagu.
Da yake ƙarin bayani, shugaban ya ce, “Mun tono gawar kuma muka mayar da shi gida don yin sallar jana’iza, an ceto sama da kashi 80% na shanun, muna godiya ga jami’an tsaro musamman jami’an tsaron OPSH bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ƙwato gawar da shanu.”
Mai magana da yawun rundunar ‘Operation Safe Haven’ Manjo Samson Zhakom da DSP Alabo Alfred na rundunar ’yan sandan jihar, har yanzu ba su mayar da martani ga saƙon da wakilinmu ya aika masu kan wannan lamari ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Operation Safe Haven da ya ɓace
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’an tsaro sun harbi matar aure sun lakaɗa wa jama’a duka a Katsina
Al’ummar Unguwar Filin Samji da ke garin Katsina sun buƙaci hukumomi su tabbatar da adalci, bisan zargin da ake wa jami’an Hisbah da na Rundunar Tsaron Al’umma na gwamnatin jihar (C-Watch) da harbin mutane da kuma lakaɗa musu duka ba tare da dalili ba.
Wata matar aure mai suna Khadija Hamisu Wada ta samu raunuka sakamakon harbin bindiga, yayin da wasu mutane da dama suka ji raunuka bayan an kai musu hari da adduna, wuƙaƙe da sanduna.
A cewar mazauna yankin, aƙalla mutane bakwai ne suka ji munanan raunuka a lokacin da abin ya faru.
An ruwaito cewa Khadija na dauke da harsasai biyu a ƙugu, kuma likitoci sun gargadi cewa cire su da gaggawa na iya jawo mata matsalar laka.
Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 80 a Kebbi Rikicin ADC: Sanata Nenadi ta zama shugaba a KadunaHarsashi guda da ya shiga ƙafarta an cire shi, sai dai tana roƙon hukumomi su taimaka mata da magani da shari’a domin ceto rayuwarta.
Khadija ta shaida wa manema labarai cewa, “Na fita neman ɗana ƙarami Baba Aliyu ne, sai jami’an C-Watch suka harbe ni sau uku — sau biyu a ƙugu, da sau ɗaya a ƙafa. Har yanzu ina ɗauke da harsasai biyu a jikina.
“Likitoci sun ce sai sun matsa kafin a cire su, don kada a lalata ƙashin baya. Allah ne Kaɗai Ya san azabar da nake ciki.”
Khadija, uwa mai yara bakwai, ta fito ne daga gida mai ƙaramin karfi, kuma mijinta tsohon ma’aikaci ne da ke karɓar fansho.
Ta ce ba su da halin biyan kudin aikin tiyata da magunguna, don haka ta roƙi Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa da ya shiga lamarin don ceton rayuwarta.
Ta ce, “Tun bayan harin nake zuwa asibiti kullum amma babu mafita. Likitoci suna ce min in koma gida kawai. Ka yi tunanin rayuwa da harsasai a jikinka tsawon kwanaki tara zuwa goma, jikina yana ƙara lalacewa, ba na iya bacci ko kwanciyar hankali ba.”
’Yarta kaɗai da ke da aure, Maryam Hamisu Wada, ta dawo daga gidan mijinta don kula da ita da sauran ’yan gida. Ta bayyana cewa tun bayan harin ba ta samun nutsuwa ko barci, tana roƙon hukumomi su taimaka wajen ceton mahaifiyarta.
Maryam ta roƙi Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Katsina da gwamnatin jihar su ba da umarnin a karɓi mahaifiyarta a Asibitin Janar Amadi Rimi, don fara aikin tiyata na cire sauran harsasai biyu da ke jikinta.
‘’Yan Hisbah da C-Watch sun kawo mana hari’Wani mazaunin yankin, Muhammad Shafiu, ya ce: “Ina zaune gaban gidan su budurwata muna hira sai jami’an Hisba da C-Watch suka zo da bindigogi da sanduna suka fara duka ba tare da wani bayani ba. Sun yi min rauni sosai har na suma. Ina rokon gwamnati ta tabbatar da adalci.”
Wani mutum mai suna Tijjani Abubakar shi ma ya shaida cewa, “Ina zaune bakin ƙofa sai jami’an Hisba da C-Watch suka iso. Ba tare da wani dalili ba suka fara dukan mu da sanduna har na ji raunuka da dama a jiki.
“Ina kira ga Gwamna Raɗɗa da ya ba da umarnin bincike don kauce wa maimaituwar wannan mummunan lamari.”
A nasa bangaren, Rabi’u Idris, ya ce shi baƙo ne da ya je yankin don sayen rago, amma aka doke shi har ya suma.
“Na yi ƙoƙarin bayyana musu cewa ba mazaunin yankin ba ne, amma suka ƙi sauraro. Sun doke ni har na fita daga hayyacina. Yanzu ina neman haƙƙina ta kotu har sai an tabbatar da adalci.”
Wani shaida da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, jami’an C-Watch sun kutsa gidan iyayensa suna zargin kanensa da rashin tarbiya.
“Sun razana iyayena, suka bugi iyayenmu, suka wulaƙanta mu ba tare da wani hujja ba. Muna neman adalci.”
Yanzu haka akwai fargaba a yankin, inda wasu mazauna ke barazanar ɗaukar doka a hannunsu, yayin da wasu ke roƙon gwamnati ta shiga tsakani.
Sun bayyana lamarin a matsayin cin zarafi da amfani da ƙarfi fiye da ƙima kan fararen hula.
Shaidu sun bayyana cewa jami’an Hisba aka fara kiran don sulhunta faɗa tsakanin wasu samari a yankin, amma lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali bayan jami’an Hisba suka nemi taimakon jami’an C-Watch, wanda hakan ya janyo harbe-harben da dukan mutane.
Da yake mayar da martani, Kwamandan Ayyuka na Hukumar Hisba ta Jihar Katsina, Muhammad Musa, ya musanta zargin cewa jami’ansa ne suka harbi mutane, yana mai cewa jami’an Hisba ba su riƙe bindigogi.
Ya ce maimakon haka, ’yan daba na Filin Samji ne suka kai hari suka lalata ofishin Hisba da ke yankin.
Duk da irin kalubalen tsaro da ke addabar al’ummomin Katsina, mazauna jihar suna kira ga gwamnatin jihar da ta gudanar da cikakken bincike, ta ɗauki matakin gaggawa don dawo da aminci da amincewar jama’a a cikin birnin Katsina.