DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
Published: 16th, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo.
A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi riƙon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu.
Wannan al’ada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya da iyayen riƙo.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ya ya Hausawa iyaye
এছাড়াও পড়ুন:
Tsoffin ma’aikatan NECO na neman a biya su bashin haƙƙoƙinsu
Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da suka yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi.
Shugaban ƙungiyar tsofffin ma’aikatan, Dokta Abdullahi Rotimi Williams ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da hedikwatar kungiyar a Minna, babban birnin Neja.
Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta NijeriyaShugaban ya kuma koka kan yadda gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma’aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo bayan hakan, musamman maƙalewar haƙƙoƙinsu.
“Da yawa tsoron ritaya ake yi yanzu. Don haka wannan ƙungiyar za ta taimaka wajen rage waɗannan matsalolin.
“Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne na lafiya. Don haka ina roƙon shugaban hukumar da ya tabbatar cewa daga yanzu an kammala shirye-shiryen da suka kamata kafin ma’aikacin NECO ya yi ritaya.”
Ya kuma ce duk da jagororin hukumar na yanzu sun biya wasu daga cikin haƙƙoƙin nasu, ba a kai ga biyan alawus ɗin ƙarin girma ba, da na tafiye-tafiye ba.