Sojoji Sun Daƙile Harin Boko Haram A Yobe
Published: 22nd, April 2025 GMT
A yayin harin, mutane da dama sun gudu zuwa dazuka, amma sun fara dawowa yayin da zaman lafiya ya fara samuwa.
“Yanzu mutane sun fara dawowa garin kuma abubuwa sun fara dawowa dai-dai,” inji wani mazaunin yankin.
Wani dagacin ƙauyen, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce an samu zaman lafiya kuma al’umma sun fara komawa harkokinsu na yau da kullum.
“Muna gode wa sojojin bisa yadda suka daƙile harin cikin gaggawa,” inji shi.
Wannan ba shi ne karo na farko da aka kai hari a Buni Yadi ba, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a game da buƙatar ƙarin tsaro a yankin.
Mazauna yankin na kira ga gwamnati da ta tura ƙarin sojoji don hana faruwar irin wannan hari a gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Boko Haram Daƙilewa Hari
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
Dakarun Sojin Najeriya, sun ceto wasu mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace a Ƙaramar Hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano.
Wannan zuwa ne bayan mazauna Yankamaye Cikin Gari suka sanar da jami’an tsaro cewa ’yan bindiga sun shiga ƙauyensu a daren ranar Juma’a.
’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar AfrikaWannan na cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce sojin ƙasa tare da haɗin guiwar sojin sama da ’yan sanda sun garzaya wajen, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, sannan suka ceto mutanen da abin ya shafa.
Sai dai Zubairu, ya ce ’yan bindigar sun riga sun kashe wata mata mai shekaru 60 kafin sojoji su isa yankin.
Ya ƙara da cewa bayan harin farko da suka kai, sojojin sun bi sahun ’yan bindigar zuwa yankin Rimaye, inda suka yi musu luguden wuta, wanda hakan ya tilasta musu barin mutanen da suka sace.
Sai dai har yanzu ba a gano inda mutane huɗu da suka sace suke ba.
Bayanai sun nuna cewar bayan ’yan bindigar sun tsere, sun nufi Ƙaramar Hukumar Kankia da ke Jihar Katsina, kuma jami’an tsaro na ci gaba da bibiyarsu.
Kwamandan rundunar, ya yaba da jarumtar sojojin, ya roƙi jama’a da su riƙa bai wa hukumomin tsaro sahihin bayanai a kan lokaci domin kawar da ’yan bindiga a jihar.