Aminiya:
2025-07-12@04:20:52 GMT

Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya

Published: 2nd, May 2025 GMT

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta yaye sabbin matuƙa jiragen sama 35 bayan sun kammala samun horo.

Babban Hafsan Rundunar, Iya Mashal Hassan Abubakar, ne ya sanya sabbin matuƙa jiragen anini a yayin bikin da aka gudanar a Makarantar Tukin Jirgi na rundunar (401 FTS) da ke Kaduna.

Yayen nasu ya zo ne watanni kaɗan bayan rundunar ta mallaki sabbin jiragen yaki guda 12, waɗanda suka ƙara mata ƙaimi wajen ayyukan samar da tsaro da kuma ta’addanci.

A wani taro da ya gudanar da tsofaffin sojojin rundunar a Kaduna, Iya Marshal Hassan Abubakar ya shaida musu cewa rundunar tana jiran karin jiragen yaƙi guda 34.

Ya buƙaci waɗanda aka yayen nasu da su yi amfani da wannan dama wajen cika burin ’yan Najeriya da ke da kyakkyawan fata a kansu.

Rundunar na da nufin amfani da sabbin matuƙan jiragen nata a ayyukanta na tabbatar da tsaro a sassan kasar nan.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: jirage Rundunar

এছাড়াও পড়ুন:

An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN

An gabatar da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin Shugaban Kwamitin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN).

Wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da Ganduje ya yi daga shugabancin APC kwanan nan, inda ya bayyana cewa ya yi hakan saboda wasu muhimman dalilai na ƙashin kansa.

2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai

Jam’iyyar ta maye gurbinsa da Ali Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya.

Gbenga Saka, mai bai wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shawara kan harkokin dijital, ya wallafa bidiyon bikin rantsar da Ganduje a shafin X.

Ganduje, wanda tsohon Gwamnan Jihar Kano ne, ya kasance cikin kwamitin hukumar tare da wasu kamar su: Ms Olubunmi Kuku, Babbar Daraktar FAAN, Ms Dorothy Duruaka, Ahmed Ibrahim Suleiman.

Sauran sun haɗa da Nasiru Muazu, Omozojie Okoboh, TP Vembe da kuma Bridget Gold a matsayin sakatariyar kwamitin.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne, ya naɗa Ganduje shugaban wannan kwamitin tun a watan Janairun 2025.

A wajen bikin, Minista Festus Keyamo ya ce: “Muna sa ran wannan kwamitin zai taimaka wajen bunƙasa harkokin sufurin jiragen sama a ƙasar nan, haɗa yankuna daban-daban, da kuma kawo ci gaban tattalin arziƙi.

“Duk da ƙalubale kamar matsalar gine-gine da sauye-sauyen da ke faruwa a harkar jiragen sama a duniya.

“Ina da tabbacin ƙwarewarku za ta taimaka wajen cimma burin FAAN.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dalilin da ya sa muka gayyaci Sheikh Lawal Triumph – ’Yan sanda
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 24 a Arewa maso Gabashin Nijeriya
  • Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno
  • An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos
  • ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano
  • ’Yan sanda sun ƙaddamar da samamen “Operation Kukan Kura”, sun kama mutum 98 a Kano
  • NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
  • An gabatar da Ganduje a matsayin shugaban kwamitin hukumar FAAN
  • Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai
  • Za A Horas Da Jami’an Tsaron Sakkwato, Kaduna Da Benue Sabbin Dabarun Aiki