Gazawar Gwamnati Kan Kiyaye Rayuka Da Dukiyoyi: Gwamnan Filato Ya Nemi Yafiyar Al’ummar Jihar
Published: 16th, April 2025 GMT
Ya kuma jaddada cewa, “An yi duk wani shiri don kauce wa hakan, amma duk da haka mun gaza, a madadin gwamnati da hukumomin tsaro ku yafe mana”.
Gwamnan ya yi Allah-wadai da ci gaba da hare-haren da suka addabi yankin Irigwe, ya kuma yi alkawarin sabunta alkawarin kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar.
Mutfwang ya bukaci al’umma da su dawo da tsare-tsaren tsaro na iyaye da kakanni, ya kuma yi kira ga matasa da su sa ido sosai, musamman a lokacin damuna mai zuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin ministan — Badaru
Tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya san dalilin da ya sa ya yi murabus.
Badaru, ya ajiye aiki ne a ranar Litinin, inda ya ce matsar rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus.
Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokintaShugaban ƙasa ya amince da murabus ɗinsa kuma ya naɗa Janar Chris Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.
Badaru, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi murabus ne saboda barazanar da Amurka ta yi na ɗaukar matakin soji kan Najeriya game da zargin kisan Kiristoci.
“Ina so na bayyana a fili cewa wannan labari ƙarya ne, an ƙirƙire shi don ɓata min suna, kuma ba shi da alaƙa da ni ko wani da ke magana a madadina,” in ji shi.
Ya ce an ƙirƙiro wannan ƙarya ne don a ɓata masa suna da kuma haddasa rikici tsakaninsa da shugaban ƙasa.
“Gaskiyar dalilin murabus ɗina na bayyana ta shugaban ƙasa. Duk wani ƙarin bayani na daban ƙarya ne da aka ƙirƙira,” in ji Badaru.
Ya tabbatar wa Tinubu da ’yan Najeriya cewa har yanzu yana biyayya, tare da jajircewa wajen ganin an samu zaman lafiya, tsaro da nasarar jam’iyyar APC kafin zaɓen 2027.