Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwana 10
Published: 2nd, June 2025 GMT
Gwamnatin Kano ta ba makarantu hutun kwanaki goma domin bikin Babbar Sallah da za a yi ranar Juma’ar wannan makon.
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa makarantun za su fara hutun ne daga ranar Laraba, 4 ga watan nan na Yuni da muke ciki, zuwa ranar Lahadi, 15 ga wata.
Sanarwar ta kuma bukaci iyaye da ’ya’yansu suke makarantun kwana da su je da wuri domin daukar yaran a ranar Laraba.
Kwamishinan mai kula da ma’aikatar, Ali Makoda, ya kuma bukaci iyaye da su tabbata daliban sun dawo makaranta a kan kari bayan kare hutun Babbar Sallar.
An lakaɗa wa Mataimakin Firinsifal duka saboda hana satar a jarabawa Uba ya harbe ɗansa har lahira saboda zaton biri ne Jirgin soji ya kashe ’yan sa-kai 20 da ke fatattakar ’yan bindiga a ZamfaraA sakonta na taya daliban murna da fatan za a yi Babbar Sallah lafiya, ma’aikatar ilimin ta bayyana cewa hutun ya yi daidai da jadawalin zangon karatu da ake ciki, kuma ba a canza shi ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babbar Sallah gwamnatin Kano makarantu
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta Gargaɗi Isra’ila Kan Tilasta Wa Al’ummar Deir al-Balah Na Gaza Tashi
Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce umurnin da sojojin Isra’ila suka bai wa Falasɗinawa na ficewa tsakiyar Gaza, babban koma baya ne ga ƙoƙarin ceton rayukan al’ummar yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.
A ranar Lahadi ne Isra’ila ta umarci Falasɗinawa a Deir el-Balah, da su koma kudancin Gaza saboda ayyukan soji.
MDD ta sake nanata gargaɗin da ta yi cewa al’ummar Gaza da dama na mutuwa saboda yunwa kuma suna buƙatar agajin abinci cikin gaggawa yayin da Isra’ila ke ci gaba da taƙaita shigar da kayan agaji.